SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Manage…….
28/October/2019
*MRS SARDAUNA*
????????????????????????????????????????
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*WRITTEN by*
phatymasardauna
????Mrs Sardauna????
Dedicated to my lovely brother Khabier
????Kainuwa Writers Association
*WATTPAD*
@fatymasardauna
Editing is not allowed ????
Chapter 15
Zaid kuwa ba shine ya farka daga bacci ba, sai wajen 8:30 am, abun haushi da takaicin ko sallan asuba baiyi ba, bathroom yashiga yasakeyin wanka, haɗe da ɗauro alwala, sallaya ya shunfuɗa haɗi da soma kabbara sallah, kokunya bayaji domin kuwa rana tafito faɗe faɗe, amma wai sai a lokacin yake sallan asuba, Allah wadaran halinka Zaid, ai dama ibada da iskanci basa taɓa haɗuwa waje ɗaya, babuma kamar zina, ya Allah kakaremu daga sharri da aikata zina, ameen….
Tsab yagama shirya kansa cikin wasu haɗaɗɗun riga da wando ƴan kanti, maroon colour, sosai kayan suka amshi jikinsa, kasantuwarsa mai farar fata, wandon irin pencil ɗinnan ne yayinda rigar takasance mai aninaye a gabanta, sannan tana da guntun hanu iyaka guiwa, facing cap maroon colour yasanya a kansa, ta ke kyau da kwarjininsa suka sake bayyana, haƙiƙa Zaid ya haɗu tako wani fanni, matashine maiji da gaye gakuma kuɗi da suka ɗaure masa gindi, feshe jikinsa da turarukansa masu ƙamshi yayi, haɗe da ɗaukar wayarsa ya zura cikin aljihun wandon sa, kallonsa yakai kan Salima da take ta sharan bacci, wani munafukin murmushi yayi haɗe da buɗe wata ƴar ƙaramar drower yaciro rafan kuɗi ƴan dubu dubu ɗauri ɗaya, rufe drower’n yayi haɗe da sa mata key,,, wurgi da kuɗin hanunsa yayi zuwa jikin Salima, haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, bakinsa ɗauke da fito,, a ransa kuwa cewa yake “banzar yarinya ko daɗi ma bata da shi, mcheeeww nidai naja mawa kaina, a kwashe kwashena naje nasamu dusar mata !, amma bakomai zan fanshe ajikin kine sugar baby, wallahi duk randa na kamaki saina miki raga raga !!” kaitsaye wajen motarsa ƙirar BUGGATI yanufa, yana shiga cikin motar yayi mata key, tuni mai gadi ya wangale masa tankamemen gate ɗin gidan, shikuwa bawani ɓata lokaci ya cilla hancin motarsa waje…. Kaitsaye gidansu ya nufa, domin tunjiya Dadynsa keta ƙiransa akan yazo yanason ganinsa,, tafe yake acikin mota amma earpiece ne saƙale a kunnensa yanashan waƙa, bayan kiɗan dake tashi acikin motar tasa, gudu yake tsulawa baruwansa da wanda ke bayansa ko gabansa, a haka har ya’iso cikin gidan nasu, yanafita acikin motarsa yanufi ɓangaren mom ɗinsa,, zaune take akan kujera, tasha ado cikin shiga ta alfarma, yayinda wata yarinya ke duƙe a ƙasanta tana aikin yimata tausa aƙafafunta, daga kaganta kaga zallan hutu da jindaɗi, domin kuwa zoben hanunta kaɗai ya’isa yasai maka babban gida mai kyau awani garin,, tana ganinsa tasaki murmushi haɗe da kafesa da’ido, bakomai yasa tayin hakanba, face ƙoƙarin gano maike damunsa, dan taga fuskar tasa a ɗaure tamau,, “barka da hutawa Mom” Zaid yafaɗa dai dai lokacin daya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon, Mom bata amsa masa ba saima kallonsa da taci gaba dayi, a hankali Hajara ta ɗago idanunta ta saci kallon Zaid,
“Zanci ubanki idan baki daina kallo naba shegiya munafuka mai baƙar fuska !!” Zaid yafaɗa cikin hargowa, tuni Hajara ta ruɗe ƙafofinta sun soma rawa, domin tabbas tasan yakamata tana kallonsa ne, itakam yau tashiga uku, taƙirawa kanta ruwa,, “ke Hajara tashi ki wuce ciki, anjima kya dawo ki ci gaba da matsamin ƙafan” Mom tafaɗa, sumi sumi Hajara ta tashi daga duƙen da take hartana jin tuntuɓe tsabar sauri tabar falon,,
“Wai Zaid maiyasa kake hakane ? dudduniya babu yarinyar daka tsana kamar Hajara, waima ni ba wannan ba, kokasan cewa ina da labarin duk irin abubuwan da kake aikata wa, sai yaushe zaka girmane Zaid ? ni bance kada kayi abunda kake so ba, amma kadaina bin mata dan Allah Zaid, wannan bahalin mutanen kirki bane !” Mom tafaɗa cikin rarrashi,, ko gizau Zaid baiyiba balle ya amsawa Mom,, bata damu ba domin dama tasan zaiyi wuya ya amsa mata ɗin,, bata sake ce dashi komaiba, saima tashi tayi tabar masa falon, domin bazata iya da wannan baƙin rannasa ba, ace mutum shi komai kayi masa bazaka burgesa ba, shegen baƙin hali da gadara, tamkar wani basarake,,, Mom na tafiya, wayar Zaid tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, bai ɗauki wayar ba saima tashi da yayi yafice a falon, kai tsaye babban falon Dady ɗinsa ya nufa…. Maganar dai ɗaya ce, shine yafito da matar aure,, “to” kawai Zaid yacemawa Dady’nnasa, sun ɗan taɓa hira akan harkan kasuwancinsu, kafun daga bisani Zaid yayi mawa Dady’nnasa sallama yatafi…….
