NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Cikifa kace Doctor?matana tana ɗauke da cikina?” yatambaya cike da tsananin mamaki.

“Eh mana, ai bazanma wasa ba, dagaske matarka tana ɗauke da ciki, shiyasa take ta amai babu ƙaƙƙautawa” duk cikin harshen turanci irin nasu na America suke maganan. 

Bazai taɓa misalta irin daɗin da yajiba, hakanan ya tsinci kansa da sakin murmushi, tashi yayi ya rungume Afrah, jiyake kamar ya ciro cikin aJikinta, yadawo dashi jikinsa, gani yake kamar zaifi kula da cikin.   Agurguje yayi duk wani cike cike da zaiyi sukabar asibitin.  suna isa cikin gida yayi parking motar, amaimakon yabarta tayi tafiya da ƙafanta, saiya ɗagata caɗak, wai yana gudun kada cikin ya jijjiga.  Akan kujeran falo ya direta haɗe da zama daɓas agabanta, hannayenta yakamo duka biyu, cike da farinciki yace.  “Nagode Afrah, nagode miki sosai, kin bani farincikin dana rasa,  haƙiƙa Allah ne yadubeni yadawomin da farincikina ta hanyarki,  please Afrah, kikulamin da ƴata dake cikin cikinki kinji, daga kan naira ɗaya har 100m zan iya mallakamiki, matuƙar zaki kulamin da ƴata dake cikinki, inasonta inasonta fiye da komai aduniya, Allah ne yadawomin da abuna, dama tawace bata kowa ba, please ki kulamin da cikin dake jikinki, namiki alƙawari zanbaki duk wani abu dakikeso”

Mamakine yakusan kashe Afrah, sam bata fahimci me kalamansa suke nufi ba, yace dama tasace bata kowa ba to wakenan? tambayar da take matuƙar so tasamu me amsa mata kenan.  Ganin ya kafeta da idanunsa ne yasanya tasaki murmushi haɗe dacewa “Nima inason na haifamaka ɗa ko ƴa, kuma insha Allah Zan kula da cikin nan sosai, fiye ma da yanda zan kula da kaina, amma me yasa kaketa cewa ƴa, bamusan fa menene ba macece ko namiji Allahu a’alam”
Murmushi Zaid yayi haɗe da miƙewa tsaye “Mace zaki haifa insha Allahu, wannan bayin kaina ko yin wani bane, yin Allah ne, shiya hanani, yanzu kuma shiya bani, saboda haka bazan gajiya dayi masa godiya ba” yana kaiwa nan azancensa yawuce ɗakinsa.   Haryanzu dai ita bata fahimci ina kalamansa suka dosa ba, kwanciya tayi akan kujera, minti kaɗan bacci ɓarawo yayi gaba da ita.

Shikuwa yana shiga cikin ɗakinsa, ɗan ƙaramin drawer ɗinsa ya buɗe wanda ciki yake aje diary’nsa, ɗauko diary,n yayi yasoma rubutu, yana kammalawa ya buɗe shafin farko na diary’n nasa, take wani hoto wanda ke ɗauke da kyakkyawar fuskarta ya bayyana, tayi kyau ƙwarai acikin hoton, gaɗan ƙaramin bakinta nan yasha lipstick, murmushi yayi alokacin daya kai hanu yashafi kan kumatunta,   ahankali yace “Nasani dama zaki dawo gareni, kobata hanyar zama tawa ba, amma tabbas zaki dawo gareni, gashi kuma kindawo ta hanyar dayafi dacewa,  nan bada jimawa ba zakizo amatsayin tawa ta har abada, duk wuya duk tsanani ke ɗin zaki kasance tawace, nine wanda bakida kamarshi acikin duniya, nine mutum guda ɗaya wanda zai kasance me matuƙar mahimmanci a wajenki, nine wanda bazaki taɓa samun irina ba har abada, ni ɗayane nake da wannan matsayin agareki, bayanni babu wani”   wasu irin hawayene masu zafi suka gangaro daga cikin idanunsa, da sauri yarufe diary’n kana ya shiga toilet donyin wanka, jinsa yake acikin matsanancin farinciki, lallai Allah yamasa kyauta, wacce zata kasance mafi soyuwa agareshi.
(Wayaga Zaid da ƴa ko ɗa????)


Wani irin kulawa na sadidan Zaid ke bawa Afrah, kome takeso adunia shiyake yi mata,  zuwa yanzu harmamakinsa takeyi, irin yanda yake nunamata tsananin ƙauna,  wani lokaci har kuka takeyi, itama tana matuƙar son cikin sosai, amma yanda Zaid ke ƙaunar cikin ba’a magana, tasani badon komai yake nuna mata wannan ƙaunarba saidon cikin dake jikinta,   haka take rainon cikinta cike da ƙaunar abun dake cikinsa, wani lokaci tana mamakin yanda Zaid keta faɗan wasu irin maganganu wanda suke matuƙar ɗaure mata kai, daga zaran yataɓa cikin sai yafara cewa “Babyna kina lafiya ko, na ƙosa kidawo gareni, inakewarki sosai, kizo muyi rayuwarmu wacce bamuyita ba da, muyi rayuwa cikin farinciki, inasonki sosai babyna!” abun dayake faɗa kenan, hakan kuwa mamaki yake bata sosai, duk kuwa yanda taso fassara kalaman nasa, bata iyawa, hakanan take haƙura kawai ta share. Cikin nada wata huɗu Zaid ya ware wani ɗaki dake cikin bedroom ɗinsa, saida yacika ɗakin tam da kayan wasan yara, babu abun da babu nawasan yara acikin ɗakin,   acewarsa ɗakin babynsa ne, itadai Afrah idanu kawai tazuba masa, saboda taga soyayyar dayakeyiwa abun dake cikinta naneman zautar dashi.


