SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Oh Allah wannan yarinyar zata kasheni, lallai randa na kamaki bazan miki da sauƙi ba !!” Zaid yafaɗa a cikin zuciyarsa, shi bakomaine ma yake basa takaici da’ita ba kamar rashin magana da batayi, daga eh sai a’a kawai take cewa shi wallahi haushima take basa…
Ita kuwa Zahrah batasan wainar da Zaid ke toyawa ba, saboda kanta na ƙasa, shikuwa gogan tudun breast ɗin ta kawai yakafe da ido, harwani haɗiye yawu yake, tamkar (bestyna Jikar Hajiya tasamu zazzafan balangu,lol)… Daddaɗan sauti ne yasamo tashi daga cikin wayarsa, da alama ƙira ne yashigo wayar tasa “Baby” shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar ɓaro ɓaro, wani irin dokawa zuciyar Zahrah tayi, domin kuwa taga sunan dake yawo akan screen ɗin wayar tasa… A hankali yaɗauki wayar haɗe da karawa akan kunnensa, tunda ya ɗauki wayar baice ƙalaba saidai murmushi kawai da ya yawaita akan fuskarsa, hakan kuwa ba ƙaramin ƙona zuciyar Zahrah yayi ba, wato dai dama yana da budurwa,, har ya cire wayar akan kunnensa banji yace ƙala ba, “Ina wayar dana baki ?” yayi maganar cikin halin ko inkula, “Tana nan” tabasa amsa a taƙaice domin wani haushi ne ya tokare ma ta maƙoshi,, “Maiyasa bakya amafani da’ita ?” “Babu amfanin hakan ” takuma basa amsa ataƙaice, kallonta yayi haɗe da fashewa da dariya harsai da fararen haƙoransa suka bayyana,, tamkar wani tv haka Zahrah tayi ƙasaƙe tana kallonsa bakaɗan ba yayi kyau da yana dariyan, lalle Zaid ƙarshene wajen kyau,, saida yayi dariya sosai kafun ya tsagaita haɗe da kallonta “Kishi ko Ƴan mata ?” turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tayi haɗe da yi masa hararan wasa, lumshe idanunsa yayi gami da buɗewa alokaci guda, “Soyayyata tayi miki mummunan kamu amma zurfin ciki ya hanaki faɗa, shikenan to ni zantafi sai kificemin a mota ko” yaƙarasa maganar yana mai tamke fuska tamkar bashine ya gama dariya yanzu ba….Hmm Zahrah uwar kuka, take idanunta sukayi rau rau dasu, cikin muryar ta mai sanyin amo tace “Kayi haƙuri !!” kallonta ya kuma yi alokaci na barkatai “Hakan nanufin kin amince kina so na kenan??” A hankali tashiga kaɗa kanta alamar “eh” Kyakkyawan murmushinsa mai sauti yayi haɗe da kashe mata idonsa ɗaya, da sauri tayi ƙasa da kanta, tana ɗan murmushi, tana mai kuma jin wani irin farinciki na ratsa zuciyarta, ko ba komai yanzu ya fahimci cewa akwai soyayyarsa acikin zuciyarta…. Ledan dake bag sit ɗin motar ya ɗauko haɗe da miƙo mata cikin murya mai sanya nutsuwa dakuma nuna tsantsar soyayya yace “wannan kyautane a gareni, sauran kuma special gift na amsar soyayyata da kikayi very soon yana nan zuwa, amma bana fara baki wata kyauta…” ya ƙare maganar yana murmushi. Wani ɗan ƙaramin box ya ɗauko daga cikin wani keɓaɓɓen waje dake cikin motar, box ne mai kyaun gaske wanda aka ƙawata jikinsa da wasu irin furanni masu kyawu da ɗaukar hankali, koda ya buɗe box ɗin wani kyakkyawan zube ne ya bayyana, wanda akayisa da zallan gold, murmushi Zahrah tayi domin kuwa sosai zoben yayi mata kyau, hanunsa yamiƙa mata, alamar ta bashi nata hanun, cike da kunya tamiƙa masa lallausan hanunta, saida Zaid ya sauƙe ajiyar zuciya, lokacin da taushin fatar Zahrah da tasa suka haɗe waje guda,, kama hanunnata yayi da kyau haɗi da ciro zoben yasanya mata cikin yatsarta ta uku, ɗas zobennan yazauna acikin yatsar Zahrah, tamkar angwada hanunnata kafun ayishi, batasan sanda tayi murmushi ba harsaida haƙwaranta suka bayyana, bakomai yasa hakanba, face kyaun da taga zoben yayi mata a hanunta, dama ita mutumce mai tsananin son kayan ado, rashi ne yasanya ta dangana komai nata ga Allah…. “Cire zobennan daga yatsarki dai dai yake da cire sona azuciyarki, please ki tausayamin kada kicire domin ina tsananin sonki My Zahrah ta, ke ɗin ta dabance a wajena, kimin alƙawari bazaki taɓa cire zobennan ahanunki ba, har abada !!” Yanda yayi maganar idan ka kallesa zaka