NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi yakumayi saidai a wannan karon ya ɗago idanunsa ya kalleta.

“Eh dukansu abokaina ne, meya faru?” yatambayeta yana me tsareta da idanunsa..

Murmushi ta ƙaƙalo haɗe da cewa
“Babu ko mai kawai dai naga sunyi yawa ne, kuma naga wasu daga cikinsu banga fuskokinsu a wajen bikinmu ba shiyasa”

“Ae mu maza ba irinku bane munfiku yawan jama’a, wasu daga cikinsu basu samu daman zuwa bikinmu ba shiyasa bakisansu ba, kamar Jabeer baisamu halattaba saboda baya Nigeria yana Polland yana karatu, kuma baijima da dawowa ba,  sauran kuma wani uzururruka ne suka hanasu zuwa, kinsan maza da sabgogi”  yafaɗi haka yana me sake kwanciya acikin jikinta.

Yanzu tasamu amsar da takesonji cikin sauƙi, kenan dama Jabeer baya Nigeria ne shiyasa bainemeta ba, da sauri ta yi watsi da tunaninsa haɗe da ƙoƙarin zame Jikinta daga cikin nasa jikin.

Ƙara rungumeta yayi batare daya bata daman tashi ba,  kallon cikin ƙwayar idanun juna suka shigayi, kallon tsananin SO Dr.Sadeeq keyi mata, yayinda ita kuma nakasa fassara wani irin kallo takeyi masa, na ƙauna nane ko na SO oho,      Lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu alokaci guda, yanayin yanda taga idanun nasa sun mareraice shiyasanya taji tsikar jikinta ya tashi,   aduk sanda ta kalli cikin idanunsa takanji wani abu na ratsa har cikin ɓargonta, hakanne ma yasa bata ɗaukan lokaci me tsawo tana iya kallon cikin idanunsa,    sosai idanunsa keyi mata kyau.

“Baby bacci nakeji!”
yafaɗi haka cikin murya me sanyi, yana  me sake lumshe idanunsa.

“Ɓacci a wannan lokacin? Yanzu fa lokacin sallan isha ne”
ta faɗi haka cike da mamakinsa, tasan dai shiba mutum ne dayake da saurin bacci ba.

Hanu yasa yaɗan murza idanunsa, kansa kawai ya kaɗa mata batare dayace da ita komaiba yakoma jikinta ya kwanta.  Yana lumshe idanunsa ladanin masallacin kusa da gidansu yasoma kwaɗa ƙiran sallah’n Isha.   Jiki babu ƙwari haka yayi alwala yawuce masallaci..

Koda ta idar da sallah batayi yunƙurin tashi akan sallayan ba, zama tayi tana me rero karatun Al’Qur’ani ahankali. 

Yana shigowa ta rufe Al’Qur’ani’n domin dama takai ƙarshen suran da take karantawa.

Direct bathroom ya wuce,  tanajin ƙaran ruwa tasan wanka ƴakeyi..     Bawani jimawa sosai yafito daga shi sai towel ɗaure aƙugunsa,  kallo ɗaya tayi masa ta ɗauƙe kanta, har yau bata iya jure ganinsa a haka, tashi itama tayi ta wuce bathroom ɗin donyin wanka.

Dogon wandon jeans kawai ya sanya ajikinsa haɗe da feshe jikinsa da turarensa me daɗin ƙamshi..    Kwanciya yayi lamo agadon haɗe da lumshe  kyawawan idanunsa.

daga ita sai wani ɗanƙaramin towel tafito ɗaure ajikinta, yanzu kam bata wani jin kunyarsa sosai, tana iya fitowa gabansa a haka, sai dai idan taga ya kafeta da idanu, sai taji gaba ɗaya tayi wani irin da ita.      Kallonta yayi yakuma sake lumshe idanunsa, yayi imani  idan yaci gaba da kallon wannan haɗaɗɗiyar surar tata zata iya zautar dashi.

Turare kawai ta shafa ajikinta, ko sleeping dress batasanya ba, yau kuma da towel takeson kwana,   kashe musu wutan ɗakin tayi ta kunna musu na bacci, wanda bashida haske sosai.   

A maimakon tanufi  gefensa ta kwanta, sai ji yayi ta haye kansa. 

“Wayyo mama lutiya zata karyani!” yafaɗi haka aɗan shagwaɓe.
Sake sakar masa duka nauyinta tayi akansa, haɗe da cusa kanta cikin wuyansa.

“Kai nauyinka baisa na karye ba sai nine zan karyaka, ko kamanta kafini nauyi”     taƙare maganar tana me manna masa wani irin hot kiss akan wuyansa.

Lumshe idanunsa yayi sosai yaji kiss ɗinnata ya ratsa shi.

“Wai yaushe kika zama haka ne princess?”  yatambayeta, don harga Allah kwana biyun nan yana mamakinta.

