NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna shiga cikin asibitin direct aka wuce da Zahrah labour room.  Wasu likitoti ne guda uku mata akanta,  babu abun da take sai salati da cije baki, ita kaɗai tasan me takeji,  ganin bazai iya jurewa ba, yasanya sa faɗawa cikin labour room ɗin, dayake dama asibitinsu ya kawota, yanazuwa gaban gadon, ya kama hanunta,  buɗe wahalallun idanunta tayi ta kalleshi,  atare wasu hawaye masu zafi suka fito daga cikin idanunsu,  matsanancin tausayinta yakeji, fiye da tunanin me tunani,  Hanunsa dake saman nata, takama ta matse, haɗe da girgiza masa kanta, cikin wata irin murya me ɗauke da tsananin ciwo tace.
“Kayafemin idan na mutu dan Allah!”

Kai ya girgiza mata da sauri haɗe da cewa. “Bazaki mutu ba Zahrah, zamu rayudake acikin duniyarnan insha Allah, zaki raini abun da zaki haifa ɗa hanunki, insha Allah!!” cike da tsananin rauni ya faɗi haka, sosai zuciyarsa ta karye,  bata sake ce dashi komaiba, kawai ta ɗauke idanunta akansa, cigaba tayi da nishi haɗe da karanto addu’a, Doctor na riƙe da hanunta, yana tofa mata addu’a, haɗe da shafa kanta, ƙwalla ne kawai suke fita daga idanunsa. Wani irin yunƙuri haɗe da nishi tayi sai ga kukan jariri ya cika ɗakin.  Laƙwas haka tayi akan gadon, lokaci guda komai nata ya tsaya, motsi da numfashinta, duk suka ɗauke, kumatunta yasoma bubbugawa yana ƙiran sunanta, hawaye kuwa akan fuskarsa wani na koran wani kamar an buɗe famfo.
Wata daga cikin likitoti matanne ta ɗauki yaron, takaishi wajen da ake aje jariri, kallon Dr.Sadeeq da yake hawaye tayi, tace
“Haba Sir, wannan fa ba wani abun damuwa bane kasani, yanzu zata farfaɗo insha Allah”
Hankalinsa ma baya wajenta balle yaji me take cewa, shigaba ɗaya ma basirarsa toshewa tayi, amaimakon yabata taimakon dayasan zai dawo da ita hayyacinta, saiya tsaya yana ƙiran sunanta, yana kuma jijjigata.   Likitance tashiga bata taimako,  wani ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe,  alaman ta farfaɗo, bayan kamar mintuna uku ta shiga buɗe idanunta a hankali,  dashi tafara tozali ya tusata a gaba, sai kuka yake, hanunta ta miƙa masa, da sauri yataho yakama hanun,  kissing ɗinta yayi akan goshinta, haɗe da  rungumeta, atare suka shiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, sun kusan 8 minute ahaka, kafun taɗan janye jikinta daga nasa, murya a sanyaye tace “Ina Hajiya?”  “Tana waje” yabata amasa a taƙaice, yana me binta da kallo me ɗauke da tsananin ƙauna, haɗe da tausayi me ruguza zuciya.  

Wata daga cikin likitotinne tace “Sir yakamata a kimtsata, sai mukaita ɗakin hutu”
Juyowa yayi ya kalli likitan haɗe da cewa. “Babu buƙatar ɗaya daga cikinku sai ta kimtsata, nida kaina zan kimtsa abata”

“Sir tana buƙatar ɗinkifa, saboda ta ƙaru” likitan takuma faɗan haka.

Da sauri ya kalli Zahrah, take hawayen dake cike acikin idanunsa, suka gangaro kan ƙuncinsa, wani sabon tausayinta ne yasake kamasa, “Ina sam bazai iya mata ɗinki ba, bazai taɓa koda kwatantawa bane ma, dakansa da hanunsa ya huda Zahrah’nsa? wannan abun bamai yiwuwa bane” yafaɗi haka acikin ransa. Baice da likitotin komai ba, sai matsawa dayayi kusa da Zahrah, yasake sumbatarta akaro na biyu, wata allura ya ɗauko yayi mata a hanunta, tayanda yasan bazataji zafiba,   kallonta yayi still hawaye yake, daƙyar ya iya jan ƙafansa yafice daga cikin ɗakin, abun mamaki kota kan jaririn baibiba, tun dama yafaɗo dunia bai kulasaba, yanata rabin ransa Zahrah. 

