SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Saƙone dama akabani nakawo miki, yana waje, idan ba damuwa muje saiki gani”
Kallon tsoro tashiga yi masa, saboda batasansa ba balle tasan wanene ya aikosa.
“Badamuwa, Raliya rakata sai kuje kuga saƙon ko”
Hajiya tafaɗi haka, don ta lura da tarin tsoron daya bayyana akan fuskar Zahrah’n.
Hakan kuwa akayi tare suka fita da Aunty Raliya.
A compound ɗin gidan suka tsaya gaban wata haɗaɗɗiyar mota ƙirar mercedes maroon colour, mutuminne ya bubbuɗe ƙofofin motar, take kayan dake shaƙe acikin motar suka bayyana, ɗan makulli ya miƙowa Zahrah haɗe da cewa
“Ranki ya daɗe gashi ni nacika umarnin da aka bani, wannan kyautace daga megida na, yace na ce miki Allah ya raya”
Mamaki haɗe da al’ajabi ne suka kama Zahrah da Aunty Raliya.
“Kyauta daga me gidanka kuma? wayeshi to?” Zahrah tayi masa duka waƴannan tambayoyin cike da son jin amsa, haɗi da kuma mamaki, gani take kamar mutumin baida cikakken hankali.
Murmushi kawai ɗan aiken yayi haɗe da sake miƙo mata makullin motar yace
“Kiyi haƙuri bai bani damar sanar miki dashi ɗin kowaye ba, amma yace dan Allah ki karɓa”
Ta buɗe baki zatayi magana kenan motar Dr.Sadeeq ta kutso kai cikin gidan.
Kasa cewa komai tayi har Dr.Sadeeq yafito daga cikin motarsa, ya ƙaraso garesu, kallonsa Zahrah tayi shima kallonta yakeyi.
“Hajiya ga makullin ni zan wuce” wannan mutumin yafaɗi haka, yana sake miƙa mata ɗan makulli.
“Ko ma waye ya aikoka, kace masa banaso, don bana buƙata” tafaɗi haka tare da juyawa daniyar komawa inda ta fito.
“Zahrah!”
Sunanta da Dr.Sadeeq yaƙirane yasanyata tsayawa cak haɗe da juyowa tana kallonsa.
“Zoki amsa, ki kuma yi masa godiya” Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me karantar yanayinta.
Cike da mamaki tace “Amma…”
“Banaso kice komai ki amsa kawai nace” yakatseta daga maganar da take ƙoƙarin yi.
Jiki asanyaye ta karɓi makullin motar.
Ciki ciki tace “Kace nagode”
“To” kawai ɗan aiken yace kana ya juya yafice daga cikin gidan.
“Wai meke faruwa ne, waye ya aikosa?” Aunty Raliya ta tambayi doctor, don ta lura kamar yana da masaniya akan wanda ya aiko motar da cikinta ke shaƙe da kaya.
Murmushi Doctor yayi haɗe da cewa “wani aminina ne dake zaune a Dubai, shine dana gaya masa ta haihu yayi mata wannan kyautar”
Dafe ƙirji Aunty Raliya tayi tare da cewa
“Lallai wannan koma wayeshi yanaji da naira, wannan motarfa zatakai 4million inma bata fi ba, ga kuma kayan dake cikinta, wanda suma kaɗai sun haura 1m, me kenan yake nufi?”
“Babu wani abun da yake nufi Aunty, haka dama shi yake kyautarsa, muje ciki ko” yaƙare maganar yana kallon Zahrah wacce ta daskare a wajen.
Cike da mamakin kyautar abokin Doctor ɗin Aunty Raliya taja ƙafanta takoma falon Hajiya, Zahrah ma jikinta a sanyaye tabi bayanta, shima falon yanufa, yanda yaga tana tafiya asanyaye ne yasanyasa yin murmushi kawai.
Bata tsaya a falon ba direct ɗakin dayake masauƙinta ta wuce, tsayawa tayi a gaban mirror zuciyarta cike da tarin tambayoyi kala kala, sam bataji zuciyarta ta aminta da kyautar nan da’akayi mata ba, kwata kwata batama yarda cewa wai abokin Doctor bane ya bata. Tana acikin tunanin, yaturo ƙofar ɗakin yashigo bakinsa ɗauke da sallama.
Amsa masa sallaman nasa tayi haɗe da zuba masa idanunta, dagani kai kasan tambayoyine cike a bakinta.
takowa yayi ya ƙaraso daf da ita, hanunsa yasanya ya jawota jikinsa, saida yashaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta, ya sauƙe ajiyar zuciya, kana yace.
“Kinyi kyau sosai”
Murmushi ta ƙaƙalo haɗe da cewa. “Nagode”
Cikinsa yashafa tare da cewa. “Yunwa nakeji sosai, nayi missing sweet cook ɗinki, please ko zaki kawomin abinci?”