Cikin rashin fahimtar maganan nasa tace  “Bangane ba”

“Naga ne kindaina jin kunyana, sannan kuma nima da nake da kunyan nema kike ki lalatani ki maidani marar kunya”

Cizo takaimasa akan ƙirjinsa, wanda yasanya sa sakin wata ƴar ƙara.

Yana dariya yace
“To ƙarya nayi ai gaskiya nafaɗa, yanzu bakyajin kunyana ko kaɗan, har kaya kike cirewa a gabana…”

Wani cizon takuma kaimasa batare da ta bari yaƙarisa abunda yakeson faɗa ba,   da sauri yatureta  takoma ƙasansa shikuma yazama yana samanta, yayi mata rumfa da kirjinsa, duka hannayenta yakama yariƙe acikin nasa.

Cikin dariya ta soma ƙoƙarin ƙwace kanta daga jikinsa don talura cizon da tamai yakeson  rama wa.

“Dan Allah kayi haƙuri bazan ƙaraɓa!” tafaɗi haka aɗan tsorace dan ta lura dagaske cizonta zaiyi.

“Ae babu maganar haƙuri yarinya, aƙirji kika cijeni,  nima kuma dan haka aƙirjinki zan cijeki”    yafaɗi haka yana me warware towel ɗin dake jikinta.

Cikin dariyan data kasa hanashi fitowa tashiga yi masa magiya amma yace sam shi sai ya rama.

Yana ɗaura bakinsa akan ƙirjinta, tayi shiru  lokaci guda ta shiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, harwani lumshe idanunta take tsabar daɗin abun da yakeyi mata da takeji,    shikuwa dagangan yayi mata haka so yake ya tsokalota sai yayi mata wayo yayi baccinsa, hanunta tasanya ta ɗago kansa,   wani irin kallon tayi masa wanda ya rikirkitasa,      bakinsu ta haɗe waje ɗaya, atare suka soma sucking lips ɗin juna,   shida yake shirin mata wayo sai gashi ya susuce alokaci ɗaya, har yazo yafita ɓuƙata…..        Bargo yaja ya rufe musu duka jikinsu, yana kwance akanta  bacci me daɗi ya ɗaukesu…..


ZAID

Tunda aka sallamosu daga asibiti baice da kowa ƙala ba,  haushin kowa yakeji,  tuƙuƙin baƙin ciki zuciyarsa keyi masa, ji yake yatsani kowa, bayamaso wani yashigo cikin lamarinsa..

Zaune yake a cikin falonsa, dagashi sai 3 guater jeans ko riga baidashi duk da kuwa irin sanyin  da ake busawa a gari amma shi haka yake zaune a tuɓe, bawai kuma don bayajin sanyinba taurin kai dana zuciya ne kawai irin nasa ya hanasa suturta jikinsa. 

Ƙafansa nakan rug yayinda kansa ke kalllon sama ya lumshe duka idanunsa,     sake muskutawa yayi akaro na barkatai, haɗe kuma da ƙara ƙanƙame idanunsa da suke a lumshe,  waishi adole so yake yayakice tunanin Zahrah acikin zuciyarsa, amma duk yanda yaso cire tunanin nata  acikin ransa ya kasa,   hanu yasa ya ɗan bugi kansa da ƙarfi,  dai dai lokacin Afrah tafito daga cikin ɗaki  daga ita sai wata ƴar ƙaramar riga dake sanye ajikinta, ko guiwarta rigan bata wuce ba.

Wani irin ƙamshin turaren dayaji acikin hancinsa ne yasanya sa buɗe idanunsa,   ya watsa su akanta, kallonta yashigayi daga sama har ƙasa.   “gatanan dai kamar wata ƴar kaza amma shegiya sai fitinan tsiya” yafaɗi haka acikin zuciyarsa, saboda ya lura kanta yana rawa, nema take ta shigarmai rayuwa taƙarfin tsiya, kuma zaiyi maganinta ne.

Afrah kuwa zuciyartane tashiga dukan uku uku, tsoronsa ne yasake shiganta bama kamar yanda taga idanunsa sun juye sunyi jajur dasu,  harta juya zata koma ɗaki, saikuma ta tuno da shawarar da ƙawarta Asma ta bata, Asma tace mata ” Zaid ɗan duniya ne yanason mata sosai, saboda haka tayi duk yanda zatayi ta shawo kansa ta hanyar nuna masa surarta a fili, idan ta nuna masa bata da kunya zasu dai dai ta”   tunowa da waƴannan kalaman na Asma yasa Afra taji tasamu ƙwarin guiwa..    Sanja takunta tayi  zuwa wani salo da ban, direct wajen dayake kishingiɗe ta nufa tana me motsa kowani gaɓa dake jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button