SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana buɗe ƙofar sukayi ido huɗu da Afrah, sai da taji gabanta ya faɗi, musamman da ta ganshi a tuɓe, amma kuma dolenta zata kau da tsoronta.
“Meye?” yatambaya yana me ƙare mata kallo.
“Ammm… dama abincine nakawo maka” tafaɗa tana me kallon plate ɗin dake riƙe a hanunta.
“Banaci!” yafaɗa ataƙaice yana me yunƙurin rufe ƙofar ɗakin nasa.
Dasauri ta kutsa kanta cikin ɗakin, cike da mamaki yake kallonta.
“Dan Allah kaci, kada kacemin a’a, Dan Allah!” tafaɗi haka tana me langwaɓar da kanta gefe, take idanunta sukayi rau rau dasu, da’alama kuka take son yi.
Ajiye abincin anan, yafaɗa yana me nuna mata kan sofa, cikin jin daɗi ta aje abincin, harta juya zata fita kuma, saita tsaya, haɗe da dawo da kallonta garesa. “Kayi haƙuri, ko badanni ba, kaci abincin” juyawa tayi tacigaba da tafiya, hartakai bakin ƙofar fita Zaid yace
“Afra”
Juyowa tayi garesa, ƙwalla yagani kwance acikin idanunta, da hanunsa yayi mata nuni alamar tazo, kanta aƙasa hartaƙaraso gareshi, domin gaba ɗaya, yacika mata idanu, sosai murɗaɗɗiyar surar jikinsa, ta ƙayatar da ita.
Bata tsammata ba saiji tayi, yasanya hanunsa, ya jawota jikinsa, rungumeta yayi, haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗanta, ya lumshe idanunsa, jikinta ne gaba ɗaya yayi sanyi, hanunta duka biyu tasanya itama ta rungumesa, ƙam, haɗi da lumshe idanunta, wani irin shauƙi ke ratsata, ƙamshin sa mai matuƙar daɗi, shi yayi sanadiyar dulmiyata cikin wata duniya….
Yana rungume da ita amma kuma zancen zuci yake.
“Tabbas, abun da Abid yafaɗa masa, gaskiyane, Afra itace matar da Allah Ya zaɓa masa kuma daidai dashi, wannan zaɓin Allah Ne, bazaɓinsa ba, kuma zaɓin Allah Yafi zaɓinsa, saboda haka, dole zai karɓi Afra amatsayin matarsa, kuma zai yi ƙoƙari wajen ganin, ya yi mata adalci, bayajin sonta aransa, amma zaiyi iyaka, bakin ƙoƙarinsa wajen ganin, yazauna da ita lafiya , idan ya rabu da ita, baisan wace buɗaɗɗiyar zai kuma samu ba, shidai yasan irin Zahrah ita kaɗaice, kuma yariga daya rasata, saboda haka dole zaiyi haƙuri da Afrah, kodan son kyautata masa daya lura tanayi”
Zaune take akan kujera, ta ɗaura ƙafafunta, bisa kan wani table na glass, dake cikin falin, wata ƴar ficikan riga maroon colour ne, sanye ajikinta, saman wuyan rigan net ne, yayinda hanun rigan kuwa, ya kasance na vest, wato siririn hanu, tayi kyau sosai acikin shigar nata, hanunta riƙe yake da kofi, wanda ƙe ɗauke da Banana Smothie aciki, sai kaɗa kanta take da alama, taji daɗin Banana Smothie’n da take sha, duk da cewa, har yanzu bata wani jin daɗin jikinta, amma haka ta daure, take abu kamar me lafiya, miƙewa tayi daga zaunen da take, haɗe da ƙarasawa gaban tangamemen tv plasma’n dake aje cikin falon, remote ta ɗauka, ta ƙara volume ɗin tv, ta aje remote ɗin kenan, wutan nepa ta ɗauke, gashi magriba ta somayi, ɗakin babu wadataccen haske, babu zato ba kuma tsammani, taji an sanya hanu an rufe mata idanunta, wani irin ƙara tasake alokaci guda, sai kuma ta yanki jiki tafaɗi ƙasa, da hanzari Dr.Sadeeq wanda shi yayi mata haka, yasanya hanu ya tarota tafaɗa cikin jikinsa, wayarsa ya laluɓo ya kunna torchlight, daidai lokacin ne kuma wutan nepan ya kuma, dawowa haske ya baibaye ɗakin, amatuƙar razane yashiga girgizata, yana ƙiran sunanta, amma ina ko motsi batayi ba, hanunsa yakai kan hancinta, yaji babu alamar shiga da fitar numfashi, tsorone yakamasa, haɗe da ruɗewa, akiɗime yashiga jijjigata, amma bata motsaba, saboda babu numfashi ajikin ta…..
