SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

(Yau fejin nasu Zaid ne, bazamu waiwaya gidan Doctor ba, team Doctor da Zahrah i’am sorry)
9/february/2020
Fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
CHAPTER 108
Kaikawo take tayi a cikin kitchine ɗin, sauri take ta kammala aikinta, tsaye take acikin kitchine ɗin, tana wanke wani plate dake riƙe a hanunta, sosai nayi mamakin ganinta a haka, rigace irin T-shirt me faɗinnan sanye ajikinta, duka duka tsayin rigar ko rabin cinyanta bai ƙarasa ba, bata kuma sanya wando dan rufe cinyoyinta ba, wani irin slipper ne me kyaun gaske sanye aƙafarta, wanda aka ƙawata samansa da wani kyakkyawan follower,
Irin yanayin shigar nata yasanya tayi kama da irin yaran turawan nan.
Sam bata ji motsin shigowarsa ba, hakan yasa bata kawo cewa akwai wani mahaluƙi dake kallonta ba.
Sake gyara tsayuwarsa yayi, haɗe da jingina bayansa, da jikin ƙofar fita daga kitchine ɗin, sosai tayi masa kyau, babu abun daya fi ɗaukar hankalinsa ajikinta, kamar hips ɗinta, ga santala santalan cinyoyinta, da suka bayyana kansu, gwanin ban sha’awa, gaskiya komai na Zahrah me kyau ne, ta cika mace hundred percent, yajima yana fata da burin samun cikakkiyar mace, me cikar halitta ka marta, a matsayin matar aurensa, sai gashi Allah Ya dubesa ya basa Zahrah.
Ɗan tsayawa tayi, haɗe da sanya hannayenta bisa ƙugunta, tana me sauƙe numfashi, a hankali, da’alama dai akwai gajiya a tattare da’ita.
“Kin gaji ko?”
Cike da mamakin jin muryarsa, acikin kunnuwanta, da tayi ta juyo, tana me fuskantarsa.
Murmushin sa me kyau, ya sakar mata, haɗe da soma takowa zuwa gareta.
“Yaushe kadawo bansani ba?” ta tambayeshi, cike da tsananin mamaki.
“Najima da dawowa, nadai tsaya kallon abar sona ne” yafaɗi haka yana me lumshe gajiyayyun idanunsa, sosai yakejin gajiya ajikinsa, baƙaramin aiki yau yasha a office ba.
“Sannu da dawowa!”
tafaɗa tana sakarmasa murmushi.
Jawota cikin jikinsa yayi, haɗe da rungumeta, kansa ya ɗaura akan wuyanta, wata ajiyar zuciya, me ƙarfi ya sauƙe.
“Nayi kewarki sosai my lovely wife!” cikin murya, me sanyi, ya yi maganar.
Murmushi takuma sakar masa, haɗe da langwaɓar da kanta gefe gudu. “Nima nayi kewarka Hubby na!” cikin salo ta ƙare maganar.
“Dagaske kema kinyi kewata my wife? nifa dukanki nayi kewarki!” yafaɗi haka yana meyi mata wani irin kallo, dake ɗauke da wani tarin ma’anoni masu yawa.
Ganin kallon dayakeyi mata, yasa tasaki murmushi me ɗan sauti, ƙoƙarin janye jikinta daga nashi tasoma yi.
Ƙam ya riƙeta, haɗe da sake mannata acikin chest ɗinsa, da alama dai bayason tacire jikinta acikin nasa jikin.
“Uh dan Allah, Kabarni na ƙarisa aikina, kuma mafa duk ƙauri nake, amma kaketa mannani a jikinka, kaɗan bari nayi wanka kaji!” tayi maganar cikin yanayi na lallashi, tasani sarai, idan dai ba lallashinsa tayi ba, to bazai bari ta kammala aikin data fara ba.
“Nidai naƙi wayon, kuma ni banji wani ƙauri da kike ba, princess nadawo amatuƙar gajiye, gashi kuma ganinki ahaka yasake ɗaura min wani gajiyan, please kiyarda ko 30 minute ne kiban, ina da buƙatarki fa akusa dani….”
Bata bari ya ƙarasa zancen nasaba, tayi saurin toshe masa baki da tafin hanunta, shagwaɓe fuska tayi, haɗe da marerece idanunta, kanta ta girgiza masa akan kada yace komai.
