SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAYD
Gaba ɗaya ya sauya, yazama wani silent dashi, bayason hayaniya ko kaɗan, kwanansa biyu kenan, yau baya gida, yana can guest house ɗinsa, yana jinyar kai da zuciyarsa, sosai yake karatun Al’Qur’ani, babu dare ba rana, hakan kuwa sosai ya haifar masa da salama, acikin zuciyarsa, saidai kuma duk wani bugun numfashi dana zuciyarsa, tare suke tafiya da soyayyarta, ƙarya yake, shi yasani, ƙaryane, soyayyar Zahrah, tafita acikin zuciyarsa, lokaci guda, baisan wani irin kalan, zazzafar soyayya bace yakeyi mata.
Zaune yake akan kujera, ya lumshe kyawawan idanunsa, sallaman Abid ne ya karaɗe cikin falon, ahakali ya ware idanunsa, akan Abid.
Murmushi Abid, ya sakar masa, haɗe da ƙarasowa, wajen da Zaid ɗin ke zaune.
“Namijin duniya!” Abid yafaɗa yana me dafa kafaɗan Zaid.
(Namijin Duniya, na Aunty Mami, wacce bata karantaba, tayi missing)
Murmushin ƙarfin hali, Zaid yayi, haɗe dasa haƙori ya cije laɓɓansa, girgiza kansa kawai yayi, yana me tunano rayuwarsa ta baya.
“Yaushe kafara shan magani, batare da an tursasaka ba?” Abid yatambaya, yana me duba magungunan, dake zube akan wani table, dake aje gaban Zaid.
Murmushi Zaid yayi haɗe da duban Abid, cikin murya me sanyi yace.
“Please Abid, kasan banason yawan damuwa, ɗazufa kabar gidannan, yanzu kuma me yadawo da kai?”
Murmushi Abid yayi, haɗe da cewa
“Nazo ne, na maidaka gida, yajin ya isa haka, ka bar ƴar mutane, ita kaɗai, hakan kuma baidace ba”
“Zamana anan yafi min daɗi Abid, gaskiya banajin zan koma gidan nan” Zaid yafaɗi haka, da iyaka gaskiyarsa.
“Kada kace haka Zaid, bansan yakakeji acikin zuciyarka ba, amma tabbas nasan abun da kakeji bayayi maka daɗi, amma kuma, komawarka kusa da matarka, inaga zaifiyemaka wannan zaman kaɗaicin, da kakeyi”
“Banajin zan iya zama da wata Abid, Zahrah ce muradina, amma narasata” hanunsa yaɗauka, yakamo na Abid, ya ɗaura a dai-dai, saitin zuciyarsa, Cike da rauni yace.
“ji yanda zuciyata, take bugawa Abid, soyayyarta ne acikin ta, marar misaltuwa, inaso namanta da ita, amma nakasa, nakasa daina tunaninta, wallahi inasonta Abid, kataimakeni, inaso nadaina tunata, bazan iya jurewa ba, nasan kuma bazan taɓa samun madadinta ba!” tuni har ƙwalla suncika idanunsa.
Tsananin tausayin, abokinnasa ne yakamasa, haƙiƙa Zaid yana a zabtuwa, to amma haka tasa kalan ƙaddaran take, babu wani wanda ya isa sanja masa.
“Kayi haƙuri Zaid, kasaurari abun dazan faɗa maka, haƙiƙa soyayya na azabtar dakai, amma kaci gaba da daure zuciyarka, sannu a hankali, zaka manta ta, watarana, komai zai zama labari, inaso kayi ƙoƙarin mantawa da komai, ka je ga matarka, saboda itama tanada haƙƙi akanka, koba komai kai ɗin mijin tane, kuma Allah Zai kamaka da rashin, sauƙe mata haƙƙinta, tashi kaje kayi wanka kazo, nayi dropping ɗinka agida!” Abid yafaɗi haka cikin lallashi.
Babu musu Zaid yamiƙe, ya wuce cikin bedroom ɗinsa, dakansa ya haɗa ruwa yayi wanka, yana fitowa ya sanya, wasu riga da wando, masu kalan jinin kare, wato maroon colour, kayan suna da kyau, kasancewarsu, masu tsada, sosai kyawun sa yafito, acikin kayan, hmm ZAID, ZAID ne har yau, shiɗin na musammanne, irinsa basuda yawa, kuma wahalar samu garesu, shiɗin nadabanne, kyau dakuma ɗaukar hankali, yana a tattare dashi, Ajininsa hakan yake, wato burgewa, ga duk wanda yaganshi, duk da cewa yayi rama, amma kuma murɗaɗɗiyar surar jikinsa tananan, da turarensa me daɗin ƙamshi, ya feshe jikinsa, yana fitowa cikin falon, Abid yasaki murmushi, cikin sigar tsokana yace.
