SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Waike Zahrah lafiyarki kuwa ? tun ɗazu kin yi wani sukuku dake, abincin karyawanki ma gashi can a kicin (kitchine)), ko sawa a bakinki bakiyi ba, mai ke damunki ne wai ??” Inna dake tsaye gefen Zahrah tatambaya,,
“Banjin daɗi ne Inna, tunsafe gabana faɗuwa yake, gani nake tamkar wani abu zai sameni, wallahi Inna tsoro nakeji !!” Zahrah taƙare maganar lokacin da idanunta suka cika da ƙwalla,,
“Tsoro kuma ?, tsoron me kuma Zahrah ? to Allah ya kyauta, inma wankin danace kimin ne bakyaso, ai basai kin min ƙarya ba ” Inna taƙare maganar tana nufar hanyar kicin,,, Zahrah dai batace ƙalaba saima ƙara faɗawa duniyar tunani da tayi…..
11:00 am wayar Zahrah tasoma ruri alamar shigowar ƙira,, har tuntuɓe tayi, agarin zuwa ɗaukar wayar domin a tunaninta Zaid ɗinta ne, yaƙira,, Besty Husnah, shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar,, cikin rashin kuzari ta ɗauki wayar haɗi da karawa akan kunnenta, “Hello, Zahrah, wai ina kikene kinfasan 11:30 am, muna da lecture amma haryanzu baki zoba, kinkumasan dai har text zamuyi yau, please kiyi sauri kada ki makara !!”
Ajiyar zuciya Zahrah tasauƙe haɗe da cewa “Wallahi duk yau banjin daɗi ne ƙawata, amma ganinan zuwa, gabana ke yawan faɗuwa, ba don text ɗinnan bama da bazan zoba gaskia !!” Zahrah tafaɗa cike da damuwa,
“SubahanAllah, faɗuwar gaba kuma Zahrah, to Allah yatsare, kidai riƙe addu’a, sai kin shigo” Husnah tafaɗa cike da kulawa..
Cike da kasala Zahrah ta aje wayar bayan taturamawa Zaid saƙonnin waya (text message’s) kusan guda shida kenan, tatura masa daga safe zuwa yanzu,kan cewa tanemesa wayarsa akashe….
Wanka tayi sharp sharp, mai kawai ta shafa, ajikinta, bata tsaya wani fente fente ba tazura, wata maroon ɗin doguwar riga, wacce daga samanta har ƙasanta, maɓallai ne,, sosai rigan ta amshi jikinta, farin hijabi ta sanya, haɗe da ɗaukar jakar makarantarta, ta rataya akan kafaɗarta,,, sama sama tayi mawa Inna dake zaune atsakar gida tana taunar ƙashin kaza sallama,, tana sanya ƙafarta a ƙofar gida, faɗuwar da gabanta keyi ya tsananta, haka zuciyarta ke bugu da sauri sauri, sunan Allah tashiga ƙira acikin zuciyarta,, a hankali take tafiya tamkar wacce ƙwai yafashe mawa ajiki,, saida tayi tafiya mai nisa tsakaninta da gida, kafun ta ankara da wata baƙar mota jeap, dake binta a baya,, storo ne yakama ta don haka sai ta soma sauri,, da wani irin gudu motar tasha gaban Zahrah,, harsai da ƴaƴan hanjin cikin Zahrah suka kaɗa,, da hanzari wasu ƙattai su biyu suka fito daga cikin motar, ƙoƙarin soma ja da baya Zahrah tayi, amma ina tuni ƙattan nan sun cimmata, ɗaya daga cikinsune yakamota, haɗe da tukui kuyeta waje ɗaya, yayinda ɗayan kuma ya ciro wani farin hankacif (handkerchief) daga cikin aljihunsa ya manna mata akan hancinta,, take numfashinta yaɗauke, ta faɗa jikin wanda ke riƙe da’ita, buɗe murfin motar ɗaƴan yayi suka turata ciki, ba ɓata lokaci suma suka shige, driver ya tashi motar suka cilla kan titi……
Tafiya sukayi mai nisan gaske, tamkar zasubar cikin garin Abuja, still Zahrah na sume batasan inda take ba, suna isa gaban wani makeken gida mai kyau da tsari, gate ɗin gidan ya wangale, suka tura hancin motar ciki,, a wani rumfa dake cikin gidan sukayi parking, ɗaya daga cikin mutanen dasuka ɗauko ta ne, ya ɗago ta a wuyansa, yanufi wata ƙofa wacce ita kaɗaice ƙofa acikin kanfacecen compound ɗin gidan,, kan wani makeken gado, ya wurgata, haɗe da zaro wayarsa ya ɗaura akan kunnensa,, “Oga komai ya kammala !!” wannan ƙaton yafaɗa cikin wata bamagujiyar muryarsa marar daɗin amo,, “Okay” kawai naji yace haɗe da cusa wayartasa cikin aljihu,, fita yayi daga ɗakin haɗe da danna mawa ƙofar ɗakin da Zahrah ke ciki makulli,, yayi ficewarsa……
( ????kuyi haƙuri banmuku long typing ba kaina ke ciwo shiasa…)
*5/November/2019*
*MRS SARDAUNA*
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written by
phatymasardauna
????Mrs Sardauna????
