SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Nairori sunyi kuka a wannan rana, sosai Zaid yayi ɓarin kuɗi tundaga randa aka haifeta kawo yau dayake suna, dukiya kawai yake ɓararwa, tun abun nabawa Mom ɗinsa da Afrah mamaki, har suka daina mamaki, saboda zuwa yanzu sunsan soyayyar da Zaid keyiwa ƴarsa Zahrah ta wuce gaban kwatance, harta bacci akan ƙirjinsa takeyi.
(Sai haƙuri idan kunga typing error, Yau banyi editing ba, wai ina kukene masoyan Zaid, kwata kwata naga alama bakwa farinciki, ace matar Zaid ɗinku nada ciki, amma ku kasa nuna farincikinku, ashe soyayyar takuma, batakai zuci ba, haka team Doctor ma, kuma ashe soyayyar taku ta bogece, tunda anmasa haihuwa ko barka bakuje ba…..)
✅OTE ME ON WATTPAD
@fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
WATTPAD
@fatymasardauna
Godiya ta Musamman Agareku HASSAN ATK and HUSSAINI 80k haƙiƙa kuɗin kun cancanci babban yabo, ako da yaushe akullum kuma ina yaba ƙoƙarinku, Allah Yabiya muku baƙatunku na alkhairi. Dani da sauran marubuta muna godiya sosai agareku
NOTE Nasan daga fara book ɗinnan kawo yanzu na ɓata ran wasunku da yawa, amma inaso kusan cewa sam bahaka naso ba, wannan labarin me suna SHU’UMIN NAMIJI ƙirƙiransa nayi da kaina, ba wani ko wata bane suka bani labari ko shawaran nayi, sannan kuma inaso yawancinmu musan cewa yarda da ƙaddara yana daga cikin imani, balallaine kasamu abunda kakeso alokacin da kake soba, haka kuma balallaine akullum kazamo me nasara ba, haƙiƙa Nasara wani babban jigone da kowa keson samu acikin rayuwarsa, haka kuma rashin nasara ma wani jigo ne da ke sawa mutum ke gane kuskurensa awasu lokutan, idan da’ace komai muka nema zamu samu, to tabbas da ayanzu dayawanmu munshagala da bautar ALLAH Hakan kuma sam ba dai dai bane, arayuwa akwai abu biyu NASARA da kuma FAƊUWA, balallaine kazamo me sa’a ba ako da yaushe, dayawanku suna jin haushin abun da nayi, na hanawa Zaid auren Zahrah, inaso ku fahimceni, banhana Zaid auren Zahrah da gangan ba, ko wai don son zuciyata ba, a’a, inaso kufahimci cewa rashin Zahrah acikin rayuwarsa shine mafarin shiriyarsa, koda a gaskene ba wai a novels ba, idan kanemi abu baka samuba, kada kazargi wani abu, kada kuma kaga kamar ALLAH Baya sonka ne, ko kaɗan bahaka abun yake ba, bai zama lallai abun da kakeso yazamanto alkhairi agareka ba, haka kuma wani lokaci Allah Yakan jinkirta baka abun da kakeso koda kuwa abun alkhairi ne a gareka, kada kayi fushi domin hakan ma wata JARABAWA ce agareka, ALLAH’n daya haliccemu yafi kowa sonmu, shi ke bamu, shi kuma ke hanamu, kada ki/ka sa damuwa acikin zuciyarka, wai don waninka yasamu kai baka samu ba, kaima watarana zaka samu Insha Allah, sannan kowa aduniya baya wuce rabonsa, haka Idan ALLAH Maɗaukakin Sarki ya tsara abu, to babu wanda ya isa ya sauya, natsinci kainane kawai da fara typing ɗin wannan labarin batare da nayi tunanin komai ba, hakanan nafara rubutashi, cikin ikon Allah kuma yabani sa’a, kuka karɓeshi hanu bibbiyu, haƙiƙa labarin nan nice nake rubutasa, amma kuma bani ke da ikon abun da zai faru acikinsa ba ALLAH Ne, komai da ɗan Adam zaiyi acikin duniyarnan bashi keda ikon yinsaba ALLAH Ne kawai ke bashi dama, to haka ALLAH Yatsara cewa Zahrah ba matar Zaid bace, babu kuma wanda ya isa ya bawa Zaid ita sai ALLAH….. Kuyi haƙuri masoyana ina rubuta muku labarinne aduk yanda yazo kaina, nasan dayawa kunji ba daɗi, saboda bakwason Doctor, sai dai kuma babu yanda nidaku zamuyi dole sai haƙuri, wasu har yanzu suna ran cewa, Zahrah zata koma ga Zaid, sai dai ina mai baku haƙuri domin awannan labarin Zaid ba zai taɓa auren Zahrah ba, haka ƙaddaransa take, kuma duk musulmi yanada kyau ya yarda da ƙaddaransa walau mai kyau ko marar kyau.
