NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana tsaye agaban dining area tana nunawa hause girl yanda zata shirya musu dining ɗin,  tasha adonta cikin wani jan lace me kyau da burgewa, taƙara cika ta zama babbar mace, dagani kai kasan tana murza naira son ranta, domin wani haske ta ƙara tayi fat da ita.     Shigowarsu cikin falon suna dariya yasanya ta maida hankalinsu gareta, batasan wannan wace irin soyayya bace ke tsakanin Zahrah da Babanta Zaid, soyyace irin ta bugawa a jarida.

Tana tsaye tana kallonsu suka ƙaraso dining area’n kujera yaja ya zauna akai kana ya ɗaura Zahrah akan kujeran dake gefensa na dama, dama kuma haka suke zama koda yaushe.

Murmushi Afrah tayi haɗe da cewa “Nashiga ɗakinka banganka ba ae, sainayi tunanin kana wajen yin gym, ashe ma kuna tare da Zahrah”

Murmushi kawai yayi haɗe da sanya hanu ya shafi kan Zahrah, baitankawa Afrah ba saima duban Zahrah da yayi cike da so yace “Me zan zuba miki?”

“Duk abunda zakaci Babana nima shi zanci!” Zahrah tafaɗi haka tana kashe masa idanunta ɗaya.

Dariya suka sanya atare haɗe da bata hanunsa suka tafa,  abinci yasoma zuba musu da kansa, acikin plate ɗaya, dama kuma a yanzu baya taɓa cin abinci saida Zahrah, zaiƙi ci da kowa amma zaici da ita, kujera Afrah taja ta zauna itama, haɗe da soma yin serving ɗin kanta, don ta lura babu wani wanda yake ta ita, daga Zaid ɗin har Zahrah, su dama kansu kawai suka sani. 

Shida kansa yaciyar da ƴartasa, itama haka ta dinga basa abincin abaki har ya ƙoshi,   sama sama suke hira da Afrah, nan ma itace take jansu da hira, amma daba haka ba bazasu kulata ba, ita har mamakinsu ma take, Zahrah sam bata damu da ita ba, kamar ba itace ta haifeta ba, zancenta baya wuce mahaifinta dakuma Momyn Friend ɗinta, wanda suke makaranta ɗaya dashi.

Tana gama goge bakinta da tissue ta kalli Papa Luv ɗinnata ashagwaɓe tace.    “Please Papa luv yau muje shan ice cream mana!”

“My Soul yau inada aiki, mubari sai gobe mana, kinga fa next week zamu koma U.S.A, akwai abubuwan danakeso nayi kuma kafun mu koma” yafaɗi haka bayan ya aje kofin tea ɗin dake riƙe ahanunsa.

Sake shagwaɓewa tare da narke fuskarta tayi, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa
“Ae Dan Allah Nace Papa Luv, inaso naje ne!”

“Shikenan zo muje na shiryaki” yafaɗi haka yana mai miƙo mata hanunsa.

Tsalle ta doka haɗe da faɗawa jikinsa ta rungumesa, cike da farinciki ta kai masa sunbata akan ƙuncinsa. 

“Thank You Papa Luv”

Ɗagata yayi caɗak akan kafaɗunsa haɗe da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan table, direct suka wuce ɓangarensa. 

Kai kawai Afrah ta girgiza haɗe da cigaba da cin abincinta, sam abunsu baya damunta, tasaba da hakan, koda yaushe haka suke, kamar tip da taya basa rabuwa.

Shida kansa yayi mata wanka yashiryata cikin wasu riga da wando na jeans masu matuƙar kyaun gaske, naɗe mata dogon gashinta yayi a tsakiyar kanta, da wani babban ribbon,  lokaci ɗaya kyawunta da tsananin kamaninta da Zahrah suka sake bayyana, shima wanka yayi kana ya shirya kansa, cikin wasu riga da wando masu kyaun gaske,  sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake, Little Zahrah dakanta saida tayaba kyawun da Papa Luv ɗinta yayi.  

Yana riƙe da hanunta suka fito harzuwa falo, kallonsa ya maida ga Afrah wacce ta mato akan kallonsa.

“My Wife bazaki zo kirakamu bane?” ya tambaya.

Murmushi kawai tayi haɗe da lumshe idanunta, akasalance tace “Kuje kawai Dear nikam inanan, amma ku tahomin da nawa ice cream ɗin”

Hanu Zahrah ta ɗaga mata alaman bye bye kana suka fice daga cikin falon.  

