SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi tayi masa haɗe da cewa “Unguwar su ƙawartawa da nake gaya maka ne, kuma ganan ma gidan nata” taƙare maganar tanayi masa nuni da gidan dake gefensu, bugawar zuciyarsa ne ya ƙara tsananta, take yaji kansa nayi masa wani irin sarawa.
“Kimaidani gida Afrah, tunkafun ranki ya ɓaci!” cikin yanayi na ɓacin rai yake maganar.
Dama tasan za ayi haka, hanunta ta ɗaura akan nasa cikin son ta rarrasheshi tace “Kayi haƙuri Dear, bazamu wuce 30 minute ba, nasan kasan gidan, kakuma san wacece acikin gidan, banyi haka donna ɓata maka ba, nayi hakane don kawai kasamu salama, ƙwarai nasan idan harta yafema kuma ayau idan kuka ga juna, tabbas komai zai wuce, duk da nasan sai ahankali, amma kuma dukanku zaku samu sassauci….”
“Kimaidani gida nace kona ɓaɓɓala ƙashinki gida biyu anan wajen!!” amatuƙar hasale yaƙare maganar.
Saida ta tsorita domin bata tsammaci wannan tsawan daga gareshi ba.
“Fita” yace da ita murya a dake.
Sumi sumi ta fice acikin motar, dan ta fuskanci sam babu alamar wasa a tattare dashi. Fita shima yayi daga cikin motar ya koma wajen zaman driver domin dama a wajen mai zaman banza yake dazama, itakuma tana wajen zaman driver.
Yana shiga yatada motar, kallon Afrah yayi fuska babu walwala, da sauri ta buɗe motar tashiga, da ƙarfi yaja motar sukabar ƙofar gidan.
Suna zuwa gida, ya wuce ɗakinsa kai tsaye, itama Afrah tayi nata ɗakin, sam bataso haka yakasance ba, taso ace abun da ta ƙudurta aranta shine ya faru.
Kayansa yashiga haɗawa acikin trolly ɗinsa, saida yatabbatar ya haɗa duk wani abun da yake buƙata, dama kuma jiya aka kawo masa visa’n su.
Tana tsaye agaban mirror daga ita sai wata ƴar fingilan riga, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kansa, akwatinta ya ciro acikin drawer, kallonta yayi itaɗinma kallonsa take.
“Kishirya kayanki, 6 pm zamu tashi gobe insha Allah” yanakaiwa nan azancensa yasakai yafice daga cikin ɗakin.
Mamakine yakama Afrah, “dama ya shirya musu tafiya shine baisanar da’ita ba?” tambayar da tayiwa kanta kenan, ganin bata da wani wadataccen lokaci yasanya, tashiga shirya kayanta acikin trolly’n, da ya fito mata dashi.
Zama yayi akan gado haɗe da jawo diary ɗinsa ya buɗe, abun rubutu ya ɗauka yaɗanyi rubutu, kaɗan kana ya rufe diary’nnasa ya tura acikin wata ƴar ƙaramar jaka.
Washe gari
Kamar yanda ya faɗa ƙarfe 6 dai dai jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar America, a wannan karon baya tunanin zai waiwayo Nigeria, so yake ya koma America da zama gaba ɗaya, wannan shine ƙudurinsa, sai dai idan Afrah tace zatazo Nigeria bazai hanata ba, shikam dai yasa aransa cewa bazai zoba, saidai ko wani babban dalili, me ƙarfi.
*** *** ***
Abuja University Gwagwalada.
Yau suke bikin kammala degree ɗinsu, saboda haka gaba ɗayansu sunacikin farinciki. Kowannensu yasha adonsa cikin shiga ta burgewa gwanin ban sha’awa.
Tsaye take ajikin wata bishiya tana waya, sanye take da baƙar tie abaya gown ajikinta, wacce daga hanunta zuwa ƙasanta aka mamayeta da ado na flowers masu kyaun gaske. Da babban mayafi tayi amfani wajen rufe jikinta, sai dai kuma duk da haka, saida cikinta ya bayyana kansa, sosai taƙara haske da kuma kyau, sai wani ɗaukar ido take, daganinta kaga me ciki, wacce take cikin jin daɗin, yanzu watannin cikinta huɗu kenan amma kuma tuni ya bayyana kansa, ita kanta har mamakin girman cikin nata take, don watanninsa basukai ace girmansa yakai har haka ba.
“Zakizo mu kammala pictures ɗinne kokuma zaki tsaya soyewa” Husnah dake tahowa ga Zahrah tafaɗi haka da ɗan ƙarfi. tayanda Zahrah’n zata jita.
