NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Hajiya dake kallonsu ta window tasaki murmushi haɗe da komawa cikin falonta ta zauna, aranta tanayi musu fatan shiriya.

Saida suka biya ta JABI lAKE sukayi sayayya tukun kafun daga nan suka wuce gida.

Wanka ta sakeyi ta shirya kanta cikin wata irin fitinanniyar sleeping gown, wacce ta bayyana komai na surarta bata ɓoye komai ba,  rigar doguwace har kusan ƙafa, amma kuma duk da haka itaɗin kamar babu take, kasancewarta shara shara.   dogon gashinta ta sake a bayanta, haɗe da shafe jikinta da shu’umar Humra,     wani sweet Lip Gloss tashafa akan leɓenta.

Yana zaune a falo yana danna laptop ɗinsa,  ƙamshinta ne yafara kawo masa ziyara, lokacin daya sauƙe idanunsa, akanta sai da yaji wani irin shock ajikinsa,  da sauri ya miƙe ya ƙarasa gareta.   buɗe hannayensa yayi daniyar rungumeta, da sauri ta matsa gefe, tanayi masa dariya, haɗe da yin wata irin tsayuwa,  wacce takusa zautar dashi.

Lumshe idanunsa yayi tare da sanya hanunsa ya jawota jikinsa. Ƙam ya rungumeta, sai gashi yana sauƙe ajiyar zuciya akai akai.   Kallon juna suka shiga yi idanun ko wannensu ɗauke da tsananin sha’awar ɗan uwansa. Jikinsa na rawa ya kama lip ɗinta na ƙasa, yana tsotsa ahankali, jiyake kamar yanashan honey.    da kanta ta zame rigar dake jikinta, ta faɗi ƙasa, take surarta ya bayyana,  hmmm ba yau yafara ganinta ba, amma kuma ya zautu ƙwarai daganin surar jikinta, jiyake kamar ma baitaɓa kusantarta ba, sosai yayi missing ɗinta.    Jikinsa na rawa ya ɗauketa suka wuce bedroom,  tuni dama Asad yayi bacci, dama shi haka yake sam baida ƙiriniya,  daya ƙoshi sai bacci, bakuma zai tashiba sai dai idan yanajin yunwa.  

A yau ɗin ne suka sake tabbatar da cewa sunyi kewar juna,  musamman ma  Doctor Sadeeq da kusan cinyeta ne kawai baiyi ba, gaba ɗaya ya zauce, ya susuce, wasu maganganu yake wanda ita kanta batasan me yake cewa ba, saboda sun lula wata duniya ta musamman, wacce  sukayi nisa  acikinta basaji basa gani, kansu kawai suka sani. Aranan nan wata zuma suka shayar da junansu, wanda bazasu taɓa mantawa ba. Wannan ranan takasance rana ta biyu masu muhimmanci a garesu.


Bayan wata 6……..

America

Zufa ne keta ketowa ta goshinsa, gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa, kai komo yaketayi agaban labour room ɗin sama da 1 hour kenan yana abu ɗaya, jiyake kamar yasanya hanu akansa yaita ƙwala ihu.  Ɗaya daga cikin  Nurse ɗin dake kanta na fitowa  ya nufi wajenta, da sauri idanunsa sunkaɗa sunyi jajur dasu.  Murmushi Nurse ɗin tayi masa haɗe  da cewa “Ina tayaka murna, matarka ta haihu, kasamu baby girl”   wani irin sanyin daɗi yaji acikin ƙirjinsa, baisan lokacin dayayi sujja don nuna godiyarsa ga Allah ba. 

Ana kaita ɗakin hutu, wata nurse tace yashigo ya karɓi babynsa,    lokacin daya sanya hannayensa ya amshi babyn, wani irin kukane ya ƙwace  masa, alokacin da idanunsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskarta kuwa,  bugun zuciyarsa ne ya ƙaru, saboda  kokaɗan  yarinyar bata kama da mahaifiyarta,  durƙushewa yayi aƙasa, riƙe da yarinyar tasa yana kuka, hakan kuwa sosai yabawa likitotin mamaki.

Bakomaine yasa sa yake kuka haka ba,  face tsananin danasani na rayuwar da yayi abaya da yake.   yakasance mazinaci, mashayin giya.  “Yanzu idan ƴarsa mafi soyuwa agaresa, tataso taji labarin abun da ya aikata a baya,  wani irin kunya zaiji? mezaice da’ita idan ta tambayesa, meyasa yazamo haka?” tambayar da yayiwa kansa kenan, amma kuma baida amsa, baida kuma me amsa masa.

