NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi tayi haɗe da ƙarasowa cikin falon, zama tayi gaf dashi, haɗe da ɗaukan hanunsa ta ɗaura akan cinyarta.   “Naje nasamu batanan, kuma dama banaso nabarka kai kaɗai agida, shiyasa na dawo” tafaɗi haka tana me ƙara faɗaɗa murmushinta.

Kansa yajinjina haɗe da ɗaukan goran ruwan dake  aje a gabansa, yakai bakinsa,  kallonsa take tanaso tafaɗa masa abun dake cikin ranta, amma kuma tsoro takeji saboda batasan taya zai ɗauki maganar ba.

Matsewa kawai tayi haɗe da sanya hanunta ta saƙalo hanunsa,  fuskarsa takafe da ido kana tace “Yau nahaɗu da Zahrah”
Da sauri ya ɗago kansa ya kalleta, cike da tsananin mamaki yace “Wace Zahrah?”

“Zahrah wacce kasani, wacce kuma tunaninta ke maƙale acikin zuciyarka, babu dare babu rana” ta bashi amsa.

“A ina kikasanta, har kikasan cewa itace Zahrah’n danake tunani akowani lokaci?” yajefomata tambaya yana me kafeta da idanunsa.

“Duk wanda yasanka dole zaisan Zahrah, mussamman ma ace wanda yake kusanci dakai, ko kamanta cewa har yanzu akwai hotonta acikin ɗakinka?”

Miƙewa yayi daga zaunen dayake haɗe da cusa hannayensa cikin aljihun wandonsa.

“Zahrah ɗaya na sani a rayuwata, kuma tajima da mutuwa, saboda haka ni bansan wata Zahrah ba” yanakaiwa nan azancensa yasakai yawuce cikin bedroom ɗinsa, ko waiwayenta baiyi ba.

Mamakine ya bayyana ƙarara akan fuskar Afrah, sakamakon jin kalaman Zaid da tayi,  “Dare safe rana, bashida wani aiki sai tunaninta, tasha jinsa yana kuka a toilet, dukkuma akan Zahrah ɗinne, amma wai kuma yau da bakinsa yake cewa Zahrah ta mutu, anya kuwa Zaid yana lafiya?” Afrah ke magana da zuciyarta.
Murmushi tayi asakamakon tunawa da wani abu da tayi, tashi tayi tanufi ɗakin da Zaid yashiga.

Yana zaune agefen gadonsa hanunsa, riƙe da wani littafi da kuma biro,  da’alama nazartan littafin yake, amma kuma idanunsa cike suke da ƙwalla, yanajin motsin shigowar Afrah, yayi sauri ya rufe littafin, ransa a ɓace, ya juyo gareta.

“Mekikazo ɗauka? Bana faɗa miki cewa bakoda yaushe ne, nake da buƙatarki ba, please get out!” yaƙare maganar yana meyi mata nuni da ƙofar fita daga cikin ɗakin.

Ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da takowa zuwa garesa, tana zuwa gabansa ta durƙusa haɗe da zube guiwowinta a ƙasa.

“Kagafarceni idan abun dana faɗa maka akan Zahrah ya ɓata maka rai, banyi haka donna ɓata maka ba, saidai kuma zanfaɗa maka koda zaka tsaneni ne,  wallahi bazaka taɓa yin rayuwar farinciki ba, harsai kasamu Zahrah ka ƙara neman yafiyarta,  nasan cewa kana da buƙatar Zahrah akusa dakai, fiye da yanda kake da buƙatar ko wace mace a duniya,  amma kuma ƙaddara babu yanda bata juyawa bawa, dan Allah kayarda dani, akwai abunda zanyi wanda zaisa kusamu jituwa a tsakaninka da Zahrah, harma da mijinta”

Kallonta yayi da jajayen idanunsa haɗe da tashi, kawai yawuce cikin bathroom.
“Afrah bazata taɓa ganewa bane, shi kaɗai yasan irin zogi da kuma ciwon da zuciyarsa keyi masa, aduk sanda aka ambato masa sunan Zahrah,  a yanzu so yake yasa aransa cewa, babu wata Zahrah, domin wacce yasani tajima da mutuwa, wanda yake gani a yanzu, wata Zahrah’nce daban kuma ta wani ce”  tsaida zancen zucin nasa yayi,  haɗe da cire rigar dake  jikinsa, direct gaban shower ya nufa, tsayawa yayi haɗe da sanya hanunsa  ɗaya, ya dafa jikin bango, ruwane keta dukan kansa dakuma bayansa, sauda dama idan yana acikin ƙunci, tsayawa yake gaban shower ruwa yaita dukansa, dahaka yake ɗan samun relief.


