NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Jikin Afrah ne ya ɗauki tsuma, take ta fashe da wani irin kuka me taɓa zuciya. 

“Wayyo Allah na, nashiga uku, me zancewa Zaid? kaicona, nakasa haƙuri, gashi yanzu na jawa kaina”    abun da Afrah ke faɗa kenan acikin zuciyarta,  gaba ɗaya tsoron ma tashi daga kan gadon take, da ƙyar ta iya jan bargo ta rufe jikinta dashi.

Ruwa ne ke dukan kansa,  yana tsaye agaban shower kamar wani statue,  iyaka ƙololuwar ɓacin rai, yau ya shigesa,   baitaɓa tunanin zaiji ciwo acikin zuciyarsa, wai dan yasamu Afrah ba a cikakkiyar virgin ba, sai gashi abun ya juye tunaninsa.

“Ashe dama haka maza sukeji, idan basu samu  matarsu a cikakkiyar budurwa ba?” yatambayi kansa.

“ZAHRAH”

itace wacce  tafara faɗo masa acikin ransa,  take fyaɗen da yayi mata yashiga dawowa cikin kansa filla filla, tamkar alokacin komai ke wakana haka yaji acikin jikinsa,    da sauri yasanya hanu ya kama kansa, haɗe da kurma wani uban ihu,   yama manta da cewa acikin toilet yake.    

Wani irin nadama ne me girma  ya ruskesa  acikin  zuciyarsa,   sai yanzu ya tabbatar da cewa bai kyautawa Zahrah ba, yaku ma cutar da ita cutarwa me girma, ya ruguza mata alfaharinta.

“Meyasa yayiwa Zahrah haka?  me yasa yarabata da budurcinta? wani irin cutarwa ne yayiwa Zahrah haka?” yatambayi kansa cikin tsananin tsana da ƙyamar kansa.

“I hurt you Zahrah, why do i did this to you?  I’am stupid, i dont have sense, meyasa zan aikata haka?  kaicona dana cutar da rayuwarki,  na gusar miki da farincikin ki, na hanaki mallakawa mijinki budurcinki, na ƙwace budurcinki taƙarfin tsiya, forgive me, i hate my self, because of what i did to you,  natsani duk wata rayuwar duniyar nan, rayuwa batamin daɗi Zahrah!!”   cikin wani irin murya me haɗe da sautin kuka Zaid ke faɗan haka.   

Haƙiƙa yau baida abun da zaice, yasan Allah  ba azzalumin kowa bane, sai wanda ya zalunci kansa, gashinan shi ya zalunci kansa, kuma yagani,  gashi yanzu Allah ya haɗashi da wata ballagazar mace, wacce ta raba budurcinta ga mutanen titi,  yanzu ga abun da Zina ta haifar masa, bayajin son Afrah ko ɗigo acikin zuciyarsa, amma kuma yaji matsanancin ciwon samunta a haka da yayi, to idan dai shi yaji ciwon samunta ahaka, me mijin Zahrah kuma zaice? shida yake so da kuma ƙaunarta.

Jingina kansa yayi da jikin bangon toilet ɗin,  yayinda ruwan dake fitowa acikin shower ke dukan bayansa.  Rumtse jajayen idanunsa yayi, haɗe da sanya haƙoransa ya danne laɓɓansa, jiyake kamar yata gwara kansa ajikin bango, har sai kan ya rabe gida biyu, koda zaiji salama, acikin zuciyarsa,      hanunsa na dafe da saitin zuciyarsa, dake yi masa zafi,   yajima a tsaye ruwa na dukansa, har sai da jikinsa yasoma karkarwa kafun ya kashe shower’n….

Buɗe ƙofarsa, yayi dai dai da bugawan zuciyar Afrah, take jikinta yacigaba da karkarwa kamar anjona shocking.

Ko kallon inda take baiyi ba,  direct gaban drawer ɗinsa ya nufa, wata farar T-shirt ya ɗauka ya sanya ajikinsa.

Ganin baice da ita komai ba, yasanya ta daɗa firgicewa, batasan me ze mataba nan gaba, cikin muryarta me ɗauke da tarin tsoro, haɗi da fargaba tace.  

“Dan Allah kayi haƙur……”

“Get out!!”

yafaɗi haka batare daya bari ta ƙarasa maganar dake cikin bakinta ba.

Cikin kuka takuma cewa

“Dan Allah kayi….”

“I say get out!!!”

yafaɗi haka atsananin tsawace, har sai da Afrah taji ƴaƴan cikinta sun kaɗa.

Gaba ɗaya ta ruɗe ta firgice, yanayin yanda taga idanunsa sunyi jajur dasu, shine abun da yafi komai ɗaga mata hankali,   da gudu ta fice daga cikin ɗakin, ko kayanta bata tsaya ɗauka ba, sai blanket ɗin da tayi amfani dashi wajen rufe jikinta.

