NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda tashiga cikin ɗakinta take kuka,  yau ne  karo na farko a rayuwarta, da tayi babban nadamar bada kanta da tayi a waje, yau tayi nadama ƙwarai,  yau ta ga sakarci dakuma wautanta, da ta ɗauki kyautar budurcinta sukutum, ta dan ƙawa wani banza, wanda yayi mata ƙaryan zai aureta,  me ake da irin wannan rayuwar, wayewar banza, wayewar wofi,  taɗauki zugan ƙawayenta, da suke ce mata wai inmace batasan daɗin sex ba bata waye ba, ta biyewa son zuciyarta taje ta bawa wani banza kanta, batare da sadaki ba ya haye kanta, ya karɓi budurcinta, batare da ko da sannu ba,  wace irin banzar hallakakkiyar waye wace wannan? wayewar da zata saka kaji kunyar Allah da ta mutanen duniya, kaicon irin wannan wayewar, tir da irinta,    bata taɓa manta yanda su Asma ke zugata akan cewa wai yakamata ta bada kanta ga saurayinta Ameer, ta kuma san duniya,  duniya ma ta santa, har cewa suke wai ita baƙauyiya ce, saboda kawai bata yarda wani namiji ya taɓa jikinta,  haka suke wareta acikinsu, haka suke nuna mata kyara, wai don kawai bata bari maza suna taɓata,  tabiye sharrin zuciya data ƙawaye, ta kuma  ɗauƙi shawararsu, ta yi watsi da mutuncin kanta,  gashi yanzu tun aduniya, ta shiga kunyar mijinta, takuma shiga halin nadama da danasi, ga kuma tozarcin da zata fuskanta daga wajen mijinta.

Zama tayi daɓas aƙasa tashiga rera kukanta, haɗe da tsinewa Asma da ma duk wasu ƙawayenta, da sukayi ruwa da tsaki, wajen tsundumata, cikin halakan data faɗa, shikuwa saurayinta Ameer, wanda shiya fara saninta ƴa mace, ta zuba masa tsinuwa yafi guda ɗari biyu,   da ƙyar ta iya lallaɓan kanta tashiga toilet donyin wanka..

Yajima acikin masallacin kafun ya dawo gida, abun dayajima baiyiba kenan, wai yaje masallaci yajima har haka,  karatun Al’Qur’ani yayi, kuma da yardan Allah yaɗan samu salama acikin zuciyarsa..

Afrah najin shigowarsa cikin gidan,  ƙafafunta yasoma rawa, take taji wani irin ciwon ciki ya kamata,  mugun tsoronsa takeji, tun ada ma, balle yanzu kuma da wannan abun yashiga tsakaninsu, ta tabbatar sai yakasheta acikin gidannan, kuma ya kashe banza.

Yana shiga cikin ɗakinsa, ya ɗauki magungunansa yasha,  tashi yayi yafice daga cikin ɗakin nasa, direct ɗakinta ya nufa.

Tanajin motsin ana buɗe ƙofarta ta miƙe zunbur, take wani irin fitsari ya zubo mata, tsabar tsoro, aikuwa tana jefa idanunta, cikin nasa, taji numfashinta, na shirin ɗaukewa.

Da rinannun idanunsa yake kallonta,  ganinta da yayi yasake tuna masa ɓacin ransa,  jiyake ya tsaneta, amma kuma yazama dole yayi mata tambayoyin dake cikin ransa..

“Zauna” yafaɗi haka cikin dakiya.

Jikin Afrah na rawa ta zauna aƙasan tiles.

Ƙafansa ɗaya yasanya, yataka kan gado, haɗe da ɗan ranƙwafowa.

“Dama ke karuwa ce?”  first tambayar daya fito daga cikin bakinsa kenan.

Ƙirjin Afrah ne ya buga, take hawaye suka ɓalle akan fuskarta, kanta tashiga girgizawa alamar

“A’a”

Laɓɓansa ya cije cike da takaici yace.
“Da bakinki nakeso, ki bani amsa bada kai ba.”

“A….a wallahi ni…..ba..ba..ka..ruwa..bace!” murya a sassarƙe tabashi amsa.

“Kinsan me ake ƙira da karuwa?”
Yatambayeta.

Dasauri ta kaɗa kanta, saikuma tatuna da abun dayace mata, baki na rawa tace “Karuwa itace mebin maza, wacce take zaman kanta”

“Good, ashe kinsan mene ake ƙira da karuwa, kenan ke ɗin karuwa ce?”

Da sauri tace “Wallahi niba karuwa bace”

“Idan ke ba karuwa bace, dan ubanki ina kikai budurciki!!!” amatuƙar tsawace yayi maganar, saboda ya matuƙar harzuƙa.

Guntun fitsarin da take ta riƙewane ya silalo, tsabar ta tsorata,    ƙyarma tafara tamkar wata mejin sanyi, tsabar tsorata da yanayinsa da tayi, ta makasa ce dashi komai.

