SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Yanayin da suka samu kansu aciki, yakasance me daɗi agaresu, gaba ɗaya daren sun ƙare shi ne cikin soyayya, yayinda Zahrah keta zuba masa shagwaɓa shikuma ya dage sai lallaɓata yake, koda sau ɗayane bayason abun dazai ɓata ranta. Gaba ɗaya yagama shagwaɓata, yamai da ita saikace wata ƴar 7 year. Yanzuma shagwaɓan tagama zuba masa, tana kwance luf acikin ƙirjinsa, yayinda shikuma ya kafeta da idanunsa, dake ɗauke da mayen sonta. Kissing ɗinta yayi akan goshinta, haɗe da maida duka hannayensa cikin ƙirjinta, har yau jinta yake kamar sabuwar budurwa, koda yaushe ƙara shiga zuciyarsa take, sannan babu wani abu na jikinta daya sauya daga mai kyau zuwa marar kyau, breast ɗinta har yau sunanan a yanda suke babu wani abu daya samesu, hakan nema yasa ako da yaushe yake nanuƙe mata, ya murzata son ransa, atunaninsa bacci take saboda haka yayi ƙasa da kansa zuwa ƙirjinta, wani numfashi ta sauƙe alokacin da taji hucin numfashinsa, na sauƙa akan ƙirjinta ahankali, dama baccinta baiyi nisa ba, duka hannayenta ta cusa acikin gashin kansa, tana yamutsawa slowly, ahaka har bacci ya ɗaukesu dukansu..
(Nima bacci nakeji, kuyi haƙuri typing ɗin dare nayi, yanzu nagama kuma dare yayi sosai, saboda haka da safe idan Allah Yakaimu zan sake muku shi. Please kubani Vote sosai a wannan page ɗin, Inason wannan page ɗin, da wanda zanyi gaba sufi kowanni page na baya yawan vote, next page na Zaidun mune.)
✅OTE ME ON WATTPAD
@fatymasardauna
Love
Romance
SON SO @ my wattpadians.
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother KHABIER
????Kainuwa Writers Association
WATTPAD
@fatymasardauna
Godiya ta musamman agareka NAZEEFI YAREEMA (N YAREEMA) wannan fejin gaba ɗayansa kyautane agareka
Godiya mai tarin yawa ga duk wani ko wata, dake mini forwading novels ɗina, haƙiƙa kuna ƙaramin ƙarfin guiwa, kuma inajin daɗin hakan sosai, Allah Yabarmu tare
Bazan taɓa mantawa dakuba my lovely fans, haƙiƙa kuma kuntaka rawar gani sosai wajen sambaɗomini comment, ina alfahari daku aduk inda kuke masoyana, Allah yabar ƙauna maitarin yawa a tsakaninmu Ameen
Da bazarku nake taka rawa my Wattpadians, SON SO tare da SON ƘAUNA nakeyi muku, Inasonku irin sosai ɗinnan
CHAPTER 118
(END! END!! END!!!)
Rayuwa tana tafiya ne da gudu gudu batare da wani mai rai ya ankara da hakan ba, akullum kwanan dunia shekarunmu ƙara ƙarewa suke, sannan ƙara girma muke, sake kusantar mutuwa muke. Daga kwana ɗaya anzarce kwanaki daga kwanaki anwuce satuttuka daga satuttuka anwuce watanni daga watanni anɗarawa shekaru. Haka yake ako da yaushe, acikin waƴannan kwanaki da shekarun kuma abubuwa ne masu yawa suke faruwa suke kuma shuɗewa, wani yasamu cigaba wani kuwa yasamu naƙasu, wani ransa yayi baƙi wani kuwa ransa yayi fari ƙal. To hakance takasance acikin labarin ZAID da ZAHRAH, shekaru sunja rayuwa ta haɓaka, shekaru sama da biyar kenan yanzu, har lau kuma rayuwa suke cike da farinciki….
“MY SOUL! MY SOUL!! MY SOUL!!!” muryarsa daketa kwaɗa ƙiran sunan MY SOUL ta ƙaraɗe ilahirin farfajiyan gidan, tundaga cikin katafaren falonsa, keta kwaɗa ƙiran har ya kawo compound ɗin gidan.