Rungumeta ya sakeyi tsam,  acikin ƙirjinsa, ahankali yace.

“Kindawo gareni Zahrah, Allah yadawomin dake, Inasonki Inasonki, inamiki so na musamman Allah ya albarkaceki ƴata!!!” kiss ya manna mata akan goshinta, kana yazuba mata idanu,  bazaiyi mamakin kamannin daya gani akan fuskar ƴartasa ba, saboda yasan ba aja da ikon Allah, kuma hakan ma wata rahamace da Allah yayi masa,  Allah ya hanasa Zahrah alokacin dayaso, yanzu yakuma basa Zahrah alokacin dayaso,   hancinta bakinta duka kalan nasa ne, amma kuma idanunta tamkar idanun Zahrah aka ciro aka sanya mata, kallon farko da yarinyar tayi masa, saida yaji tsikar jikinsa ya tashi, saboda gani yayi tamkar Zahrah ce dakanta agabansa.  yana rungume da yarinyar ya ƙarasa gaban Afrah dake kwance akan gado tana kallonsu,  ranƙwafowa yayi ya manna mata kiss akan goshinta, hanu yasa yashafi kumatunta, haɗe da cewa “Nagode ƙwarai Afrah, Allah ya miki albarka, bazan manta da wannan ƙoƙarin da kikamin ba, Inasonki”

Karo na farko kenan arayuwarta da taji kalmar nan tafito daga bakinsa akanta,  “Inasonki” ta maimaita kalmar abakinta cike da mamakinsa.
Kansa yajinjina mata haɗe da sakin murmushi. 

“Ki kwanta ki huta, nasan kinsha wahala sosai” yafaɗi haka yana shafa kanta.
Lumshe idanunta kawai tayi saiga hawaye nabin kan fuskarta. Hanu ta miƙa masa ya bata yarinyar,   ba iya mamaki ba hadda tsoro saida ya bayyana akan fuskar Afrah, sakamakon ganin fuskar yarinyar ɗago kanta tayi ta kalleshi da sauri.

Kamar yasan me take tunani,  murmushi yayi mata haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗanta.   “Kada kidamu, Allah ne yayi ikonsa, Allah ne yadubeni yayimini rahama,  sannan kuma ko da ace kowa zaiyi mamakin kamannin yarinyar ni bazanyi ba, saboda wacce take kama da ita, jinin jikinane, sannan kuma Allah yana da ikon yin komai”

Ajiyar zuciya kawai Afrah ta sauƙe haɗe da kafe yarinyar nata da ido, tabbas da badan taji ƙauna irinta uwa da ƴa akan yarinyarba, to tabbas da tace ba itace ta haifi yarinyar ba, Zahrah ce, shine aka sanja mata, aka ɗauki nata aka kaita wani gun, itakuma aka kawo mata wannar, a matsayin ƴarta. Rungume ƴar tata tayi, tanajin ƙaunarta aranta.


Suna komawa gida Zaid yayiwa Afrah kyautar zuƙeƙiyar mota, tare da kuɗi Naira Million 3 duk na murnan ta haifa masa baby ne,  washe gari kuwa suka tarkato suka dawo Nigeria, abisa takurawan Mom ɗinsa. amma da anyi suna yace  zasu koma.  Aranan da aka haifa masa Zahrah aranan ya mallaka mata babban kamfaninsa na ƙera takalma, dake Italy, aranan kuma akasanjawa kamfanin suna zuwa sunan yarinyar, saɓanin da dayake sunan Zaid.

Tunda aka haifi Zahrah Zaid baibari kowa ya ɗauketa ba, inbanda uwarta, nan ma nono kaɗai take bata,  idan yaɗauketa yashiga ɗakinsa da ita, kulle ƙofar yake da key gudun kada wani ya damesa, komai na duniya shiyake mata, wani irin so da ƙaunar yarinyar yake ji, wanda baitaɓa jin irin saba, akullum kallon Zahrah kawai yakeyiwa yarinyar. Irin soyayyar dayake yiwa yarinyar shike tsorita kowa.

Ranan suna kamar yanda ya alƙawartawa kansa cewa idan ya haifi ƴa mace sunan Zahrah zaisawa yarinyar,  hakance takasance domin kuwa sunan nata yasaka, wato FATIMA ZAHRAH, koda Afrah taji sunan da ƴartata taci sai kawai tayi murmushi,  ko kaɗan batayi fushi da faruwar hakan ba, saboda tasan albarkacin Zahrah itama zata samu soyayya ta musamman daga wajen Zaid ɗin, haka kuma albarkacin Zahrah ƴarta itama zata samu gagarumar soyayya daga wajen ubanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button