NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, da ƙyar ta iya ciro nonon nata ta kai bakin yaron, yana kamawa ta runtse idanunta da ƙarfi, saboda wani zafi da taji, haka dai ta ɗan daure, shikuwa yaron sai zuƙeta yake, gajiya tayi dajin zafin ta cire nonon abakinsa, kwantar dashi tayi, itama kana ta kwanta agefensa, baccin gajiya ne ya kuma ɗaukarta…

Idan dai hartaji sauƙan numfashinsa akan wuyanta, to yazame mata dole ne farkawa daga baccin da take, yanzu ma sauƙan numfashin nasa taji adai dai saitin kunnenta, a hankali take ware idanunta harta sauƙesu akansa. Murmushi yasakar mata haɗe da ɗaura kansa akan ƙirjinta.

“INA SONKI!!!” yafaɗa murya a sanyaye….

(Insha Allah gobe zanmuku update, yau naso nayi da yawa, to wallahi tsoron editing nake, amma Insha Allah gobe kujira sabon posting, maybe ma yanzu kullum zanna baku update saboda mugama book ɗin da wuri)

  *28/February/2020*

✅OTE ME ON WATTPAD
@fatymasardauna

Love

Romance

????????????????????????????????????????

      SHU’UMIN NAMIJI !!

    Written By
Phatymasardauna

Dedicated To My Brother KHABIER

????Kainuwa Writers Association

         
WATTPAD
@fatymasrdauna

     CHAPTER 115

“NIMA INASONKA!”

Tafaɗa tana me lumshe idanunta. Iskan bakinsa ya hura mata akan fuskarta, haɗe da sake rungumeta,  ɗayan hanunsa yasanya ya shafi kan jaririn nasa, dake ta bacci.   Murmushi Zahrah tayi ganin yanda Dr.Sadeeq ya kafe yaron nasa da ido.    Hajiya da Inna ne suka shigo cikin ɗakin atare, da sauri Zahrah ta janye jikinta daga na doctor, shima a kunyace ya sauƙa daga kan gadon yana sosa kai.

“Hmmm Allah yashirya, Inna kina gani ko, wai da ahakan yakeso na basa ita” inji cewar Hajiya.

Murmushi kawai Inna tayi batace komai ba.  ( Su Inna anzama nitsaljin????)   Kallon Doctor Hajiya tayi haɗe da cewa “Zo muje inason magana dakai”  babu musu yabi bayanta suka fice daga cikin ɗakin.

Zama tayi akan kujera haɗe da maida hankalinta garesa.
“Me dame kake shiryawa sunan nanne?  sannan kuma da wani suna kayiwa yaron huɗu ba?”

Murmushi ya ɗanyi haɗe da cewa  “Ai nagama shirina tuntuni Hajiya, dama lokaci kawai muke jira,  sannan kuma dama tuntuni sunan babanta nake son sawa yaron, dashi kuma nayi masa huɗu ba”

Hajiya tace “Masha Allah, To Allah Ubangiji ya rayasa, hakan da kayi kuma ka kyauta, tashi kaje dama maganan da zamuyi kenan” 

Miƙewa yayi haɗe da yi mata sallama yafice daga cikin falon.

Lokacin da Husnah tazo ganin Baby kusan haukacewa tayi, sai santin yaron take wai yayi mata kyau sosai, komai nasa irin na babansa, ga idanunsa kyawawa, itadai Zahrah dariyanta kawai take, saboda itama Husnan tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki.

Akwatuna guda biyu Dr.Sadeeq ya  kawo wa Zahrah, ɗaya nata ɗaya na baby’nsa  wai kayan barka,  kayane masu kyau da tsadar gaske sosai ya kashe kuɗi, wai ahakanma wasu kayan nanan zuwa.

Kulawa Zahrah take samu a wajen Hajiya sosai, idan kaganta ma kamar ba itace ta haihu ba, sosai jikinta ya murje, tasakeyin fresh, hasken fatarta ma sosai ya ƙaru, komai nata ya cika, taƙara kyau akan nada, shikansa Dr.Sadeeq idan yaganta, ko son ɗauke idanunsa  akanta bayayi, saboda yanzu tasake zama wata mace ta musamman,  duk inda ta zauna kuwa ƙamshi take rabawa.