Sanye yake da wando track suit sai kuma wata farar t-shirt ƙafarsa sanye suke cikin wani takalmi mai igiyoyi. Tsayawa yayi haɗe da sanya hannayensa akan ƙugunsa yana fesar da numfashi, yayinda yaketa baza idanunsa, ko zai hango wacce yake nema. Babu wani abu daya sauya ajikinsa, sai ma kyau da hasken fata daya ƙara, ga wani haɗaɗɗen ƙasumba daya daɗa ƙawata kyakkyawar fuskarsa, lallai shiɗin namiji ne cikekke, wanda zai ɗauki hankalin duk wata mace data gansa, ya haɗu sosai da sosai, duk da cewa shekarunsa sun ƙaru akan nada, amma duk da haka yana nan ayanda yake, kyawunsa da kwarjininsa suna nan, haryanzu shiɗin mutum ne mai tsananin son gayu, sam bayason ƙazanta, komai nasa me ajine. ZAID kenan namijin dayazamo abun kwatance acikin sauran mazaje, namijin daya iya jure dakon soyayya me tsananin zafi, namijin daya zamanto sadauki, akan soyayya.
Sake gyara tsayuwarsa yayi, haɗe da ƙara furta ƙiran sunan
“MY SOUL”
Da gudun gaske wata kyakkyar yarinya wacce bazata wuce 6 year ba ta ƙaraso tsalle ɗaya tayi ta haye bayanshi, lumshe idanunsa yayi, alokacin dayaji an ɗale kan bayansa, yasan babu wani ko wata da zaiyi masa wannan aikin idan ba MY SOUL ɗinsa ba. Hanunsa yasanya ya jawota daga bayansa, zamewa yayi akan guiwowinsa haɗe da ɗaura duka hannayensa akan kafaɗunta.
“Maƙoshina saura kaɗan yafashe My Soul duk kuma akanki ne, kinaji inata ƙiranki shine kikaƙi ki amsa ko?” tamkar wani ƙaramin yaro shagwaɓaɓɓe haka ya faɗi maganar.
Dariya fara kyakkyawan yarinyar da yanayin fuskarsu ke shige da tata tayi, haɗe da sanya hanunta akan dogon hancinsa.
“I’am Sorry My Papa luv, ina cikin garden ne, kuma na amsa amma bakaji ba” yarinyar tafaɗa tana ɗan juya idanunta.
Murmushinsa mai kyau yayi mata haɗe da jawota jikinsa ya rungume.
“Bazaki daina juya idanunki idan kina magana ba ko?” yatambayeta yana me shafa bayanta ahankali.
“Papa luv banice fa nakeyin hakan da gangan ba, nima banasanin najuya idanuna idan ina magana!” tafaɗi haka a shagwaɓe hartana ɗan buga ƙafafunta a ƙasa.
Lumshe idanunsa kawai yayi yana maijin ƙarin ƙaunar ƴartasa na ratsa jini da tsokan sa, sosai yanayinta ke kama dana Zahrah babba, haka kuma ɗabi’ar Zahrah ne wani lokaci idan tana magana takan juya idanunta, to itama wannan haka ta keyi, sau da dama idan tana abu, kallon real Zahrah kawai yakeyi mata, domin kuwa yanzu da ta ƙara girma kamanninta da Zahrah sai ya sa ke fitowa, baisan wani irin soyayya yakeyiwa ZAHRAH ƴarsa ba, gaba ɗaya soyayyan da yayiwa Zahrah itace ta dawo kan yarinyar, wani irin so yake yi mata da baida misali, jinsonta yake ako ina na jikinsa, Zahrah ƴarsa itace rayuwarsa, itace Hasken sa, itace madubinsa, wacce idan ya duba ransa keyin sanyi, samunta yafiye masa komai aduniya, samunta wani alkhairi da ginshiƙi ne acikin rayuwarsa, domin kuwa tunda yasameta, arzikinsa suka yalwata akan nada, shikansa ayanzu baisan iya adadin dukiyarsa ba, itakanta yarinyar kamfanoni masu tarin yawa ya buɗe mata, sosai yake samun alkhairi adalilinta.
“Papa Luv!” yarinyar ta ƙirasa murya a sanyaye.
Buɗe idanunsa yayi ahankali haɗe da sauƙesu akan babyn ta sa “Na’am My Soul” ya amsa mata.
Ya mutse fuska tayi haɗe da cewa “Yunwa nakeji Papa Luv banyi breakfast ba”
Waro kyawawan idanunsa yayi haɗe da miƙewa tsaye ya sungumeta suka nufi inda zai sadasu da babban falon gidan.