Barinta yayi awajen sayan kayan maƙulashe irinsu chocolate da sauransu shikuma ya nufi wajen turaruka.    Tana tsaye ta ƙurawa wani babban ledan chocolate dake can sama idanu, so take ta ɗaukoshi ta sanya acikin kayanta amma kuma wane ita, ya ɗarawa tsayinta,  jitayi anrufe mata idanu a hankali,   a iya saninta mutum ɗayane keyi mata hakan,  saboda haka yanzuma tasan cewa shiɗinne, dariyan farinciki tasaka haɗe da cewa “ASAD!” 

Dariya yayi haɗe da sake mata fuska ta juyo zuwa garesa, kyakkyawan yarone wanda bazai wuce 7to8 year ba, yarone fari tas dashi tamkar ajinsin larabawa yafito,     tsallen murna Zahrah tasanya haɗe da rungumesa, shima rungumeta yayi cike da jin daɗin ganin ƙawartasa wacce rabonsa da ita yau tsawon sati uku kenan, tun da aka basu hutun makaranta rabonsa da ita..

Cike da ɗokin ganinsa Zahrah tace. “Laaa Asad dama zanganka anan? kaida waye kukazo? nidai nida Papa Luv ɗina mukazo, aibansan zamu sameka anan ba da munzo tunda wuri”

Hanu yasanya ya ɗan murɗe bakinta cikin halayyarsu ta yara yace “Baki gajiyawa da Surutu Soul ina Papan naki?”  yaƙare maganar yana me baza idanunsa.

“Asad me kakeyi anan, bacemin kayi chocolate zaka ɗauka kazo ba?”  

Daga Asad har Zahrah atare suka juya suna kallon mai maganar.     Kyakkyawar mace wacce ta amsa sunanta mace mai aji da kamala, sanye take da abaya gown black colour ta yane jikinta da mayafin abayar, komai nata na burgewa ne, kallo ɗaya zaka mata, kakuma son sakewa domin ba irin ƙananan matannan bane, duk da cewa bata da wani jiki, haka kuma bata wani sanja ba, har yanzu  tana nan da kyawunta mai fusgar hankali.

“Itace Mamanka?” little Zahrah tafaɗi haka ƙasa ƙasa tana kallon Asad.

Kai Asad ya kaɗa mata alamar “Eh” 

Da gudunta ta ƙarasa wajen Momyn Asad ta rungumeta,  cikin surutunta daya zame mata sabo tace.
“Oyoyo Mom Asad, dama inataso mu haɗu dake, amma bakya zuwa school ɗinmu, Dad ɗin Asad ne kawai yake zuwa,  ni da Asad abokaine sosai, kuma dan Allah kudawo U.S.A kunji, muma kunga can zamu koma” tunda little Zahrah tafara zuba bata tsagaitaba sai yanzu.

Hakanan Zahrah taji yarinyar ta burgeta, durƙusawa tayi agaban yarinyar haɗe da sanya hanu ta shafa fuskarta, hakanan taji bugun zuciyarta ya ƙaru, “Idanunta ne ke mata gizo kokuwa dagaske kamanninta take hangowa akan fuskar yarinyar?” tambayar da tayiwa kanta kenan, cike da son sanin amsa.

Murmushin da Little Zahrah tayiwa Mom Asad ne yayi sanadiyar kusan rugujewar zuciyarta.    “ZAID” tafurta sunan acikin maƙoshinta da kuma kan laɓɓanta, sai dai kuma amon sauti baifito ba.

“My Soul”

Taji wata murya dabazata taɓa mantawa da ita ba tafaɗa.

Dagudu Little Zahrah takamo hanun Papa Luv ɗinta dake tsaye.

“Yauwa Papa zokaga Momyn Friend ɗina Asad, wacce nafaɗamaka tana da kirki, tana bawa Asad abun daɗi, shikuma yana bani.” 

Idanunsa ya sauƙe akan bayan wata mace dake durƙushe a ƙasa tabasa baya,   cigaba da jansa little Zahrah tayi harzuwa inda Mom Asad ke durƙushe amma bata ɗago fuskarta ba.

“Momyn Asad, ga Papa Luv ɗina nima, tare dashi mukazo” little Zahrah tafaɗa cike da kauɗi.

Ahankali ta ɗago manya manyan idanunta ta ta kalli mutumin da Zahrah ke cewa shine Papa Luv ɗinta.

Atare bugun zuciyarsu suka tsananta, take wani irin abu ya tsarga jiki da jijiyoyinsu.

Da ƙyar ta’iya daure zuciyarta ta ƙaƙalo murmushi.

Shima murmushin yayi haɗe da sunkuyar da kansa ƙasa.

Hanun Asad ta kama jiki asaɓule ta juya daniyar barin wajen.

“Asad” taji muryar Zaid yaƙira sunan yaron.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button