Ranar suna yaro yaci sunan baban Zahrah wato Adam, za’ana ƙiransa da (Asad) lokacin da labarin sunan  da aka sawa yaro yazo kunnen Zahrah sosai taji daɗi, wani irin farinciki taji acikin ranta, girman Doctor kuwa ya ƙaru acikin idanunta, ta tabbatar cewa shiɗin mai so da ƙaunarta ne.
Da sassafe meyi mata meckup tazo ta tsantsara mata ado, sosai fuskarta tasha kwalliya,  wani haɗaɗɗen lace orange and milk colour tasanya ajikinta, wanda yaji ɗinkin riga da sket irin 12 piecess ɗin nan, sosai kayan sukayi mata kyau, domin sunja kuɗi wajen sayansu da ɗinkasu, kowa yaga Zahrah da babynta saiyace masha Allah. Saboda  sunsha kyau sosai. Hidima sosai akayi tundaga kan abinci da abun sha, har izuwa abubuwan da za’a rabawa baƙi,  akwati guda biyu Hajiya tayiwa Zahrah da ɗanta, haka Baffa ma akwati yayi mata Inna ma zagewa tayi tayiwa Zahrah akwati shaƙe da kaya, Auntie Raliya ma akwati ta mata,  sosai Zahrah tasha kaya, har rasa inda zata sa kayan tayi,  ana cikin haka saiga kayan Dr.Sadeeq sun iso, akwatuna huɗu, biyu natane shaƙe da kaya,  sauran biyun kuwa  na yarontane,  bata gama mamakin irin dukiyar da Dr.Sadeeq yakashe mata ba, saiga Aunty Raliya tana rangaɗa guɗa, hanunta riƙe da key, danƙawa Zahrah key ɗin tayi ahanunta, haɗe da cewa “Ungo amsa kyautace ta musamman daga mijinki, ya baki kyautar gidansa dake cikin asokoro” mamakine ya kusan kashe Zahrah

“Gida kuma Aunty?” ta tambayi aunty Raliya don tayi tunanin ko kunnuwanta ne basu jiye mata da kyau ba.

“Ƙwarai kuwa gida, saima kinga gidan, don gidane me tsananin kyawun gaske, yafa kashe kuɗi sosai wajen ƙawata gidan”  Inji cewar Aunty Raliya.

“A’a Aunty gaskiya nikam banaso, wani irin kyautane haka? hidimar da Doctor yakeyi dani tayi yawa, daga haihuwata zuwa yau yakashe kuɗi yafi 3 million fa Auntie, yanzu kuma yace yabani kyautar gida suku tum, inajin tausayinsa Aunti banason nazama rauni acikin arzikinsa” Zahrah tafaɗi haka da iyaka gaskiyarta.

Murmushi Auntie Raliya tayi haɗe da sanya hanu ta dafa duka kafaɗun Zahrah.

“Kada ki damu Zahrah, shi ɗinfa mijinki ne, kuma kome zaimiki aduniyarnan bazai biyaki ba, kamar yanda kema bazaki iya biyansa duk abun daya miki ba, saboda haka babu wani abun damuwa don yamiki wannan kyautar, kin cancanci hakanne agareshi, don haka amshi makullin gidanki, ke dai kawai kiyi masa godiya, irin wacce ta dace” Aunty Raliya ta faɗi haka tana me damƙawa Zahrah makullin gidan ahanunta.

Kuka Zahrah ta fashe dashi tana jin ƙarin ƙaunar mijinnata na huda mata zuciya, lallai yazama dole agareta taƙara ƙaimi wajen kyautata masa. 

Yamma nayi aka haɗa walima me rai da lafiya, bayan malama tazo tagabatar da wa’azine akayi ciye ciye, aka kuma sha drinks, duk wanda yazo sunan kuwa babu wanda baisamu kyaututtuka ba, abun sai dai ace Alhamdulillah, kafun magriba tuni mutane sun watse, gida ya saura daga Hajiya sai Zahrah da kuma Aunty Raliya.

Wanka tasakeyi ta tsantsara ado cikin wani irin meterial me kyau da tsada, wanda yana cikin kayan da Doctor ya ɗinka mata don fitan suna, doguwar riga akayi mata wanda ya matuƙar kama jikinta sosai,  dogon gashinta dayasha saloon ta kanannaɗe atsakiyar kanta, ba abun dake fita ajikinta sai ƙamshin humra dana body spray.
Zama tayi akan gado haɗe da ɗaukan wayarta tashiga kan whatsapp, yaronta kuwa tuni dama yana wajen su Hajiya dake zaune a falo suna hira,   Sadiya me aikin Hajiya ce tashigo cikin ɗakin haɗe da sanarwa Zahrah cewa wai tayi baƙo yana falo.
Jitayi gabanta yaɗan faɗi, amma saita dake tace da Sadiyan tace da baƙon tana zuwa.
Mayafi ta ɗauka ta yafa ajikinta, kana ta zura flat shoe ɗinta, tafice daga cikin ɗakin.

Su Hajiya tasamu zaune afalon, sai kuma wani, wanda bata ma taɓa ganin fuskarsa ba.  Kafun takai ga gaishesa, shiya ɗago mata gaisuwa, amsawa tayi tana ɗan murmushi,    gyara tsayuwansa yayi haɗe da cewa..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button