Hanunsa takama, suka fice daga cikin kitchine ɗin, haka yake binta tamkar wani raƙumi da akala, suna shiga cikin bedroom, ta zaunar dashi akan gado, bathroom ta wuce direct, ruwan wanka me ɗan ɗumi, ta haɗa masa acikin bathtub, haɗe da sanya masa turaren wanka, me daɗin ƙamshi, acikin ruwan, take banɗakin ya gauraye da ƙamshi, tana fitowa daga cikin bathroom ɗin, ya kafeta da manyan idanunsa, durƙusawa tayi ta cire masa takalmi, da kuma safar dake ƙafarsa, ita da kanta tacire masa suit ɗin jikinsa, dakuma necktie ɗin dake saƙale a jikin wuyansa, Hanunta ta sanya, ta shiga ɓalle masa aninayen rigar dake jikin sa, ahankali ta zare masa rigar, shi dai haka ya tsaya, yana kallonta, yana me kuma lumshe idanunsa, lokuta zuwa lokuta, murmushine ya bayyana akan fuskarta, lokacin da idanunta, suka sauƙa akan faffaɗan chest ɗinsa, haƙiƙa yanada jiki me kyau, tasan hakan kuma, bazai rasa nasaba, da yawan gym ɗin dayakeyi ba.
Kallonsa tayi haɗe da sake sakarmasa murmushi, hanunsa ta kama daniyar janshi zuwa cikin toilet, da ƙarfi yajawo hanunnata, tafaɗa jikinsa, matseta yayi ajikinsa, haɗe da matso da fuskarsa gaf da tata.
“Ahakane zanje nayi wankan, bayan baki ciremin kaya ba?” yafaɗi maganar ƙasa ƙasa.
Cikin rashin fahimta tace.
“Wani irin kaya kuma, bayan wanda nacirema yanzu?”
Hanunta yakama, ya ɗaura akan belt ɗin dake saƙale jikin wandonsa, tsareta yayi da idanu, da’alama dai har wandon ma, so yake ita tacire masa da kanta.
Kunyan sane ya kamata, amma tasan wayon da zata masa.
“Naji zancirema, muje cikin toilet ɗin” tafaɗi haka tana nufar ƙofar toilet ɗin.
Jin abun da tace, yasanyasa, rufa mata baya, suna shiga cikin toilet ɗin tadawo baya, da sauri tafice daga cikin toilet ɗin, ta rufosa ta baya.
Dariya tashiga ƙyalƙyalawa, tana mejin daɗin wayon da tayi masa.
“I am sorry Hubby, kayi wanka kaji, banaje na kula da girkina, kada ya ƙone!” tafaɗi haka cikin muryar da ta tabbatar cewa zai jiyota.
Jin da tayi yana ƙoƙarin buɗe ƙofar toilet ɗinne, yasanya da sauri ta fice acikin ɗakin gaba ɗaya, tana dariya.
Murmushi me sauti shima yayi, kana ya girgiza kansa, waishi Zahrah zatayiwa wayo, hmmm.
Kwanciya yayi acikin bathtub ɗin , sosai yaji daɗin ruwan wankan data haɗa masa, ga ɗumi ga kuma ƙamshi me daɗi, a hankali gajiyarsa ta soma warwarewa.
Tana kammala girkin, ta zuba acikin manyan food flask, haɗe da jeresu cikin basket’s masu hanu, sosai takejin, gajiya ajikinta, amma yazatayi, tunda ita tasanya kanta, duka kwanukan datayi aiki dasu, saida ta wankesu tas, kana ta gyara kitchine ɗin nata, lokaci ɗaya komai na kitchine ɗin, yadawo tsab dashi.
Tana shigowa cikin ɗakin, bata ko kalli inda yake ba, da sauri ta faɗa cikin bathroom, sam bataso ma yaganta a haka, wujiga wujiga da ita, duk ƙamshin kayan girki take, ruwan ɗumi ta tara tayi wankanta, take itama taji rabin gajiyarta, ya kama gabansa, towel ta ɗaura ajikinta, haɗe da buɗe ƙofar bathroom ɗin tafito.
Tsayawa tayi tana kallonsa, Tsaye yake agaban dressing mirror, yayi matuƙar kyau, cikin sky blue ɗin, shaddan dake jikinsa, agogo yake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa, yayinda tulin gashin kansa ke ta faƙan ƙyalli, da’alama dai yasha gyara, da man gashi, na musamman, akan fuskarsa kuwa, ƙawataccen sajensa ne, ya samu waje, ya kwanta luf akan ƙuncinsa.