SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsayawa sukayi cak amma ita bata juyo garesa ba, takowa yayi har inda suke ya durƙusa haɗe da kamo hanun Asad.
“My dear ya hutu?” yatambayi Asad.
“Lapiya” Asad yabashi amsa yana murmushi.
Kallonta yayi haɗe da cewa “Dama Asad ɗanki ne?”
Kanta kawai ta jinjina masa alamar “Eh” gaba ɗaya ta ƙosa subar wajen shikuma yakama Asad ya riƙe ƙam.
Murmushin dake ƙarawa fuskarsa kyau yayi haɗe da cewa “Fine boy, natayaki murnan samun wannan kyakkyawan yaron, amma kuma saidai inajin tsoron abunda zai faru anan gaba, Asad abokin Zahrah na ne, idan nan gaba yasan nayiwa mahaifiyarsa laifi mai girma yakike tunanin zai ɗauki abun?”
Kanta ta girgiza masa haɗe da ɗanyin murmushi. “Kada kace haka Zaid, abu idan ya wuce yana da kyau amantasa, afuskanci gaba, banafatan Asad yasan abun da ka aikata agareni” ɗan numfasawa tayi tare da kama hanun Asad. “Sauri nake zanwuce gida” kallonta ta mayar ga Little Zahrah da ta ƙura mata idanu tun ɗazu, murmushi Zahrah tayi mata, haɗe da shafa kanta, sosai taji son yarinyar acikin ranta.
“Allah ya albarkaci rayuwarki Rabin raina” Tana faɗan haka taja hanun Asad suka bar wajen.
Saida ta ɓacewa ganinsa kafun yasaki wani murmushi haɗe da cusa duka hannayensa acikin aljihun wandon jeans ɗin dake jikinsa. Little Zahrah ce tataho zuwa garesa haɗe da maƙalewa acikin jikinsa, murya asanyaye tace “Papa dama kasan Mommyn Friend ne?”
Murmushi yakumayi akaro na sau babu adadi, hanunta yakama suma suka bar wajen, batare daya bata amsar tambayar da tayi masa ba.
Tunda suka shiga mota batace da yaronnata ƙalaba, shima baitanka mata ba, domin dama shi hakanan yake ba mutum ne mai son yawan magana ba, yana da miskilanci wani lokaci. Ganin da yayi cewa kamar Momyn nasa na cikin damuwa ne yasanyashi gyara zama haɗe da cewa.
“Momy wani laifi ne Papan Friend yayi miki? naji kamar yace wai bayaso muji ko mu sanine oho”
Harara ta watsa masa, hakan yasashi yin gum da bakinsa, shidama gulmace ke cinsa, da yasani ma da baitambaya ba.
Tana isa gida tasamu Husnah da Areefa matar Asad, sunzo suna jiranta, sam basu sanar da ita zuwansu ba, batayi mamakin ganinsuba kamar yanda tayi mamakin ganin yanda aka sauya mata tsarin falonta, aka mamaye gaba ɗaya falon da decorations masu kyaun gaske, tsayawa tayi tana ƙarewa falon nata kallo.
“Happy Birth Day to you my dear Wife!!!”
muryar Dr.Sadeeq ta karaɗe ilahirin kunnuwanta, kallonta ta maida inda taji muryartasa na fitowa.
Fitowarsa daga ɗaki kenan yasha ado cikin riga da wando na jeans masu matuƙar kyau. Murmushi tasakar masa, gaba ɗaya ita tamanta da cewa yaune birth day ɗinta.
Hanunta yakama suka nufi wani ɗan keɓeɓɓen waje dake cikin falon, sosai aka ƙawata wajen da decoration’s mai kyau, kusan suman tsaye tayi alokacin dataga irin hidiman da mijinnata ya shirya mata, manya manyan cake masu kyau da tsada yasa akayi mata har guda uku, ga kayan ciye ciye dana shaye shaye, tsananin farinciki da ƙaunarsa ne suka mamaye zuciyarta, juyawa garesa tayi ta rungumesa, haɗe da cusa kanta acikin ƙirjinsa tana shaƙan daddaɗan ƙamshin jikinsa.
“Thank you so much my lovely husband!!!” tafaɗa cikin sanyi yayinda ƙaunarsa ke ƙara ratsa zuciyarta.
“Babu godiya atsakaninmu My Wife kina da babban matsayi a wajena, keta musamnan ce, inasonki da duka zuciyata!” Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana ƙara matseta acikin ƙirjinsa.