Kwalbar turaren dake riƙe a hanunsa ya yi wurgi dashi,  zuwa wajen wani ƙaton mirror wanda ke kafe ajikin bango, take mirror’n ya fashe, haɗe da tarwatsewa a ƙasan tiles.

Wani irin huci yake fitarwa ta bakinsa, yayinda yasanya duka hannayensa ya kama ƙugunsa,  jiyake gaba ɗaya duniyar na juya masa.
“Me ake da irin wannan  rayuwa, me ɗauke da takaicin?” yatambayi kansa.

Idanunsa ya sauƙe akan fridge ɗin dake ɗakin, wanda yake a cike da kwalbar wine ɗinsa,   a irin wannan halin dayake ciki, wine ce kaɗai zata iya bashi nutsuwa, duk da yasan ba lallaine ta iya ciresa acikin ƙuncin dayake ciki ba, amma tabbas zata iya rage masa damuwa, sai dai kuma bayajin aduniya zai iya ƙara aikata wani abu na saɓon Ubangijinsa,  ko a iya nan Allah yaɗauki rayuwarsa, haƙiƙa ya jarabtu, soyayyar Zahrah kaɗai da Allah, yasanya masa, yazamemasa babban jarabawa acikin rayuwarsa.

Zama yayi a bakin gado, haɗe da bin blanket ɗin dake shimfuɗe akan gadon, da kallon takaici,   bakomai ne yafaɗo masa arai ba, kamar randa yayiwa Zahrah fyaɗe, haka gaba ɗaya tsakiyar gadon ya ɓaci da jininta,  yasamu Zahrah a cikakkiyar budurwa. 

“Yayi gaggawa? me yasa bai bari ya amshi budurcinta ta hanyar aure ba?”  wasu siraran hawayene suka fito daga cikin idanunsa, suka sauƙa akan ƙuncinsa, sakamakon tunowa da yanda ya farke Zahrah da yayi.

Ahankali ya taka ƙafarsa ya ƙarasa gaban wani tangamemen hotonta, dake liƙe ajikin bangon ɗakin.

Zama yayi agaban hoton haɗe da cewa.
“Kiyafemin Zahrah, a yanzu nayi nadama marar amfani,  ni dakaina namiki fyaɗe, nidakaina nasa aka je har ƙofar gidanku aka ya da ke,  meye amfanina Zahrah?  me yasa nazamo mugu maƙuntaci agareki?  nagodewa Allah dayasa baki aureni ba, domin ban cancanci zama miji a gareki ba,  ni ban dace dake ba Zahrah, to tayama zan dace dake? ninefa wanda yayi miki fyaɗe, nine azzalumin dana rufe idanuna, na aikata ba dai dai ba akan ki,  to taya zaki yarda ki aureni, a’a ko kin yardama ni bazan yarda ba, domin ni dake bamu dace ba, bazan yarda nasake cutar dake akaro na biyu ba,  inasonki Zahrah so ba irin wanda kika sani ba, inamiki son da aduniya banayiwa kowa irinsa, sonki ajinina yake,  har abada bazan taɓa daina sonki ba,   ki hukuntani Zahrah, kimin duk irin hukuncin da kikeso,  nacancanci ki hukuntani Zahrah, ko kasheni kikayi bazanga laifinki ba, saboda nasan koda kasheni ɗin kikayi bazaki huce daga abun dana aikata a gareki ba,  ki ɗaga hanu ki dakeni Zahrah, kice Zaid natsaneka, banasonka, ki faɗi haka agareni Zahrah dan Allah, ki faɗa ko zanji salama acikin zuciyata!!!”
  
kuka sosai Zaid keyi kamar wani yaro ƙarami yana me rungume da hoton Zahrah acikin ƙirjinsa.

Yayi kuka irin wanda bai taɓayin irin saba, yayi kuka wanda har sai da ya haifar masa da ciwon kai,    kusan sama da awa ɗaya ya ɗauka yana zaune, agaban hoton Zahrah, da ƙyar ya’iya jaye jikinsa a wajen, ya faɗa bathroom,  alwala yayi haɗe da buɗe kofar yafito, idanunsa sunyi luhu luhu dasu, kallo ɗaya zakayi masa kasan ya sha kuka ya ƙoshi.

Blue ɗin jallabiya yasanya, direct ya wuce masallaci, duk da cewa kowa yagansa zai gane cewa yana a cikin damuwa, amma sam baidamu da hakan ba, uban kowa ma yasan yana cikin damuwa, shiba damuwarsa bane,  matsalansa ma kaɗai ta ishe sa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button