Murmushi Zahrah tayi haɗe da kashe wayar, kana ta juyo da kallonta ga Husnah.
“Kinsan banagajiya da jin muryarsa ne, amma muje mukammala agurguje, saboda gida nakeson nakoma gaba ɗaya jina nake agajiye” Zahrah ta faɗi haka tana ɗan yamutsa fuskarta.
Murmushi Husnah tayi haɗe da cewa “Nima sauri nake saboda yau Man ɗina zai turo magabatansa gidanmu, kuma ayau za’a sa mana ranan aurenmu, nasankuma baza asa ranan da yawa ba, just ba zai wuce 1 month ba”
Dariya Zahrah tayi haɗe da cewa “Lallai Husnah aure kikeso sosai, ji yanda lokaci ɗaya kika falle.”
Dariya sosai Husnah tayi haɗi da cewa “Laifine dan mace irina taso aure? nakai aure, nakuma cika mace me lafiya, kinga kuwa dole naso aure, ke nifa wallahi gaba ɗaya yanzu rayuwata, a daddafe nakeyinta, na ƙosa najini a ƙirjin mutumin, nima yakasheni da irin nasa salon” cikin yanayi na shauƙi ta ƙare zancen.
Dariya dukansu sukayi kana suka tafa.
Basu tsaya an kammala bikin dasu ba, kowaccensu ta nufi gida.
(Kuyi haƙuri, wallahi kwana biu narasa ganewa kainane, gaba ɗaya typing yafita araina, kuma kunsan abun yana aiki ne da zuciya dakuma ƙwaƙwalwa, wallahi dana fara kaina sai yanamin ciwo, saboda haka dole zan taƙaita muku labarin, insha Allah acikin satinnan zan kammala littafin, duk da bahaka naso ba, amma kuma abubuwa sunmin yawa, ina buƙatar hutu kusan na 1 month, idan na bari kuma banƙarisa ba, zan shiga haƙƙin masu karatu, kuyi manage da wannan, yau ko editing banyi ba, saboda ciwon kae, dan Allah kumin uzuri kunji, duk na naƙosa nagama labarin, saboda haka zanci gaba dayi muku shi a gurguje.)
✔️OTE ME ON WATTPAD
@fatymasardauna
Love
Romance
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI!!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
WATTPAD
@fatymasardauna
CHAPTER 113
Kwance take akan gado, hanunta riƙe da littafin hausa, tana karantawa, sanye take da doguwar riga irin bubu gown ɗinnan, zuwa yanzu cikinta ya ƙara girma, har tsoro girman ke bata, ga yawan motsin da takeji acikin cikin nata.
Yajima a tsaye yana kallonta, sosai cikin ya ƙara mata kyau, gashi cikin ya bayyana kansa acikin rigar dake jikinta.
“Ƴan mata na!” yaƙira sunanta cikin wata murya me sanyi.
Da sauri ta dawo da kallonta garesa, murmushi tasakar masa, haɗe da tasowa daga kan gadon, da ɗan gudu gudu, tafaɗa cikin jikinsa ta rungumesa.
Hannuwansa yasanya duka biyu shima ya rungumeta, kiss ya manna mata akan wuyanta, haɗe da lumshe idanunsa, yana me shaƙan ƙamshin jikinta, sosai ƙamshin nata keyi masa daɗi.
“Nayi kewarki madam ɗina me ciki” yafaɗi haka yana me shafa cikin dake jinkinta.
Ashagwaɓe tace “Nima nayi kewarka sosai fa dear!”
“Dagaske kinyi kewata? keda ma kika hanani abun daɗina, two days fa kenan yau baki bani zumana ba!” cikin yanayi na ɗan karya murya yafaɗi haka, lokaci guda yana me marerece idanunsa.
Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba, cike da shagwaɓa tace “To bakaineba saikanamin da ƙarfi, kuma Allah Hubby yanzu idan kajima kanayi sainaji kamar zan amar da kayan cikina, gashi tsoro nakeji idan kana fidda wannan sautin numfashin, kamarfa zaka sume haka kake”
Sake marerece fuska yayi haɗe da kwantar da kanta akan wuyansa, hanunsa ya ɗaura akan cikinta.”Babyn Mama kaine kake wahalar min da mata ko? kuma kaine kake hanawa abani abun daɗi na ko? please my boy kabari yau abani ko kaɗanne, kuma ae balaifina bane, banasanin ma inayin kamar zan shiɗe, kuma ma ae daɗin kine yake da yawa ko Baby boy ɗina?” yatambayi yaron cikin?