“Shirun da kikayi ya nuna alamar cewa eh ke cikakkiyar karuwace, mazinaciya, me kike nema arayuwarki, kina ƴar ƙaramar yarinya dake?” yatambayeta yana me ƙare mata kallo.

Kanta tashiga girgizawa, akaro na barkatai.

“Kayarda dani, wallahi niba karuwa bace, bantaɓa karuwanci ba!” tafaɗi haka tana kuka.

“Okay to tunda dai kince ke ba karuwa bace, ba naci ubanki, wataƙila zaki faɗamin inda kika kai virginity ɗinki” yafaɗi haka yana me ƙoƙarin zare belt ɗin wandon jeans ɗin dake sanye a jikinshi.

Da gudu ta rarrafo ta ƙaraso garesa, zubewa tayi akan ƙafafunsa tana kuka.

“Dan Allah kayi haƙuri, kayafemin, wallahi sharrin shaiɗanne, dakuma na zuciya, amma bantaɓa zaman karuwanci ba!” kuka take wiwi kamar wacce akace uwarta ta mutu.

Tsayawa yayi cak yana me kallonta, kuka take tsakaninta da Allah.

“Mene naka najin haushinta Zaid? mene naka nacewa zaka daketa? idan ita karuwace kai menene?”  wata zuciyarsa ta tambayesa.

Rumtse idanunsa yayi haɗe da cije laɓɓansa,  da ƙyar ya iya janye ƙafafunsa ya zauna, abakin gado.

Afrah dake duƙe a ƙasa tana kuka ya kalla.

Cikin wata irin murya a cushe yace.  “Afrah!”

Dasauri Afrah taɗago fuskarta ta kalleshi, duk taɓata fuskar  ta da majina, ansha kuka anƙoshi.

“Zo” yace da ita ataƙaice.

Babu musu ta ƙaraso gabansa ta durƙusa.

“Meyasa kika zaɓi  banzatar da mutuncinki a waje Afrah?” tambayar dayayi mata kenan, sai dai wannan karon, ba acikin tsawa yayi mata tambayar ba.

Cikin kuka Afrah tasoma cewa “Bansan dalili ba, amma nabiyewa son zuciyata ne kawai, nabiyewa zugan shaiɗan da kuma shaiɗanun ƙawaye, najefa rayuwata a halaka,  nasan irin wannan ranan zatazo, amma bantaɓa kawo cewa al’amarin zai kai har haka ba, domin wanda ya fara sanina amatsayin ƴa mace, yayimini alƙawarin aure, saboda haka bantaɓa kawowa araina cewa rashin kasancewata ba a  budurwa ba zai kawo min wani abu, saboda na ɗauka wanda yafara sanina a cikakkiyar ƴa macena  shine wanda zai aureni, ashe shima ƙarya yakemin, ba aurena zaiyi ba, yayi hakane kawai,dan na amince nadinga bashi kaina, aduk sanda ya buƙata!” taƙare maganar tana me tsananta kukanta.

Rumtse idanunsa yayi, haɗe da cije laɓɓansa, akaro na sau babu adadi.

“Banason kuka” yafaɗa ataƙaice yana me kawar dakansa gefe.

Duk da cewa kukan nacinta, amma haka ta haɗiye, tasoma ƙoƙarin yin shiru.

“Kinyi wanka?”  yatambayeta still kansa na na kallon wani wajen.

“Eh” tafaɗa murya a raunane.

Miƙewa yayi daga zaunen da yake, haɗe da dubanta.

“Zanshiga na kwanta, banason naji koda motsinkine, ki zauna anan ɗakin, banason damuwa”  yanakaiwa nan azancensa, yasakai yafice daga cikin ɗakin.

Afrah kam kan gadonta ta haye taci gaba da rera kukan danasani, ahaka har baccin wahala ya ɗauketa.

Zama yayi akan gado, haɗe da ɗaura idanunsa akan hotonta, hawayene suka zuraro daga cikin idanunsa, abune mawuyaci yadaina sonta, duk da yasan a yanzu ta haramta agareshi, kuma yana gudun ɗaukarwa kansa zunubi, amma kuma akan sonta, baya iya control ɗin zuciyarsa, akullum maganaɗisun ƙaunarta, ƙara fusgarsa take,  saidai kuma kamar yanda yaɗaukarwa kansa alƙawari, zai ci gaba da addu’a har Allah yakawo masa sauƙi da sassauci acikin zuciyarsa akan  soyayyarta..

(So ba ƙarya bane, So gaskiyane, amma kuma wanda baitaɓa yiba bazai gane ya yake ba, haka kuma wanda baiyi zurfi acikin saba, bazai taɓa gane ya zafinsa yake ba,  ba acire so alokaci guda, a sannu komai yake gushewa,   ƙauna acikin jini take, bata taɓa gushewa, watarana a sannu so zai gushe, amma ƙauna tana nan.   Ku yiwa Zaid da Zahrah uzuri, wallahi soyayya ta wuce gaban kwatance, idan kanason abu baka ganin laifinsa, shi so hana ganin laifi ne,  meyin so shikaɗaine zai gane inda kalamaina suka dosa.)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button