Kwance take akan kujera, sanye take da wani dogon sket, wanda yake a tsuke daga sama har ƙasansa,   sket ɗin  irin roba ɗinnnan ne,  rigarta kuwa wata ƴar vest ce marar nauyi, fara ƙal da ita, tunda ta samu cikin nan, bata rabo dajin zafi, hakan yasanya bata cika zama da kaya masu nauyi ba,  wayartace rike a hanunta, kunnenta kuwa sanye suke duka da airpiece, waƙar film ɗin Sanam Teri Kasam takeji, harwani lumshe ido take, saboda tanason waƙoƙin film ɗin sosai,   sweet ne abakinta tana ɗan tsotsa, gudun tara yawu, dayake bata ƙure volume ɗin waƙarba, hakan yasanya tajiyo bugun ƙofar da akeyi mata,   da mamaki take kallon ƙofar falon, ita dai tasan batayi da kowa cewa yau zaizo wajenta ba, kuma yanzu ba lokacin dawowan Doctor bane, batajin zata iya tashi dan haka saita bawa me knocking door ɗin damar shigowa kai tsaye.

Da sallama ɗauke a bakinta, tashigo cikin falon.  Kallon kallo suka shigayiwa juna ita da Zahrah,  ita tana kallon Zahrah ne fuska ɗauke da murmushi, yayinda  Zahrah kuwa ke ƙare mata kallo, saboda batasanta ba ma ita kwata kwata.

“Da dai anbani izinin shigowa, aida sai na shigo” takatse Zahrah daga kallon da take mata, ta hanyar faɗan haka.

Murmushi Zahrah tayi haɗe da tashi zaune tace “Bismillah, shigo”

Ƙarasowa tayi tsakiyar falon, haɗe da zama akan kujera.

“Sannu da gida” tace tana murmushi.

“Yauwa sannunki da zuwa” Zahrah tafaɗi haka itama tana murmushi.    Miƙewa tayi da niyar takawo mata ruwa da lemo, da sauri tace. “A’a barshima basai kinkawomin komai ba, daga gida nake banajin ƙishi”
Kallonta kawai Zahrah tayi kana ta koma kan kujera ta zauna, cike da ƙosawa Zahrah tace.  “Baiwar Allah Bangane wace ke ba fa”

Murmushi takumayi akaro na barkatai.   “Sunana Afrah, dama nasan baki sanniba, amma ni nasanki, kiyi haƙuri bansaniba ko hakan danayi yaɓata miki rai, jiya naganki a hotel kinacin abinci keda wani, wanda nake kyautata zaton cewa mijinki ne, tunda naganki, naji kin kwantamin arai, kuma wallahi da zuciya ɗaya nake sonki, please idan bazan takuraki ba, inaso muzama ƙawayen juna”

Murmushi Zahrah tayi me sauti, haɗe da cewa “Nagode ƙwarai da ƙauna, amma kuma inaganin kamar akwai matsala, idan har muka fara ƙawance yanzu, dududu fa yau nafara ganinki, kinga dole kafun abota musan halin juna” inji cewar Zahrah.

“Da alamu bakida wata matsala nima kuma haka, kuma insha Allah bazakiyi danasanin ƙawancen mu ba”   taƙara da cewa “Akan hanya nake, watarana zanyi miki zuwa na musamman amma kafun nan,please samin number’n wayarki” miƙawa Zahrah wayarta da ta cirota cikin jaka tayi.
Babu musu Zahrah ta amshi wayar tasanya mata number’nta aciki, kana ta miƙa mata abarta.
Murmushi tayi haɗe da miƙewa tsaye, “nagode sosai” tace kana ta nufi hanyar fita daga cikin falon, Zahrah na ganin ficewarta ta sauƙe ajiyar zuciya, haɗe da komawa ta kwanta, aranta tana addu’an neman tsari daga sharrin mugayen mutane, da kuma aljanu….


Gaba ɗaya yau tatashi jikinta arikice, ganin haka yasa Dr.Sadeeq hana kansa zuwa office, yazauna tare da ita, yanata amsar shagwaɓanta, zuwa yanzu sosai shagwaɓanta yafi na da, tun da tasamu cikin wani sakalci da taɓara ya tsiro mata,  shikuwa doctor biye mata yake, hakan yasa gaba ɗaya yanzu tazama wata, shagwaɓaɓɓiya da ita sai kace ƴar shekara 4.
Kwance take akan sofa yayinda kanta ke ɗaure bisa cinyarsa, minti irin me tsinkenan ne abakinta, tana tsotsa a hankali, yayinda shikuwa ke shafa sumar kanta a hankali.


Mamakine ya matuƙar kashesa, ganin unguwa da kuma inda Afrah ta kawosa, ɗago idanunsa yayi ya watsamata su, “Inane nan?” yatambayeta still idanunsa na kanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button