Nigeria.

Masha Allah cikin Zahrah ya ƙara girma sosai domin kuwa yanzu yana wata na bakwai ne, sosai cikin yayi turtsetse dashi,  zuwa yanzu batasanya wani kaya sai dogin ruguna, irin masu faɗin nan.
Tana zaune atsakiyar falon, yayinda ta tusa wani tray wanda ke ɗauke da kayan fruit agaba, gefe kuwa plate ɗin dambun nama ne wanda yaji albasa, sai kuma ɗan wake wanda yaji cabbage da cocumber ga tomatoes, yasha mai da yaji, wai duk wannan tulin kayan ciye ciyen Zahrah so take taci kowanne acikinsu.  

Auntie Raliya ce tafito daga kitchine hanunta ɗauke da  wani cup wanda cikinsa ke ɗauke da wani zuma, me magani aciki.

“Manya anata fama kenan” Inji cewar Auntie Raliya.

“Wallahi Auntie ni duk na rasa ma da wanne zan fara, inaga ɗanwakena kawai zanci sauran kuma nabari saina koma gida” Zahrah tafaɗi haka ga Auntie Raliya tana me jawo plate ɗin ɗanwaken ta.

Dariya Auntie Raliya tayi haɗe da zama kusa da Zahrah’n  “Gaskia Bro bai iya ajiyaba, wannan wani irin ɗa ne haka yasa miki acikin cikinki, yaro ne zance ko yarinya, sai shegen ci”

Dariya Zahrah tayi sosai haɗe da kallon Auntie Raliya cikin dariya tace “Wallahi kuwa Auntie, dubeni fa yanda nayi ƙatuwa, nayi muni, shikuma duk kwanan duniya ƙara kyau yake, gaskia ni bazan yarda ba, auntie wayo kawai yamin”
Dariya Auntie Raliya tayi haɗe da miƙowa Zahrah kofin dake riƙe a hanunta.   “Ungo amsa kishanye duka”
Zaro idanu Zahrah tayi, haɗe da kallon Auntie Raliya’n “Auntie kamar tsumi ne fa, acikin cup ɗin?”
“Ba kama bane, tsumine me kyau na mata, wanda yake matuƙar wujijjiga oga, amsa kisha banason gardama” Auntie Raliya tace tana ƙoƙarin kai kofin bakin Zahrah.

Kwaɓe fuska Zahrah tayi, haɗe da ɗan marerece ido. “Wallahi Auntie tsoro nake insha wani tsumi, a yanzun, kinsan kuwa yanda nake fama, doctor fa shiɗewa yake, nasha wannan kuma ae shikenan sumar dashi kikeso nayi”

Dariya sosai Auntie Raliya tayi, haɗe da ɗaukan tsuminta ta shanye  “Shikenan to idan kin haihu na miki haɗi na musamman, matar doctor, ashe ba abanza ba, gaba ɗaya ƙanina ya sukurkuce akanki, wato kinsan me kikeyi masa” cewar Auntie Raliya.
Dariya Zahrah tayi haɗe da cigaba da cin ɗanwakenta, sai kaɗa kai take wai ɗan waken yayi daɗi, itakuwa Auntie Raliya saiyi mata hira take,  sosai suka seta ita da ƴan uwan mijinta,  ƙauna sadidan take samu daga wajen Hajiya,  yayinda Auntie Raliya ma ke nuna mata so, sun saba sosai da Auntie Raliyan, harjinta take kamar ƴar uwarta tajini, don babu abun da take ɓoyewa Auntie Raliyan, dayake Auntie Raliyan ma irin wayayyun matan nanne, basu da nuƙu nuƙu, baruwanta dawani abu waishi surukanta, ta ɗauki Zahrah’nne kamar ƴar ƙaramar ƙanwarta, don har sirrin yanda ake kama me gida a hanu take faɗa mata..
Sunsha hira sosai da Auntie Raliya, sai bayan sallan Isha doctor Sadeeq yazo ya ɗauketa suka koma gida.  Washe gari kuwa, tun 7 am tatafi gidansu amarya Husnah, don yau za’ayi kamunta, kuma itace best friend, don ma ciki yayi mata cikas. 
Anyi kamu cikin kwanciyar hankali, yayinda kamun ya ƙawatar sosai, anyi ɓarin naira sosai baga gidansu ango ba baga gidan su amarya ba, naira tayi kuka don ankasheta a wannan ranan, kayan da amarya tasanya ma kaɗai kuɗinsu baƙaramin yawane dasu ba. Zahrah bata bar gidansu Amarya ba sai bayan magrib kusan 9 pm,  haka ta koma gida agajiye. Washe gari kuma,  aka rangaɗa walima, shima sosai yaƙayatar don anyi musu wa’azi me ratsa jiki,  ranan friday kuma aka ɗaura auren Husnah da angonta,  sosai dai akasha shagalin bikin Husnah, inda Zahrah tataka rawar gani sosai, wajen ganin tabawa ƙawartata kyauta, wacce zata burgeta. Ranan da aka kai Husnah ɗakin mijinta sosai Zahrah tayita mata tsiya, ita kuwa Husnah ko ajikinta, cewa ma tayi “Mijinta baifi ƙarfinta ba, bata wani jin tsoro, tsaf zata iya ɗauke buƙatarsa”…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button