Kwantar dakanta tasakeyi ajikinsa cike da ƙaunarsa, haƙiƙa tasamu duk wani abu da takeso, farinciki, soyayya, da kuma zaman lafiya, sosai Doctor ke bata kulawa, bayason ɓacin ranta ko kaɗan, yana ƙaunarta har acikin jininsa, itama kuma tana ƙaunar mijinnata sosai, ayanzu yafiye mata kowa da komai, yabata farinciki haka kuma yabawa iyayenta, yamantar dasu komai na ɓacin rai da talauci, ya wadatasu da komai na rayuwa, bata da wani TAURARO sama da shi, shiɗin na musamman ne arayuwarta, koda sau ɗayane bata taɓa yin danasanin kasantuwarsa amatsayin mijinta ba, ko da kowa aduniya zai juya mata baya, tasan banda Mijinta Haskenta Abun Alfaharinta. Rayuwarta tayi mata daɗi akoda yaushe saidai tace ALHAMDULILLAH..
Yana tsaye agaban dressing mirror yayinda little Zahrah ke tsaye agefensa, tana shan chocolate, Afrah ce tashigo cikin ɗakin hanunta ɗauke da kofin coffee wanda take haɗamasa kullum daren duniya.
Miƙo masa kofin coffee ɗin tayi, ya amsa yana murmushi, aje kofin yayi haɗe dasanya hanu ya jawota jikinsa ya rungumeta, bakinsa ya kai dai dai saitin kunnenta, ahankali yace “Inasonki ƴar lukutar matata!”
Dariya Afrah tasanya haɗe da cewa “Nima inasonka ɗan lukutin mijina”
Murmushi kawai yayi haɗe da sanya hanu yashafi kumatunta.
“Nima inasonka Papa na!!” little Zahrah dake tsaye a gefensu tafaɗi haka da ƙarfi.
“SON SO nake miki farincikina, idan babuke acikin rayuwata, to babu wani haske dazan sake gani, Allah yarayamin ke na aurar dake ga miji na gari!!” yafaɗi haka yana dariya, acikin zuciyarsa kuwa, har yau tsananin danasanin yanda halayansa suka kasance a baya yake, yayi danasani sosai, har gobe kuma akan danasani yake, bazai kuma taɓa daina Istigfari ba har ƙarshen rayuwarsa.
Duk da Little Zahrah bata fahimci me maganganunsa ke nufi ba, amma tasan cewa mace da namiji suna aure, domin wancan satin daya wuce ma sunje auren ƙanwar momynta.
Dagudu taƙaraso ta rungumeshi, ƙasa ƙasa tace “Nidai ko zanyi aure bakowa zan auraba sai Friend, aishima yanasona ko Papa?”
Durƙusawa yayi agabanta cike da soyayyarta yace “Yanasonki mana, ai aduniya babu wani wanda zaiƙi me wannan kyakkyawar fuskar, ke ɗin ta musammance My Soul!”
Daɗine yakama Zahrah, sake rungume mahaifinnata tayi, aranta tana ƙara ƙaunar papan nata, domin adunia tasan bayan shi babu wani wanda zaiyi mata irin wannan soyayyar dayakeyi mata a yanzu……
Duka ahali biyun rayuwarsu ta miƙa komai suna yinshine cikin farinciki da jin daɗi, akowacce rana ta duniya ƙara ƙaunar junansu suke, saidai muce MASHA ALLAH.
*Alhamdulillah anan nakawo ƙarshen labarin SHU’UMIN NAMIJI ina fatan zakuyi aiki da abun dayake dai dai aciki, inda nayi kuskure kuma Allah Ubangiji yayafemin, nagode sosai da sosai masoyana, haƙiƙa kunbani haɗin kai nakuma ji daɗin haka Allah Yabar Ƙauna, waƴanda na ɓatawa rai don Allah kuyi haƙuri, balaifina bane, haka labarin yake, haka kuma ƙaddaran ZAID da ZAHRAH yake, babu wanda ya isa sauya ƙaddaransa.
Ku ci gaba da bibiyana Insha ALLAH Zakujini da labarai kala kala wanda ina da tabbacin zasuyi muku daɗi, Ina muku SON ƘAUNA!!! Insha ALLAH Ina zuwa muku da wani sabon labarin wanda zai ɗare ma Shu’umin Namiji, ina kuma da tabbacin cewa zaku ji daɗinsa sosai.
✔️OTE ME ON WATTPAD
@fatymasardauna
8/March/2020
Taku Ako da Yaushe
fatymasardauna