gaba ɗaya yau Husnah takasa gane kan Zahrah domin kuwa, duk bayan minti kaɗan sai Zahrah ta saki murmushi ita ɗaya… Yanzuma zaune suke akan wata kujera da akayita da suminti, irin nazaman ɗaliban cikin University,, gyara zama Husnah tayi haɗe da maida hankalinta ga Zahrah… “SOYAYYA !!” Husnah tafaɗa,tana mai tsare Zahrah da idanu,, murmushi Zahrah takumayi haɗe da kamo hannayen Husnah cikin ɗan yanayin damuwa tace “bansan yanda a keyinta ba, impact ma bansan ya’ake gane ankamu da’ita ba, amma tabbas inaga nafaɗa a soyayya ƙawata, domin kuwa dare da rana koda yaushe tunaninsa baya barin zuciyata, da gaske inasonsa Husnah ? ” Zahrah ta tambaya lokacin da ƙwalla suka cika idanunta,, murmushi mai sauti Husnah tayi haɗe da cewa ” Lallai ko wanene shi yacika JARUMI acikin JARUMAI da har ya’iya sace zuciyar kyakkyawar ƙawata, tabbas ko tantama babu Zahrah kinkamu da son sa, wanene shi ? a’ina yake ?”
“har yau bansan wanene shiba, Husnah, bansan koshi ɗin waye bane, amma tabbas nasan cewa yafi ƙarfin ajina, amma yazanyi tunda shiya koyamini sonsa, bantaɓa soyayya ba, a kansa nafara shiyasa nake jin sonsa fiye da komai a gareni ” Zahrah ta ƙare maganar lokacin da hawaye suka wanke mata fuska, ” Kuka banakibane lover girl, nidai gaskia yakamata kinunamin jarumi’n nan domin nabasa babbar kyauta…. ” Ɗan murmushi kawai Zahrah tayi batare da tasake cewa komaiba, sosai Husnah tabata shawara dakuma ƙarin haske akan soyayya,, koda aka tashi a makaranta, cike da tarin tunanin Zaid Zahrah ta dawo gida, a zuciyarta kuwa cewa take “Inama da zai dawo yau tasake ganinsa, har abada bazata gajiya da ganinsa ba……”
“Hahahahaaahha gaskia SHU’UMI baka da kyau, wato dai kayi rantsuwa cewa saika lalata musu ƴa ko, hmm banga laifinka ba, domin kuwa da fari nima na kwaɗaitu da babyn kuma wallahi har gobe ina tsananin sha’awarta, amma tunda kamin shigar sauri ba damuwa, idan kaci ka rage naci sauran koba haka ba guys ” Bash yafaɗa yana dariya,, wani irin abune ya tokare maƙoshin Zaid, bawai don wani abu ba, saidon kalaman da Bash ke faɗa, wai idan yaci ya rage yabasa ya ƙarasa, lallaikam, ai dudduniya babu wanda zaici Zahrah bayanshi,,,
Kallonsa Bash yakumayi haɗe da ɗage gira cikin shaƙiyanci yace “SHU’UMI yadai kodai ka kamune ?” wata uwar harara Zaid ya wurga mawa Bash cike da miskilanci yace “Banshirya faɗawa soyayya yanzuba, babuma so a tsarina, sai dai ina matuƙar sha’awarta fiye da komai aduniya, soon kuma komai zai dai dai ta “
gaba ɗaya abokan Zaid suka kwashe da dariyan mugunta, domin sarai sunsan waye Zaid idan yace saiyayi abu babu makawa sai yayi, haka kuma duk macen daya ɗana mawa tarko, to tabbas saita faɗa,,, haka dai sukaita zuba iskancinsu……