SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ƙoƙarin juya wainar fulawan yake, amma yaƙi juyuwa, gaba ɗaya ya ƙona hannayensa, har wainarma tasoma ƙonewa, da ƙyar ya samu ya kwashe, kuma dama wanda ke cikin kaskon shine na ƙarshe, kashe gas ɗin yayi haɗe da ɗaukan tissue ya goge gumin dake tsastsafowa a goshinsa, plate ɗin wainar da kuma roban yaji yaɗauka ya nufi falo.
Tana zaune akan sofa, tayi piecess da ƙafafunta, sanye take da wata ƴar riga marar nauyi, itanan zaman jiransa take, yakawo mata wainar fulawanta taci. Yana shigowa cikin falon tasaki dariya, domin kuwa har kumatunsa manja ne.
Ganin haka yasanya sa ɓata fuska, haɗe da tsayawa yana jifanta da hararan wasa.
“Kaganka kuwa, chab aikuwa kayi dumu dumu da manja!” tafaɗi haka tana ƙoƙarin gimtse dariyarta.
Shagwaɓe fuska yayi kamar wani ƙaramin yaro, plate ɗin wainar yakawomata gabanta ya aje mata, haɗe da aje mata roban yaji, muƙut haka ta haɗiyi wani yawu tsabar kwaɗayi, tuni ya wunta ya tsinke, jawo plate ɗin gabanta tayi, haɗe da gutsuran wainar fulawan takai bakinta. Da sauri ta tofar da wainar fulawan sai kuma tashiga kelaya amai, babu ƙaƙƙautawa, amatuƙar ruɗe yayo kanta, shiya riƙeta harta gama yin aman, dakansa ya gyara wajen, zama yayi haɗe da jawota jikinsa cike da tausayinta, yashiga yi mata sannu.
Kwanciya tayi luf acikin ƙirjinsa tana me sauƙe ajiyar zuciya, sosai tagalabaita, amai ba wasa ba.
Bayanta yake shafawa a hankali, yana ɗan jijjigata, kamar wata jaririya.
“Abincinne ba daɗi, yasa kikayi amai?” yatambayeta.
Ya mutsa fuska tayi haɗe da ɗaga masa kai ashagwaɓe tace “Ƙauri haɗe da warin hayaƙi wainar fulawan keyi”
Narke fuska yayi haɗe da karya wuyansa gefe, “yanzu duk ƙoƙarin nan da yayi, yatashi a banza?” yatambayi kansa.
Ajiyar zuciya yayi haɗe da cewa “Kiyi haƙuri, bansan ya akayi yayi warin hayaƙi ba, yanzu to mezakici?” cike dakulawa ya kuma tambayanta.
Zahrah ƴar rigima da shagwaɓa, sake narke masa tayi, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba, haɗe da cewa “Ni yanzu, Banana PineApple Smoothie kawai zan sha”
“Banana pineapple smoothie ba abincine wanda zai riƙeki ba, kifaɗamin yanzu me kike so bayan smoothie ɗin?”
“Gasashshen nama, wanda aka sa masa, sweet pepper dakuma onion” ta faɗi haka tana tanɗe baki.
Hanu yasanya yashafi gefen kumatunta, inda dogon suman kanta ya kwanta, “Wannan ba abun damuwa bane, kinaso muje mu sayone kokuma naje ni kaɗai?”
Tsulum tatashi zaune haɗe da cewa “muje tare”
Ɗaki suka koma shida kansa ya shiryata cikin, wani doguwar riga na lace, yanaɗe mata jikinta da wani vail marar nauyi, shima kayan jikinsa ya sauya, suka fita hanunsu sarƙe acikin na juna.
Wani haɗaɗɗen hotel suka nufa, hotel ɗin namusammanne, domin kuwa sai waƴanda suka amsa sunansu ne suke zuwa cin abinci wajen.
Yana riƙe da hanunta suka kutsa cikin hotel ɗin, awani ɓangare wanda babu yawan jama’a sosai suka zauna, suna zama wata waiter da jikinta ke sanye da uniform taƙaraso wajensu, cike da girmamawa ta basu menu, dan zaɓan abun da suke so, Zahrah ce takarɓi menu’n tazaɓi abun da takeso akawo mata, Dr.Sadeeq kam bai buƙaci komaiba, saboda a ƙoshe yake.