13/February/2020
✅ote me on Wattpad
@fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Lovely Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
CHAPTER 110
A matuƙar ruɗe yake girgizata, yana me ƙiran sunanta, sosai ya tsorita da al’amarinta, gaba ɗaya ya ruɗe, yama manta da cewa shi ɗin likita ne, sungumarta yayi acikin ƙirjinsa, direct sai cikin mota, a gidan baya yasakata, yafigi motar da wani irin gudu, saboda tsabar gudun da yakeyi, mintuna kaɗan, suka kawoshi, cikin asibitinsu, a ruɗe yaje wajan, abokin aikinsa Dr.Salim, yasanar masa abun dake faruwa, emergency aka wuce da ita direct, shikam Dr.Sadeeq kasa shiga cikin emergency room ɗin yayi, suke karɓan emergency patient idan aka kawo, amma kuma sai yau, gashi shine da kansa ya kawo, sai kaikawo yake tayi, aƙofar shiga emergency room ɗin, kwata kwata hankalinsa baya jikinsa..
Bayan Mintuna 30
Yana tsaye ajikin bango, idanunsa a lumshe suke, zuciyarsa kuwa, bugawa takeyi da ƙarfi, tamkar zata faso cikin ƙirjinsa, ta fito.
Dr.Salim da sauran doctors, ɗinne suka fito daga cikin ɗakin, har yanajin tuntuɓe, agarin saurin ƙarasawa inda suke.
“Salim ya ya take? tafarfaɗo ne? Meke damunta dan Allah? Allah Yasa tana lafiya?” Duka waƴannan tambayoyin, Dr.Sadeeq ya jerawa Dr.Salim su.
Murmushi Salim yayi, haɗe da sanya hanunsa, ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq.
“Haba Man, saikace ba doctor ba, duk kabi ka ruɗe, bawata babbar matsala bace bafa, kaida kanka ma zaka iya maganceta, amma duk karuɗa kanka”
Ajiyar zuciya me ƙarfi, Dr.Sadeeq ya sauƙe, sakamakon jin daɗin kalaman da Dr.Salim yayi.
“Masha Allah! kada kaga laifina, wallahi Salim, inasonta sosai ne, banason wani abu, ya sameta shiyasa” Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me lumshe idanunsa.
Murmushi Salim yayi, haɗe da cewa. “Muje office”
Babu musu Dr.Sadeeq yabi bayan Salim, suka wuce office ɗin Salim ɗin.
Suna shiga suka zauna, su dukansu akan kujera ɗaya, murmushi Salim yayi haɗe da maida kallonsa ga Dr.Sadeeq, hanu yasa ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq ɗin, cikin son kwantar masa da hankali yace.
“Kada ka damu Sadeeq, ba wani abu bane, tsananin tsorone kawai, ya sata suma, amma bayan haka babu wani ciwo dake damunta, sai dai naga tana da hawan jini, amma kuma gaskiya abokina, ka iya aiki, wai ma watanku nawa da aure ne yanzu?”
Harara Dr.Sadeeq, ya jefawa Salim. “Wannan wani irin iskanci ne Salim? me ya haɗa ciwonta da tambayan watannin auren mu? yanzu ba lokacin wasa bane, ina tsananin son matata, bana ƙaunar naga wani abu yasameta, idan akwai wani abu bayan wannan, ka sanar dani, idan kuma kaƙi zan bincika da kaina, daɗin abun nima likita ne” Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me ƙoƙarin miƙewa tsaye, sarai yasan iskancin Salim, iya shegensa yayi yawa, gwamma ma yaɗauki Zahrah’nsa, kawai su koma gida, inyaso shida kansa, zaiyi checking ɗinta agida, dama ruɗewan da yayine, yasanya ya kawota asibiti.
Hanunsa Salim ya riƙe haɗe da cewa.
“Meyayi zafi kuma? daga tambayar watannin aure, yanzu duk ba wannan ba, miye tukuicina wanda zaka ban, idan nafaɗama wata magana me daɗi?”