NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Tukuici kuma? wace magana me daɗi kenan? nida matata bata da lafiya, har akwai wata magana da za’a faɗamin wacce zatayimini daɗi? nace maka kadaina min wasa ko Salim, yanzu ba lokacin wasa bane.” Injicewar Dr.Sadeeq.

“Koma dai menene can maka, kuma tukuicina ne sai ka bani, ina tayaka murna, saboda madam ɗinka, tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki, na wata biyu!” Salim yaƙare maganar yana faɗaɗa fari’ar, dake kan fuskarsa.

Zama daɓas Dr.Sadeeq, yayi akan kujera, haɗe da sanya hanunsa, ya kama duka kafaɗun Salim, cike da tsananin farinciki yace “Dagaske kake Salim? Zahrah na ɗauke da ciki na ajikinta? Kafaɗamin gaskiya, dan Allah karka yaudareni!”

Dariya Salim yayi haɗe da cewa “Wallahi ba wasa nake maka ba Sadeeq,  da gaske matarka, kuma Zahrah’n ka, tana ɗauke da ciki, sannan kuma yana da kyau, ka kiyaye ɓacin ranta, dakuma duk wani abu, da kasan zai sanya ta tsorita, saboda yawan tsorita zai iya haifar da zubewan cikin..”

Kafun ma Salim yaƙarisa zancensa tuni, Dr.Sadeeq ya sulale ƙasa yayi sujjada, na tsananin nuna godiyarsa ga ALLAH, Haƙiƙa ya matuƙar jin daɗin, wannan albishir ɗin da Salim yayi masa, rungume Salim yayi cike da farinciki.

“Thank you so much Salim, haƙiƙa yau kasani farinciki sosai, kuma kaima insha Allah, zan saka farinciki, ta hanyar baka tukuici, wanda zakaji matuƙar daɗinsa”  yanakaiwa nan a zancensa ya sake Salim, haɗe da ficewa daga cikin office ɗin, direct ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa.

Shigowarsa, yayi daidai, da buɗe idanunta,   wani irin ƙawataccen murmushine, kwance akan fuskarsa,   ƙarasowa yayi, kan gadon ya ɗagota, haɗe da rungumeta, tsam acikin ƙirjinsa, wani irin daɗi yakeji na musamman,   kwanciya tayi luf acikin jikinsa, cikin muryan shagwaɓa tace.

“Hubby me mukeyi a asibiti?”

Sake matseta yayi, acikin jikinsa, haɗe da sanya hanunsa, yashiga shafa bayanta,  cikin wata irin murya yace. 
“Bansan dame zan iya biyanki  ba Zahrah, haƙiƙa ke ta musammance, kinkawo min farinciki, na musamman, kinsani acikin wata duniya,  me ɗauke da wasu surruka, wanda suke da wuyar mantawa, Inasonki My Wife! ina tsananin ƙaunarki, nagode miki sosai, Allah yayi miki albarka!”    “Inaasoonki!!” yakuma faɗa, in a slow sound, yana me sumbatar goshinta.

Mamakinsa ne yacika Zahrah, ita sam bata gane me yake nufi ba,  kyawawan fararen idanunta, ta zuba masa da’alamu tanason jin ƙarin bayani daga garesa.

Hanunsa yasa ya shafi gefen kumatunta, idanunsa ɗaya, ya kashe mata, haɗe da cewa.
“Verry soon, ni da ke, zamu zama parents!”

“Parents?” ta maimaita sunan abakinta, da ɗan mamaki.

“Yes, ni dake munkusa zama iyaye, saboda kina ɗauke da, ciki!” yafaɗi haka yana murmushi.

Waro manya manyan idanunta tayi, haɗe da sanya hanu ta shafi kan ɗakalallen cikinta.

“Ciki! inada ciki fa naji kace?”

“Eh kina ɗauke da cikina, yanzu haka ajikinki,  saura lokaci ƙanƙani kizama mummy’s boy”

Wani irin madaran farinciki ne, taji yana ratsa duk wani ƙofar sadarwa dake jikinta, ko kusa koda wasa bata taɓa, kawo hakan acikin tunaninta ba,   rungumeshi ta sakeyi ƙam ƙam, haɗe da sakin wani irin murmushi, gaba ɗaya sai tanemi ciwon jikin nata ma ta rasa, “Ashe itama zata zama Mama? lallai  ALLAH  Abun godiya ne” tafaɗi haka acikin zuciyarta.