rantse da Allah cewa bashi bane, domin kuwa sam baiyi kama da irin mutanennan da zasuna baran soyayya ba, Wani irin farinciki haɗe da tsananin daɗi, su suka shiga huda zuciyar Zahrah, “Haƙiƙa Allah yayi mata babban zaɓi, har abada bazata taɓa daina mamakin soyayyarsu da Zaid ba, domin kuwa duk da kyawunta wallahi Zaid yakerewa ajinta, tayi imani da cewa Zaid ba’irin mazajennan bane, da ake samunsu saka ka acikin gari, irinsu Zaid sai wacce take da rabo da kuma tsananin sa’a ke samunsu, tabbas itakam tana da sa’a, tana kuma daɗa godemawa Allah ako dayaushe..” “My Zahrah !!” yakatsemata tunaninta tahanyar ƙiran sunanta,, “Nayi maka alƙawari bazan taɓa cire zobennan ahanuna ba, har gaban abada,harsai munhaifi ƴaƴa da jikoki, da shima zan mutu” Zahrah tafaɗa cike da kunya. .. Baki kawai Zaid ya hangame yana kallon Zahrah, bakaɗan ba kyawunta yaƙaru da ta ke magana, ashe haka shugar baby’ntasa take kyau intana magana baisani ba?.. Ɗan numfasawa yayi haɗe da gyara zamansa cike da salon yaudara, yace “Zantafi Dad ɗina yana ƙirana, amma gobe zandawo saboda nasake ganin wannan kyakkyawar Baby’n tawa !!”…. Saurin cusa kanta cikin cinyoyinta tayi tana murmushi, (Allah sarki basaban ba su Zahrah anji kalaman love,lol)… “Inasonki My Zahrah !!” yafaɗa cikin shauƙin ƙauna,, yanzu kam ɗago da kanta tayi haɗe da watsa masa kyawawan idanunta, wani irin zubawa tsikar jikin Zaid yayi domin kuwa wani irin kallo Zahrah keyi masa “Nima Inasonka !!” Zahrah tafaɗa tana mai shagwaɓe fuska, haɗe da karya wuyanta gefe,, har abada bazai taɓa gajiyawa da murmushi ba, domin yanzuma murmushin kawai yayi mata,, cike da nutsuwa ta buɗe murfin motar, bayan ta ɗauki ledan daya tursa sa ta kan saita ɗauka,, wani irin kallo sukamawa junansu, kafun tashige cikin gida,, Zaid yana ganin shigewarta ya saki wata irin mahaukaciyar dariya, hadda riƙe ciki, dariya sosai Zaid yakeyi tamkar wani mahaukaci, bakomai yasa hakanba, face tunowa da kalaman Zahrah dayayi, “Wai ita da shi zasu haifi ƴaƴa hadda jikoki ” Lallai yariyarnan ta haukace… Yakuma fashewa da dariya, saida yayi dariya sosai, kafun ya tsagaita hanunsa yasanya yasoma shafa, kwantaccen sajen dake kan fuskarsa,, ” Very soon zakiga Special gift ɗinki !!” yafaɗa ahankali, kansa yajinjina haɗe da fidda iska tacikin bakinsa, key yayi wa motarsa, haɗi da harbata kan titi, yau ƙal yakejin zuciyarsa domin kuwa yanzu yafara buga game ɗin yana da tabbacin cewa kuma bazaiyi game over ba…..
Zahrah kuwa tanashiga cikin gida da lale marhaban, Inna ta tarbeta, domin tuni a leƙe leƙenta da ta sabayi waje, ta leƙosu cikin mota,, amsar ledan Inna tayi, haɗe da bajewa kan taburma tashiga ciro abubuwan dake cikin ledan, still kayayyakine na kanti masu kyau da tsadar gaske, sai kuma mayukan shafa, dasu powder, hadda su tsadaddun turaruka, gefe kuwa ɗaurin kuɗine ƴan dubu dubu masu yawan gaske,, jiki na rawa Inna ta ɗauka haɗi da kaiwa kan hancinta tashiga shinshinasu, “Um kuɗi masu gidan rana, kuɗi maganin damuwar babba da yaro, kuɗi masu saiwa mutum ƴanci, kuɗi basu zuwa gareka saikana da rabo, ni dai Allah yakashe ya bani !” Inna tafaɗa cike da jindaɗi,, kai kawai Zahrah ta girgiza, har cikin zuciyarta batajin daɗin abun da Inna da Baffa keyi, domin hakan kamar zubar mata da mutumci ne, saboda iyayen ƙwarai basa haka,,, wasu ƴan tsiraru daga cikin kuɗin Inna ta kama hanun Zahrah ta damƙa mata, haɗe da cewa “Saura kifaɗamawa wancan ƙwarnafaffen Baffan naki cewa Zaidu yaron arziki yazo, ni dake ne, tattare kayayyakinnan maza kisasu a ɗakinki, domin ban buƙatarsu, kuɗi ne nawa kuma na samu, saura kwana kaɗan nima nafara sanya lasa lasai, hmmm nimafa saina zama wata babbar ƙwaruwa acikin garin Abuja’nnan, domin kuwa Allah yabani bazan tauyewa kaina haƙƙi ba ehe !!” Inna taƙare maganar tana mai turo ɗaurin ɗankwalin ta gaban goshi,, ita dai Zahrah batace da’ita ƙalaba, saima tattare kayan tayi tanufi ɗakinta…