NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Dariya sosai Abid keyi hadda tsugunnawa ƙasa, sosai labarin da abokinnasa yabasa yasanyashi nishaɗi… Ɗan tsagaitawa da dariyan yayi haɗe da maida kallonsa ga Zaid wanda hanunsa ke ɗauke da glass cup yana sipping alcohol, “Gaskia kai ɗin Shu’umi ne, amma miye next target ɗinka ??” Wani irin murmushi Zaid yayi wanda yafiyinta idan zai gudanar da mugunta, “RAPING ɗinta zanyi (Fyaɗe)” Zaid yafaɗa a taƙaice…..

((???????????? Readers…… ????????????????))

3/November/2019

   *MRS SARDAUNA......*

????????????????????????????????????????

        SHU’UMIN NAMIJI !!

      Written by
Phatymasardauna
     ????Mrs Sardauna????

Dedicated to My Brother Khabier

????Kainuwa Writers Association

      WATTPAD @fatymasardauna

Editing is not allowed????

   
Chapter 19 to 20

Jinjina kai Abid yayi haɗe da kallon Zaid, “maiyasa bazakayi amfani da soyayyar da take yi maka ba wajen biyan buƙatan ka, dole sai kayi raping ɗinta??” Abid ya tambaya, Murmushi Zaid yayi haɗe da sanya haƙoransa ya cije kyawawan lips ɗinsa, batare dayace da Abid ƙalaba, yaci gaba da shan wine ɗinsa,, sarai Abid yafahimci abunda Zaid ɗin ke nufi don haka shima baisake ɗago zancen ba, saima ɗaukar wayarsa da yayi yasoma latsa ta….
Kwance take akan ƴar yaloluwar katifarta, gaba ɗaya hankalinta da tunaninta sunaga tunanin masoyinta Zaid, wayar da Zaid yabata ne tasoma kara alamar shigowar ƙira, hanunta har rawa yake wajen son ɗaukar ƙiran, domin tana da yaƙinin cewa Zaid ɗin tane… “My Zahrah na !!” Muryar Zaid yadoki cikin dodon kunnenta, lumshe idanunta tayi alokaci guda haɗe da buɗesu, sosai taji nishaɗi na ratsa zuciyarta,, “Na’am !!” ta amsa masa in a low voice ɗinta, Zaid dake kwance kan makeken gadon sa,gyara kwanciya yayi haɗe da ɗaura hanunsa kan joy stick ɗinsa, haƙiƙanin gaskia ko muryan Zahrah yaji to fa sai sandar girmansa ta motsa, wani irin muguwar sha’awar Zahrah yakeji, ba dare ba rana, “Bakiyi bacci ba ??” yayi mata tambayar yana mai ƙasa da muryarsa,, saida ta ɗan ja numfashi kafun tace dashi ” Eh” kansa ya jinjina kamar dai tana ganinsa, sake lafewa akan gadon yayi, haɗe da ƙasa da muryarsa sosai yanda yatabbatar da cewa zataji a jikinta, ” Soyayyata ce tahanaki bacci ko !! ?” ya ƙare maganar yana mai rumtse idanunsa,, gaba ɗaya ji tayi tsikar jikinta ya shiga zubawa, take kuma kasala ta lulluɓe mata jiki, shiru tay na ɗan wani lokaci, domin takasa amsa masa tambayarsa, a zuciyarta kuwa mamaki take ga me da yanda Zaid ke sanin duk irin halin da take ciki,,….”My Zahrah !!” yasake ƙiran sunanta,, yanzu kam gaba ɗaya rasa control ɗinta tayi, domin yanda yake ƙiran sunan nata da salo acikinsa,, “Umm” tafaɗa cikin muryar shagwaɓa wacce batasan ma tayi taba,, “Ya Allah !!” Zaid yafaɗa acikin zuciyarsa, domin bakaɗan ba salon shagawaɓan nata yatafi dashi, yana matuƙar son mace shagwaɓaɓɓiya, lallai Zahrah tacika mace hundred percent,, “Naga kamar kinajin bacci, zan barki sai da safe ko Dear ?” yayi hakanne don gano wani irin yanayi take ciki,, ” Ni banjin bacci fa !!” Zahrah tafaɗa still a shagwaɓe, (Like Jikar Hajiya, da Sugar dady’nta,lol ????)