Dedicated To My Brother Khabier….
????Kainuwa Writers Association
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowe????
NOTE: Abu nafarko da nakeso ku fara sani, shine ko wani ɗan adam da irin tasa ƙaddarar da Allah yatsara masa, kowani musulmin ƙwarai anaso ya yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta, da yawanku sun min ca akai, akan kada na bar Zaid ya aikata wa Zahrah fyaɗe, wasun ku sunce hakan bai daceba, wasunku kuwa sunce, saboda ita marainiƴa ce kada hakan yafaru akanta, wasuko cewa sukayi idan haka yafaru labarin ya ɓaci,, hmmm wallahi kuna ban mamaki da sukace wai kada haka tafaru da Zahrah saboda ita marainiya ce, tambayata anan shine, Shi maraya Allah baya sauƙar masa da mummunar ƙaddara ne??, baya yi wuwa, don kina/kana, matsayin maraya ace Allah bazai haɗaka da mummunar ƙaddara ba, kowa aduniya da irin tasa ƙaddarar da Allah yarubuta zata faru akanshi, kuma wallahi babu wanda ya isa ya hana ƙaddarar mutum ta riskesa,matuƙar Allah yatsara hakan, duk da cewa wannan ƙageggen labari ne, bawai da gaske bane, amma yazama dole nayi muku nuni da cewa, ƙaddara tana rayuwa ne ajikin ɗan Adam tamkar yadda jininsa ke gudu, acikin jikinsa, yanda kuma ba’a iya kaucemawa mutuwa, haka ma ƙaddara ba’a iya kauce mata, sai dai fatan Allah yakawo da sauƙi,, mata nawa akai mawa fyaɗe kuma marayu ba uwa ba uba, shi fyaɗe ba wai sai kana da uwa ko uba, ake yi maka shiba, ƙaddara ne da take faɗawa kan kowacce mace, idan har Allah (S.W.A) ya ƙadarta faruwan hakan…. Masu cewa idan Zaid yayi mawa Zahrah fyaɗe labarin yaɓaci, inaso ku saurara kuji, ko wani labari da irin nasa tsari da salon da yake tafiya, saboda haka ni nawa da’irin salon da yake tafiya kenan, saikuyi haƙuri idan ranku ya sosu, nima nawan ran ya sosu, kunga kenan dukan mu sai muyi haƙuri da juna….
Chapter 21 to 22
2:00 pm…..
A hankali Zahrah tasoma buɗe idanunta da sukai mata, matuƙar nauyi, dishi dishi take ganin komai, yayinda ƙafafunta ne kawai ke motsawa ajikinta,, sannu a hankali idanunta suka soma washewa, gaba ɗaya ganinta yadawo, da haɗaɗɗen zanen p.o.p n dake saman ɗakin tafara yin tozali, saurin kulle idanunta tayi, take komai yashiga da wo wa cikin kanta filla filla, a matuƙar firgice ta tashi daga kwancen da take, haɗe da soma bin ɗakin da ta ganta kwance am ciki da kallo,, wani irin ihu ta kurma, haɗe da fashewa da kuka lokaci guda,, da gudu ta nufi wata ƙofa wanda take zaton nanne ƙofar fita daga ɗakin,, da iya ƙarfinta tashiga bubbuga ƙofar ɗakin tana kuka mai tsuma zuciya… “Kutaimakeni dan Allah, kubuɗemin natafi gida dan Allah na roƙeku, mai nayi muku kuka kamani !!?” abun da Zahrah ke faɗa kenan tana kuka,, sosai Zahrah ke dukan ƙofar tana kurma ihun neman agaji, amma ina ko gizau ƙofar batayi ba, bakuma alamar da wani wanda zai kawo mata ɗoƙi, tun Zahrah na bugun ƙofar da duka ƙarfinta, har dai gaba ɗaya ta rasa kuzari,, kuka sosai takeyi, a hankali ta zame jiki ta zauna ajikin ƙofar tana mai ci gaba da ruskar kuka,,,, “Wayyo Allah na, don Allah kuyi haƙuri, kubarni nayi tafiya ta !!” Zahrah tafaɗa cikin da sheshshiyar muryarta, wanda kuka yasa lokaci ɗaya ta daina bada amo mai ƙarfi,, “Wayyo Allah na Zaid kazo kataimakeni !!” Zahrah tafaɗa cikin muryar gajiya da kuka….Zahrah tayi kuka tamkar ranta zai fita, tayi ihun harta gaji, amma babu mai taimakonta, tun muryarta na iya fita haryazamto baya fita, idanunta kuwa tamkar an baɗa mata dakakken barkono haka sukayi jajur dasu, lokaci ɗaya wani irin masifaffen ciwon kai, yarufe ta, take jikinta yaɗauki zafi zau tamkar wuta, takure kanta tayi waje ɗaya, tana mai zubar da hawayen tausayin kanta, “Wayyo inama da Zaid yasan halin da take ciki tabbas tasan da yazo ya taimaketa…Abu kamar wasa zazzafan zazzaɓine ya rufe duk jikinta, a sanadin kukan da tayi…..