Mintuna kaɗan aka kawowa Zahrah abun da takeso, gyara zamanta tayi, haɗe da ɗaukan gasashshen namanta tasoma ci, harwani lumshe idanunta takeyi tsabar daɗi, ji take kamar bata taɓa cin wani nama me daɗin wannan ba, sosai taci naman, kana ta ɗaura banana pineapple smothie akai, shidai kallonta kawai yake, kome tayi burgesa take, kallonshi tayi da fararen idanunta, haɗe da ɗaukan tsokan nama guda ɗaya, takai bakinsa, babu musu yabuɗe bakinsa tasamai, ɗage masa giranta guda ɗaya tayi sama, haɗe da cewa “Yakaji naman, daɗi ko? hmm ai daga yau kullum anan zanna cin nama!” taƙare maganar tana jijjiga kanta, shidai murmushi kawai yaketa aika mata.
Harta gota, zata wuce, sai kuma tayi saurin dawowa da baya, sake ware idanunta tayi akan yarinyar, tabbas itace bazata manta fuskarta ba, kallon yarinyar tashigayi sosai, itakuma yarinyar sai dariya take tana kaɗa kanta, da’alama tana cikin farinciki. “Zahrah!” taƙira sunan yarinyar ahankali, yanda ita kaɗai da tayi maganar ne zataji me tace, “Itace wacce hotunanta suka cika jikin bangon ɗakin Zaid, kenan itace Zahrah’n Zaid? itace mafarki dakuma burinsa?” abun da Afrah ke faɗa kenan acikin zuciyarta, tsintar kanta tayi da tsayawa tana kallon ta, bawata babba bace bazata wuce 20 to 21 year ba, aƙalla tasan zata fita da 3 year, ita kanta yarinyar tayi mata kyau, domin kuwa tana da burgewa, kyawunta abayyane yake, “Hmmm idan dai har Zaid zaina mafarkin samun irin wannan tauraruwar, me zaiyi da irina?” Afrah ta tambayi kanta a bayyane.
“Mekikeyi a tsaye anan kuma?”
Muryar Zaid yakaraɗe cikin kunnuwanta, da sauri tajuyo tana kallonsa, sam ita tama manta da cewa tare suke.
Kallonta yayi naɗan sakanni, kafun ya raɓa ta gefenta ya wuce.
Ƙirjin Dr.Sadeeq ne ya buga, alokacin dayaga gilmawan Zaid ta bayan Zahrah, amma kuma da dukkan alamu shi Zaid ɗin bai lura dasu ba.
“Ya kamata mutafi ko princess, idan yaso saimu yi take away ɗin naman mutafi dashi gida, sai ki ƙarasa ci acan” Dr.Sadeeq yafaɗa a ƙagauce.
“Um um nidai Hubby kabarni please, nakusa nacinye fa” Zahrah tafaɗa a shagwaɓe.
Babu yanda ya iya, dole haka ya barta, taƙarasa cin namanta.
Tana kammalawa kuwa, yakama hanunta suka bar cikin hotel ɗin, ba gida suka nufa direct ba, saida suka biya wajen saida ice cream yasaimata, kana suka ɗauƙo hanyar gida.
Gaba ɗaya jin zuciyarsa yake a jagule, “Meyakawo Zaid wannan hotel ɗin? Kodai bibiyan matarsa yake?” tambayar da Dr.Sadeeq ke tayiwa kansa acikin zuciyarsa kenan, amma bayida wanda zai basa amsoshin tambayoyinsa. (???? Doctor fa yana tsoron Baba Zaid yasin)
Suna isowa bakin gate ɗin gidannasu, me gadi ya wangale gate ɗin Doctor yatura hancin motarsa ciki.
Tana ganin shigarsu cikin gidan, tasaki wani irin murmushi, tun fitowarsu a hotel ɗin take biye dasu, acikin motarta, batare da tabari sun gane hakan ba.
“Zanyi muku zuwa na musamman” tafaɗi haka a bayyane. Haɗe dayin reverse ta juya akalar motarta zuwa gida…
(Zanfara yi muku 1 read more, saboda banason editing, wallahi wuya yake ban????)
20/february/2020
✔️OTE me on Wattpad
@fatymasardauna
Love
Romance…….
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers }
WATTPAD
@fatymasardauna
Chapter 112
Yana zaune acikin falon, taturo ƙofa tashigo bakinta ɗauke da sallama, cike da mamaki yake kallonta. “Bakije gidan Ƙawartaki bane?” ya tambayeta yana me tsareta da kyawawan idanunsa.