Likitotinnan ne suka ɗinke ta tsab, saidai bata wani ji zafi sosai ba, domin alluran da Doctor yayi mata, allurace me ƙarfi dake hana jin zafi, suna gama ɗinketa, wata acikin likitotin takamata suka wuce bathroom,  likitance ta haɗa mata ruwa tayi wanka, tana fitowa likitan tabata wata riga wacce takarɓo awajen Hajiya tasanya, miƙo mata jaririn likitan tayi, hanunta na rawa haka ta karɓi jaririn ɗan nata, tana karɓansa taji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, fuskar Dr.Sadeeq ta kalla sak akan fuskar yaron nata, lokaci ɗaya taji wani irin so da ƙaunarsa sun cika mata zuciya, tana fitowa acikin labour room ɗin, Hajiya da Dr.Sadeeq sukayo kanta, daga ita har jaririn Hajiya ta haɗasu ta rungume, sai ga ƙwallan farinciki na zuba daga idon Hajiya, amsar yaron tayi daga hanun Zahrah haɗe da sanya sa acikin ƙirjinsa ta rungumesa, sosai takejin ƙaunar jikan nata, musamman dataga yana kama da ubansa, sai dai duk da haka akwai kamannin Zahrah a tattare dashi. Dr.Sadeeq kuwa ko kunyan Hajiya dake tsaye baiyiba yaje ya rungume matarsa, kyakkyawan kiss ya sauƙe mata akan ƙuncinta, haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗanta.

Saurin tureshi tayi daga jikinta, ta haye gado ta kwanta, tana sauƙe numfashi, kawar da kanta gefe tayi, wasu irin siraran hawayene suka gangaro daga cikin idanunta, ita kaɗai tasan menene yasata wannan hawayen. Mintuna kaɗan bacci ɓarawo ya ɗauketa, dagani kuma kasan tanajin daɗin baccin.

Alokacin da Doctor yakarɓi jaririn ahanun Hajiya, kafesa yayi da manyan idanunsa, wani irin ƙaunar ɗan nasa ne ke fusgarsa, sosai yaron ke kama dashi, rungume ɗan yayi acikin ƙirjinsa, sai kawai ga hawaye nafita daga cikin idanunsa, kallonsa ya maida ga Zahrah wacce take bacci, wutar sonta ne ke ƙara ruruwa acikin zuciyarsa, lallai Zahrah tana da babban matsayi agareshi, ta basa farinciki me ɗorewa, tahaifa masa ɗa, tayi masa komai a duniyarnan, baisan damene zai saka mata ba.

Hajiya dakanta ta ƙira Inna tasanar mata maganan haihuwan, dama tuni Aunty Raliya kam ta tsofe a asibitin, koda su Inna sukaji cewa Zahrah ta haihu, ba ƙaramin farinciki sukayi ba, sunji daɗi sunyi murna sosai, ita da Baffa duka suka rankayo zuwa asibitin.

Ba ita tafarkaba sai bayan azahar, bathroom ɗin ɗakin da take ciki ta shiga, haɗe da sake tsabtace jikinta, tana fitowa kuwa tasamu Doctor ya karɓo musu takardan sallama. Gaba ɗaya likitotin asibitin babu wanda baitaya Dr.Sadeeq murnan samun ƙaruwan da yayi ba, har ɗaki suke zuwa su duba Zahrah, sukuma tayasu murna.

Hanyar da Hajiya taga ya miƙa ne yasanyata cewa.
“Wai ina zaka damu ne Sadeeq?”

Da compidence ɗinsa ya juyo gareta haɗe da cewa. “Gidana mana Hajiya”

“Gidanka? to ba gidanka zamuba, gidana zamuyi, hauka kake na ɗauki yarinya da ɗanyen jiki, na baka? wama zai tsaya ya kula da ita? maza juya akalar motarnan” Hajiya tafaɗi haka babu alamar wasa akan fuskarta.

Sam bahaka yasoba, amma babu yanda zaiyi, shikenan shi baza abarsa yaji ɗumin matarsa dana ɗansaba, haka yata ƙunƙuni acikin ransa shi kaɗai, har suka isa gidan Hajiya.

Abinci mai rai da lafiya Hajiya ta kawowa Zahrah, ga kuma gasashshen nama, bayan taci abincin Hajiya dakanta, tasakeyi mata wanka.
Zama tayi agaban mirror tashafe jikinta da manta me daɗin ƙamshi, powder tashafa afuskarta, bata tsaya nanba harda janbaki tashafawa laɓɓanta, ga kuma kwalli da ta sanyawa cikin idanunta, mascara ta ɗauko ta zizira akan eye lashes ɗinta, take fuskarta taƙarayin kyau. Wani riga da sket na material me tsada tasanya ajikinta, take takoma ƴar baby kamar yanda take da, dogon gashinta ta kanannaɗe a bayanta, haɗe da hayewa gado, zataci gaba da bacci, miƙo mata yaron Inna tayi haɗe da cewa “Wani kwanciya kuma zakiyi bayan baki bawa yaron nono ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button