SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Wallahi duk wanda yace Dr.Sadeeq, bai haɗu ba yayi ƙarya” Zahrah tafaɗi haka acikin zuciyarta.
Dawo da kallonsa yayi gareta, fuskarsa ɗauke da murmushi yace. “Sannu da fitowa, Hajiyar wayo”
Itama murmushin tayi masa, haɗe da takowa zuwa garesa, hakanan ta tsinci kanta, da matuƙar son rungumesa, lokaci ɗaya ta faɗa jikinsa, haɗe da ɗaura kanta akan ƙirjinsa, shima dama nema yake, sosai ya matseta acikin jikinsa, tare da sanya hanunsa, akan bayanta, yana shafawa, a hankali, lumshe idanunsu, sukayi su duka, suna masu, sauƙe ajiyar zuciya.
“Kayi kyau sosai Hubby!” Zahrah tafaɗa cikin murya me sanyi.
“Nagode my princess!”
yabata amsa, yana me faɗaɗa, murmushin dake, kan fuskarsa, yanason Zahrah har acikin ɓargonsa, so sosai yakeyi mata, ko kaɗan baya fata Allah, Ya nuna masa, ranan dazai ɓata mata, alƙawari ya ɗaukarwa kansa, cewa Insha Allah, Bazai taɓa wulaƙanta Zahrah ba, koba komai itaɗin farincikinsa ce, sannan kuma tana da, wani irin girma, na musamman, acikin idanunsa, itace mace ta farko, daya fara sani, acikin rayuwarsa, itace macen data fara, jiyar dashi wani daɗi, wanda bai taɓa sanin akwai irin shi, acikin wannan, duniyar ba, Zahrah ta shayar dashi zumanta, wanda ɗanɗanonsa, keda wahalan mantawa, duk da cewa bai sameta, amatsayin cikakkiyar budurwa ba, amma haƙiƙa tanada wani, matsayi na musamman agareshi.
“Hubby!!”
taƙira sunansa cikin wani irin cool voice.
“Ummm princess ɗina, ya akayi ne?” yayi maganar yana me duban fuskarta.
Murmushin dake ƙara mata kyau, ako da yaushe idan tayishi, tasakar masa, haɗe da zare jikinta daga nasa, body lotion ɗinta tajawo tasoma shafawa, batare da tace da shi, komai ba.
“Na lura tunda nace miki, yau zamu fita, kike ta ɓare ɓare, kodai ma nace na fasa ne” yafaɗi haka yana me jingina kansa da bango, alamar nazari.
Da sauri ta juyo ta kalleshi.
“Dan Allah, Hubby karkace ka fasa, kaga fa har na kammala abincin!” tafaɗi haka a shagwaɓe.
Murmushi yayi haɗe da cewa “Cigaba da abun da kikeyi, wasa nake miki”
Murmushin jin daɗi tayi, haɗe da ɗaukan powder, tasoma shafawa akan fuskarta.
Batayi wani kwalliya sosai ba, janbaki da kwalli kawai ta saka, saikuma mascara, wanda sakasa yazamemata sabo, dazaran ta goga akan eye lashes ɗinta, sai kaga kamar eye lashes ɗin kanti tasanya, sosai kuma tayi kyau.
Wata haɗaɗɗiyar abaya gown, wanda aka sanya mata, acikin kayan aure, taciro ta sanya, sosai rigan ta amshi jikinta, da ɗan madaidaicin vail ɗin rigar, ta yane kanta zuwa wuyanta.
Wani flat shoe, me igiyoyi ta zura a ƙafafunta, kana ta fice zuwa falo, domin dama tuni Dr.Sadeeq ya jima, a falon yana jiranta.
Yana ganinta, ya lumshe idanunsa, yayinda murmushi ya faɗaɗa akan fuskarsa, cike da zolaya yace.
“Baƙuwa mukayi ne? sannunki da zuwa, ɗan ƙaraso ki zauna anan” ya ƙare maganar yana meyi mata, nuni da gefensa.
Dariya ne yakama Zahrah, tsayawa tayi agabansa, haɗe da ɗanyi masa fari da idanu.
“Yadai malam ko ka ƙyasa ne?” taƙare maganar tana me kama ƙugunta da duka hannayenta.
“Sosaima kuwa, gaskiya kinyimini, minti biyu please!” yafaɗi haka, yana me kashe mata idanunsa ɗaya, haɗe da ɗage giransa sama.
Dariya suka saka, su duka biyun, haɗe da miƙa masa hanu suka tafa.
Riƙe da hanun juna, suka nufi dinning area, plate ta ɗauka ta zuba musu fried cous cous, dakuma sauce egg, wani plate ɗin takuma ɗauka, ta zuba musu pepper soup, take gurin ya gauraye da ƙamshi. Harshensa yasanya ya lashe laɓɓansa, haɗe da ɗan lumshe idanunsa.