“Meyasa kake barin kanka da yunwa? kasan banaso, yanzu me zakaci na kawo ma?” tatambayeshi cike da kulawa.
“Koma me idan kika kawomin ni mai iya ci ne” yafaɗi haka yana me zama a bakin gado.
Harta kusa fita daga cikin ɗakin sai kuma ta tsaya cak, haɗe da juyowa, idanunsu yafaɗa cikin na juna, domin dama shima kallonta yake.
“Waye ne yaturomin da mota? Nasan kasan ko waye, domin zuciyata tafaɗamin cewa, ba abokinka bane ya turo, kamar yanda kafaɗa a baya” tambayar da tayi masa kenan, cike da burin samun amsa agareshi.
“Baki yarda da abun dana faɗa ba kenan?” ya tambayeta yana me ƙara tsareta da manyan idanunsa.
Murya a sanyaye tace “Kayi haƙuri, bawai ina nufin kamin ƙarya bane, kawai dai naji zuciyata ce bata gamsu da amsar da ka bayar ga Aunty Raliya ba”
Murmushi yayi haɗe da cewa “Zuciyarki tafaɗa miki gaskiya, domin kuwa ba abokina bane yaturo kamar yanda na faɗa a baya”
Waro idanunta tayi, duk da zuciyarta ta raya mata cewa ba abokinnasa bane, amma kuma duk da haka bata tsammaci jin haka daga bakinsa ba.
“Waye?” tatambaya murya na rawa.
“ZAID” yabata amsa ataƙaice…
(Nagaji kuyi manage, idan nasha ruwa zan ɗora daga inda na tsaya)
29/February/2020/
✔️OTE ME ON WATTPAD
@fatymasardauna
Love
Romance
One Love My Wattpadians
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
WATTPAD
@fatymasardauna
Chapter 116
“ZAID!” ta maimaita sunan abakinta cike da tsananin mamaki.
Yanda yaga jikinta na ɓari shine abun daya basa mamaki, zallan tsoro ya hango kwance akan fuskarta, yayinda cikin idanunta kuwa, suka bayyana soyayyar dake kwance acikinsu, wato soyayyar ZAID, shi yasani ba tun yauba, bakuma zai yaudari kansa ba, yasani ƙwarai Zahrah na son Zaid, so ba irin na wasaba, so matsananci, amma kuma babu yanda zaiyi, dayana da iko to daya cire mata son Zaid acikin zuciyarta, amma wannan banasa bane, na Allah Ne, yasan Zahrah tana sonsa, amma soyayyar da takewa Zaid ta dabance, da ace zai iya, to daya danne zuciyarsa, ya miƙata ga Zaid, yasan hakan zai samarmusu da farinciki, ita da Zaid, amma kuma yasan koda yayi hakan to ba mafita bane, domin ayanzu yasan dole idan baya tare da Zahrah tayi kewarsa, yana sane da cewa yakafa mata tutar son sa, wanda bazata ankara da hakan ba, har sai randa yazama baya tare da’ita, baya fatan wata ƙaddara ta rabasu, amma yasani ko mai daren daɗewa sai sun rabu, saboda akwai mutuwa, koshi ko ita, watarana ɗaya dole zai bar ɗaya, yau idan baya raye, baya fata Zahrah ta auri wani namiji idan ba Zaid ba, tunaninsa yayi nisa, baisan da cewa ta ƙaraso inda yake ba, saida yaga ta zube a gabansa, tana kuka, cikin muryar kukan takecewa.
“Kada kamin haka doctor, wallahi ni banason duk wata kyauta da zatafito daga garesa, namantasa acikin rayuwata, banaso kuma nasake tunasa, kamayar masa da kyautarsa, bana buƙata farincikin da kake bani kaɗai ya isheni”
Tunda tafara maganan yake kallonta, ajiyar zuciya yayi, haɗe da kamo hannayenta, cikin murya me sanyi yace. “Kinsani bakyau maida hanun kyauta baya, meyasa to zakiyi haka? mekike tunani akan Zaid?” ɗan dakatawa da maganar yayi, tare dayin wani murmushi, kana ya miƙe tsaye, daga zaunen da yake.
“Kyautace kawai ya miki, ai atunanina hakan ba wai yana nufin wani abubane, bazan tilasta miki ba, amma nasan abundake cikin zuciyarki, don gashi har a idanunki sun nuna, so ba ƙarya bane Zahrah, haka kuma ba laifi bane, don zuciya na dakon so, wannan ma wata ƙaddarace, wanda babu wani wanda ya isa ya kauce mata” yanakai ƙarshen zancen nasa yanufi hanyar fita daga ɗakin.