CHAPTER 117
Two years Later!
Acikin shekaru biyunnan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa hadda haihuwan Husnah, da kuma ƙarin girman da akayiwa Doctor Sadeeq a wajen aiki, Zahrah kuwa tazama lecturer acikin jami’ar da tayi karatu. Abubuwa dayawa sun faru acikin waƴannan shekarun.
Tsaye take agaban wani babban table tana haɗa wasu takardu dake gabanta, ajikinta sanye take da Abaya gown, maroon colour, wanda jikinsa yaji adon duwatsu da kuma flowers masu kyau, yayinda Abaya Vail ɗin dake yafe saman kanta, ya sauƙo har zuwa ƙirjinta, babu wani kwalliya akan fuskarta, lipstick ne kawai sai kuma kwallin data sanya acikin ɗara ɗaran idanunta, sosai taƙara kyau, cika da kuma wayewa, duk da cewa a ƴan shekaru biyun da suka wuce itaɗin ba baya bace wajen kyau, amma ayanzu komai nata yaƙara ninkuwa akan nada, yanzu tana amsa sunanta na cikakkiyar mace. Kallonta ta maida kan agogon dake ɗaure akan tsintsiyar hanunta. “4:30 pm” ta faɗa tana ɗan waro idanunta, da sauri tacigaba da tattare takardun, wasu tasa acikin jakarta, wasu kuwa ta sanyasu acikin wata drawer dake cikin office ɗin. Wayarta da jakarta ta ɗauka, kana ta nufi hanyar fita daga office ɗin.
Motarta ƙiran Corolla LE tashiga haɗe da bata wuta, ta fice acikin jami’an.. Bata wani jima sosaiba ta isa sabon gidansu wanda suka koma babu jimawa.
Da sallama ɗauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon, babu kowa afalon, sai TV Plasma ɗinsu dake ta aiki shikaɗai. Direct wani ɗaki dake cikin falon ta nufa, tsayawa tayi ajikin ƙofar ɗakin tana sakin murmushi, idanunta nakan wani yaro da shekarunsa na duniya bazasu wuce uku ba, ya nata ƙiriniyansa shi kaɗai, yaron kyakkyawane sosai, gashin kansa kuwa kamar na larabawa. Cikin sanɗa tashiga takawa harta ƙarasa wajen dayake zaune, murya a hankali tace.
“Babyy!” Jin muryar mahaifiyarsa acikin kunnuwansa yasashi juyowa da sauri, yana ganinta, ya tafi ya faɗa jikinta, yana dariya, itama dariyan tayi haɗe da manna masa kiss akan bakinsa, cike da kulawa haɗi da ƙaunarsa.
“Aunty Sannu da dawowa” cewar Haulat me yi mata rainon yaron, idan zata aiki.
“Yauwa Haulat sannu da gida” Zahrah ta amsa mata fuska a sake.
Ɗaukan yaronnata tayi suka fice daga ɗakin, direct sama ta haura inda anan bedroom ɗinta yake.
Aje yaron nata tayi akan gado haɗe da durƙusawa agabansa, chocolate irin marar zaƙi sosai ɗinnan ta ciro ajakarta, kana ta ɓare ta basa a hanunsa, da murna Asad ya karɓi Chocolate ɗin, matso da fuskarsa yayi daf da tata, kiss yayi mata akan kumatunta haɗe da cewa “Thank you Mummy!” yayi maganar ne cikin muryarsa dake ɗauke da tsananin yarinta.
Murmushi tayi kana taɗanja kumatunsa, miƙewa tayi ta wuce cikin bathroom acan ta cire kayan jikinta haɗe da sakarwa kanta shower.
Koda ta fito sama sama ta shafa mai domin yanayin garin ana ɗan busa zafi, wani dogon skin tight baƙi ta sanya, wanda yayi matuƙar bayyana surar jikinta, bama kamar hips ɗinta da suka sake cika, wata riga mai net tasanya, irin fitted ɗinnan, sosai rigan tayi mata kyau, ƙirjinta ne kawai yazamana a rufe, amma gaba ɗaya jikinta daga cikinta zuwa bayanta a bayyane suke, haka tsarin rigar yake.