“Babyna mu koma gida ko?” yatambayeta, cike da tarairaya.
Dama ita uwar shagwaɓa ce, aikuwa tuni ta narke masa, haɗe da kaɗa masa kai, alamar
“Eh”

Karɓo musu takardan sallama yayi, haɗe da dawowa cikin ɗakin,  ɗagata yayi caɗak, yasanyata acikin ƙirjinsa, haka yanufi ƙofar fita, daga cikin ɗakin, shagwaɓa tasakamai, akan cewa ya sauƙeta ƙasa, zata iya takawa da ƙafafunta, amma fir yaƙi, waishi bayasone ko kyakkyawan motsi tayi, bayaso tasha wahala, haka suka fito cikin asibitin, kowa sai kallonsu yake, abokan aikinsa kuwa, dariya kawai sukeyi masa, sam basuyi mamaki ba, domin kuwa duk wanda yasan Dr.Sadeeq, to yasan,cewa, yana matuƙar ƙaunar Zahrah’n shi, domin ko da yaushe sunanta, nanan raɗau acikin bakinsa.

A hankali yake tuƙa motar, tana manne ajikinsa,  ji yake kamar ya maidata cikin jikinsa, wani irin sabon ƙaunarta, yakeji na huda fatarsa, yana shiga cikin jikinsa.  

“Me zakici na saya miki my lovely na?” ya tambayeta, cike da kulawa.

Harshe tasanya, ta tanɗe bakinta, haɗe da cewa  “Ni gurasa kawai nakeson ci, sai kuma shaka, amma gurasan, nafison wanda, aka yanka masa tomatoes, sosai asamansa”  taƙare maganar tana haɗiye yawu.

Dariya sosai tabashi, yanayin yanda tayi maganar kaɗai, ya isa tabbatar maka cewa, cike take da kwaɗayin gurasan.
“Okay kome kikeso ni me samamikine, matuƙar a kwaishi acikin duniyar nan, ni dakaina kikeso nayi miki gurasan ko kuma, nemo miki zanyi a waje?”

Dariya tayi haɗe da dubansa cikin shagwaɓa tace “Kai ka iya gurasa ne?”

“Ko ban iyaba akanki ai zan koya” yafaɗi haka yana murmushi.

“Nidai banaka nakesoba, kawai ka nemomin, kuma ma ni nafison wanda akayi a gida, bawai wanda ake sayarwa a waje ba!” taƙare maganar tana me turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.

“Wannan me sauƙi ne, yanzu kuwa zan kaiki,  gidan da za’a miki gurasa” yafaɗi haka yana me karya akalan motar tasa, zuwa wani hanu daban.

(Wallahi nima kwaɗayin gurasan nake???? batun yauba, ko ta wayane, kuturomin please.????)

Mamakine yakamata, ganin sun tsaya agaban gidan Hajiya, kallonsa tayi haɗe da zaro idanunta
“Gidan Hajiya fa,  ka kawo mu” tafaɗa tana wuƙi wuƙi da idanu.

“Eh mana, kinsan Hajiya, ƙwararriya ce, wajen iya sarrafa abinci, kuma ina databbacin cewa ta iya gurasa, taso mushiga” yafaɗi haka yana me miƙa mata hanunsa, alaman takama.

“A’a gaskiya nidai mukoma gida, yanzu idan ta tambayi, DALILINA nason cin gurasa, muce mata me?”

Murmushi yayi haɗe da cewa “Baza ma tatambaya ba, ai itama tasan watarana, mutum yakan jin son cin irin waƴannan abubuwan”  Da haka Zahrah ta yarda suka shiga, cikin gidan.

Suna Sallama a falon, Hajiya dake zaune, tana duba wasu lace’s, dake zube a gabanta, ta amsa musu, cike da fari’a, da kuma mamakin ganinsu da tayi, domin kuwa sam bata tsammaci ganinsu, nan kusa ba, saboda basu jima da zuwa ba.

Kan Zahrah a ƙasa, ta ƙaraso cikin falon, cike da ladabi ta durƙusa, akan guiwowinta, ta gaida Hajiya.

Cike da fari’a, Hajiya ta amsa mata, haɗe da kamo hanunta, ta zaunar da ita, akusa da ita.

“Batun yauba na faɗa miki, nima uwace, ki saki jikinki dani, zanfi jin daɗin haka!” Hajiya tafaɗi haka cikin son nunawa Zahrah ƙauna.

“Nidai yanzu agidannan, ba a wani damu dani ba, idan nazo ma ba a wani bani kulawa”  abun da Dr.Sadeeq yafaɗa kenan, yanayin yanda yayi maganar kamar wani ƙaramin yaro.

Dariya sosai yabawa Zahrah, ta lura shidai shagwaɓaɓɓene na ƙarshe.

“Ai ni bana yayin tsoho, idan har nasamu sabo, dama ba ɗiya mace ƙarama nake da shiba, to Allah yabani sainace banaso? kariga daka zama goɗo goɗo dakai, me zanyi dakai, ko kinga ya dace na bashi kulawa ne Zahrah?” Hajiya ta tambayi Zahrah.

Kunyarsu ne su duka yakamata, amma kuma yazatayi, Hajiya nason janta ajiki, dole itama ta sake da ita.

“A’a Hajiya, idan kika basa kulawa, zai ƙara shagwaɓewa da yawa!” Zahrah tafaɗi haka, tana me satan kallonsa, ta gefen idanunta, tasakar masa gwalo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button