“Sabon ango kenan, sai ƙyallin amarci kake, gashi kuma kasha kyau”
Ƴar ƙaraman tsuka Zaid yayi, haɗe da wurgawa Abid harara.
“Nifa banason Iskanci, wallahi idan kasake ka kunnani, babu inda zani!” yaƙare maganar aɗan ƙufule.
“Sorry abokina, muje ko” Abid yafaɗi haka yana me tashi tsaye.
A motar Abid suka tafi, Abid ne ke jan motar, sai jan Zaid da hira yake, shi dai Zaid shiru yayi masa, haɗe da lumshe idanunsa, taya zai fassara abun dayakeji akanta?
Suna isa ƙofar katafaren gidan, Abid ya tsai da motarsa, haɗe da juyowa ga Zaid, hanunsa ya ɗaura akan na Zaid, cike da kulawa yace.
“Kamar yanda na faɗama tun a farko, tabbas saika daure, nasan kanajin ciwo, amma dan Allah karka cigaba da sanya, kanka acikin damuwa, basai na faɗa maka ba, nasan kasan cewa, akwai haƙƙi, da kuma alhakin Zahrah, dake bibiyarka, haka kuma idan har ka cutar da Afra, Allah Bazai barkaba, haka kuma haƙƙinta ma dake kanka, bazai barka, kayi rayuwa, me daɗi ba, please Zaid kayi controll ɗin kanka kaji!” cike da lallashi Abid ya faɗi maganar.
Ajiyar zuciya, Zaid ya sauƙe, haɗe da jinjina kansa, alamar yaji, buɗe murfin motar yayi ya fice, saida Abid yaga shigan Zaid gida, kafun ya tada motarsa yabar ƙofar gidan.
Tana zaune a falo, sanye take da riga da sket na kanti, gaba ɗaya tayi wani irin rama, duk da cewa dama tun asalinta, ba ƙiba gareta ba, haƙiƙa tana cikin damuwa, kwananta biyu kenan, bataji koda motsinsa bane, duk da cewa tana mejin tsoronsa, amma kuma tana buƙatar ganinsa, da sallama ɗauke a bakinsa, ya shigo cikin falon, Afrah najin sallamarsa, tayi saurin ɗago da kanta ta kalleshi, kallo ɗaya yayi mata ya kau da kansa.
Ƙarasowa cikin falon yayi, haɗe da zama akan kujera, cike da girmamawa, Afrah ta gaidasa, haɗe dayi masa sannu da zuwa.
Babu yabo ba fallasa, ya amsa mata, shiru ne yashiga tsakaninsu na ƴan sakanni.
Ƙirjinta na bugawa tace “Me za’a kawo maka?”
Kallonta yayi naɗan sakanni, da ƙyar ya iya buɗe bakinsa yace
“Kawomin Ruwa”
Jikin Afrah na tsuma, ta miƙe don kawo masa ruwa, kamar yanda ya buƙata.
Ruwan Faro takawo masa haɗe da ɗan ƙaramin glass cup, har ƙasa ta durƙusa ta aje masa ruwan, a gabansa.
Ɗaukan goran ruwan yayi yakai bakinsa, saida yasha fiye da rabin ruwan, kafun ya aje goran yana shirin miƙewa tsaye ne, yaji Afrah tasanya hanu ta kama ƙafansa, fuskarsa ɗauke da mamaki, ya juyo da kallonsa gareta, gani yayi fuskarta, tayi chaɓa chaɓa da hawaye.
“Dan Allah Kayi haƙuri, kada kajuyamin baya, inason nayi zaman aurena cikin salama, idan baka yafeminba, bazan taɓa jin daɗi ba, wallahi ƙaddarata ce tazo a haka!” kukane yaci ƙarfinta.
Wani irin tausayinta ne yakamashi, “Gwara taki ƙaddaran, tazo miki da sauƙi, akan tawa ƙaddaran” yafaɗi haka acikin zuciyarsa.
Hanunsa yasanya, ya kamo kafaɗunta, ya ta data tsaye.
“Ya isa haka, kidaina kukan nan banaso yana samin headache, kinci abinci ne?”
Kanta ta girgiza alamar “A’a”
“Okay, kinada abun da zakici ne ko kuwa?”
“Eh inadashi, na dafa abinci ɗazu”
“kici abinci!” yafaɗa ataƙaice, yana me nufar hanyar ɗakin sa.
Daɗine yakusa kashe Afra, sam bata tsammaci kulawa, har haka daga gareshi ba.
Zaid kuwa yana shiga cikin ɗaki, ya cire rigar dake jikinsa, ya wurga cikin wani dustbin, ɗin aje kayan wanki, yana shirin cire belt ɗin wandonsa ne, yaji anayi masa knockig ƙofarsa, wani irin haushine ya kamasa, a hasale ya nufi wajen ƙofar don ganin waye.