“Babe abincin nan fa zaiyi daɗi, tunkafun naci, har naji taste ɗinsa acikin bakina”
Dariya kawai tayi, haɗe da turo masa plate ɗin abincin gabansa, zama tayi akan cinyarsa, da hanunta take eban abincin, tana kaiwa bakinsa, idan tasamai abincin abaki, sai ya tsotse mata yatsunta kaf, kafun yake sakewa, ita dakanta taciyar dashi, kana itama taci, suna kammalawa ta tattara komai dake, wajen takai kitchine, fitowa tayi daga cikin kitchine ɗin, hanunta ɗauke da baskets guda biyu, aje baskets ɗin tayi akan dinning table, kallonta tamayar kansa.
“Yakamata muje ko, kaga dare fa yanata ƙarayi”
Wayarsa dake riƙe ahanunsa, yajefa acikin aljihun rigansa, haɗe da ɗaukan duka baskets, ɗin yanufi hanyar fita daga cikin falon, da sauri ta wuce cikin ɗaki, ta ɗauko hand bag ɗinta, kana ta rufa masa baya.
Saida suka hau titi, kafun ya dawo da kallonsa gareta.
“Ina zamu fara zuwane, gidan Hajiya ko kuma gidan Inna?” ya tambayeta.
“Mufara zuwa gidan Hajiya, inaga zaifi ko” tafaɗa tana kallonsa.
Kansa yajinjina, kana yaci gaba da tuƙa motar..
Yana danna horn, mai gadi ya wangale masa makeken gate ɗin gidan nasu, tura hancin motar tasa yayi zuwa cikin gidan.
Tana fitowa acikin motar, ta ɗauki ɗaya daga cikin baskets ɗin ta riƙe a hanunta, hanunsa yamiƙo alamar ta bashi basket ɗin ya ɗaukar mata.
Waro idanunta tayi, haɗe da cewa “Karufamin asiri, kabarni na ɗauki basket ɗinnan, salon nabaka, Hajiya taganka tace na mallake mata ɗa”
Dariya maganarta ta ta basa.
“Ko Hajiya batace ba, ai dama kin mallakeni” yafaɗi haka yana dariya, dariya kawai itama tayi, amma bata yarda, ta bashi basket ɗin ba.
Yana gaba tana biye dashi a baya, haka suka nufi ƙofar da zata sadasu da falon Hajiyarsa.
Da sallama ɗauke a bakinsu suka shiga cikin falon, huwaila me aikin Hajiya dake zaune aƙasa tana kallo, itace ta amsa musu sallaman nasu, cike da ladabi tashiga gaidasu, Dr.Sadeeq ya amsa haɗe, da tambayarta ina Hajiyarsa, “Tana sama” Huwaila tabasa amsa. “Je kice mata munzo” yafaɗi haka yana me zama akusa da Zahrah, da sauri Huwaila ta haura sama don cika umarninsa.
Kallonsa tayi haɗe da ƙoƙarin matsawa daga kusa dashi, hanu yasa ya danne mata cinya, “Ina kuma zaki?”
“Afalon Hajiya fa muke, idan tafito taganmu a haka, gaskiya zanji kunya” tafaɗi haka tana me ƙoƙarin zame hanunsa dake kan cinyarta.
Ɗaura kansa yayi akan kafaɗanta, haɗe da sanya hanunsa ya rungumeta, mamaki gaba ɗaya ya gama kashe Zahrah, da sauri tasoma ƙoƙarin ƙwace jikinta, amma takasa. “Me Doctor yakeyi haka ne?” ta tambayi kanta.
“Please ka sakeni agidan Hajiya fa muke!” tafaɗi maganar aɗan tsorace.
Sake rungumeta yayi, haɗe da kashe mata idanunsa ɗaya, ta buɗe baki zatayi magana kenan, Hajiya dake tsaye tana kallonsu, taɗanyi gyaran murya.
Da sauri Zahrah ta zame daga kan kujera ta zube a ƙasan sofa, tare da sanya gefen mayafinta, ta rufe fuskarta, wani irin matsanancin kunyane ya kamata, shikenan Doctor yaja mata.
Fuska ɗauke da murmushi Hajiya ta ƙaraso cikin falon, haɗe da zama akan kujera, cikin yanayi naɗanjin kunya Dr.Sadeeq ya gaidata.
Fuska a sake ta amsa masa, tana me binsa da kallon ƙauna, irin wanda ke tsakanin uwa da ɗanta, sosai taji daɗin ganinsa a haka da tayi, kallo ɗaya zakayi masa kafuskanci cewa, yana cikin farinciki, da kuma jin daɗi, hakan kuwa bakaɗan yafaranta ranta ba.