Wani irin munafukin murmushi Zaid yayi domin kuwa yasamu abun da yakeso,, Zahrah kuwa takurewa tayi kan lasheshshiyar katifarta, babu abun da take fitarwa sai numfashi a hankali hankali, hakanan ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi, mai wuyar fassaruwa,, lumshe idanunsa Yayi yana mai sauraran sauƙar numfashinta acikin kunnensa, sosai hakan ke yimasa daɗi, sai da suka kwashe kusan mintuna takwas, a haka kafun Zaid ya sauƙe ajiyar zuciya haɗe da da cewa “Tunanin mekikeyi ?” murmushi mai sauti Zahrah tayi, haɗe da cewa ” nima bansani ba amma dai haddakai a cikin tunanin” ƙasa ƙasa Zaid yayi dariya, batare da taji saba….Sosai ya daure zuciyarsa sukayi hira, kalaman soyayya kawai yayita zuba mata, tun Zahrah na noƙewa har tasaki jiki, saida dare yayi sosai kafun sukayi sallama da juna, bayan ya tursasa ta faɗamasa cewa tana sonsa… Zaid yana aje wayar yasanya hannayensa duka biyu yakama kansa, wani irin baƙon al’amari yakeji a tattare dashi, haushin kansa ma yakeji, ba ɗabi’arsa bane yawan magana, amma sai gashi dolensa ya koya saboda Zahrah,, ƙwayoyin paracetamol ya haɗiya haɗe da ƙorawa da ruwa, domin ɗan maganan dayayi harkansa yafara ciwo…. Zahrah ma dai haka aka kwana a najin feelings, ƴan mata anshiga baƙon yanayi……..

Bayan Sati Biyu….

Wata irin gagarumar shaƙuwa haɗi da soyayya ne, suka shiga tsakanin Zaid da Zahrah, wani irin sabo sukayi naban mamaki, sosai soyayyar Zaid ta faɗa ɗa a cikin zuciyar Zahrah, Zaid yayi matuƙar jajircewa wajen inganta soyayyarsa ga Zahrah, yayi mata babban ɗauri da soyayyarsa, kulawa sosai yake bata, koda yaushe suna cikin waya ba dare ba rana,, kuɗi kuwa sosai yasake mawa su Baffa da Inna, domin shi kuɗi ba matsalar sa bane,, Zahrah kuwa harta gaji da amsar kyaututtukansa, gaba ɗaya yanzu kayan da take sanyawa masu tsadar gaske ne, duk kuma aikin Zaid ne, lokaci ɗaya Zahrah ta sanja, mayuka masu tsada take amfani dasu, jikinta yayi fresh, yayinda a kullum surarta ke ƙara haukatar da Zaid cikin kogin sha’awarta,, zuwa yanzu Zahrah tayi sabon da taɗauki duk wani yarda da amincewarta tabaiwa Zaid, yanzu Zaid shine komai nata, son da take masa na da banne,,

Ƙarfe tara na daren yau, Zaid yaƙira ta a waya,, cike da shagwaɓa kamar yadda tasabar masa taɗauki wayar, “Baby nayi fushi, wanin yau duk baka ƙira ni ba sai yanzu !!” Zahrah tafaɗa tunkan Zaid yayi magana, tana mai tura ɗan ƙaramin bakinta gaba, murmushi Zaid yayi haɗi da sauƙe ajiyar zuciya, cikin muryan kasala, yace “My Zahrah, yau nagaji da yawa, saboda wuni nayi a office, amma kinsan ako da yaushe kini raina, domin bayanda za’ayi mutum yamanta da rayuwarsa !!” murmushin jin daɗi Zahrah tayi haɗe dayin fari da idanunta, tamkar yana ganinta, “naji daɗi dana zama rayuwarka, amma kasan nafi sonka ko ?” murmushin gefen baki Zaid yayi haɗe da cewa “Gobe dukanmu zamu tabbatar da wa yafi son wani tsakaninmu, domin kuwa gobe zanbaki special gift ɗinki, na tabbatar bazaki manta da wannan ranan ba, har gaban abada !!” murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa “Bawani nan kaidai kace hakane don kawai ka kawar da zancen, amma aikasan nafi sonka, Ina tsananin sonka My Zaid, bantaɓa soyayyaba, kai ka koyamin, sai gashi kuma nafika iyawa ” Zahrah taƙare maganar tana mai kashe idanunta ɗaya, tamkar tana gabansa,,, dariya sosai yayi, domin ƙwarai maganar Zahrah tabasa dariya,, “My Zahrah nima inasonki sosai, kikulamin da kanki kinji tawan, banso ki manta dani koda na second ɗaya ne acikin rayuwarki !!” ƙit ya kashe wayan bayan yagama faɗan hakan,, murmushine ya ƙwace ma Zahrah, gaskia tayi dacen masoyi, idan har ta auri Zaid to zata iya cewa, itaɗin ta musammance, tanakuma da babban sa’a acikin rayuwarta…….

Washe gari

SATURDAY….

Yau tunsafe takejin wani irin matsanancin faɗuwar gaba, wanda batasan dalili ba, gashi taƙira wayar Zaid a kashe, sam kashe waya ba al’adar Zaid bane ita tasan haka,, amma sai ta alaƙanta hakan da cewa ko yana baccine,, Zaune take a tsakar gida tayi jigum, ko abun karyawanta ma taƙi ci, gaba ɗaƴa jitake duniyar batai mata daɗi, komai yafice mata a cikin rai, muryar Habibie Zaid ɗinta kawai takeson ji, domin yasabar mata kowacce safiya, suna tare a waya,, Inna dakanta tafuskanci sauyawar Zahrah’n domin komai cikin sanyi takeyinshi,,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button