SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

(please and please kada ku saƙar min da guiwa don Allah, wallahi idan kuka faɗi bad magana, bazanji daɗin yin next page ba, ko waccenku nasan tasan ƙaddara, idan Zaid baiyi mawa Zahrah fyaɗe ba, labarina bazai tafi a yanda nake so ba, nasan zakuji haushi amma kuyi haƙuri….)
7/October/2019
MRS SARDAUNA
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written by
Phatymasardaun
????Mrs Sardauna????
Dedicated To My Brother Khabier…
????Kainuwa Writers Association
”'{{United we stand and succeed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}}”’
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed ????
Wannan page ɗin gaba ɗayansa kyautane a gareki ƴar uwa rabin jiki, My lovely Sister ZAHRAH (MOM PHADEEL) nagode sosai da kulawa Allah yabar ƙauna, kisani.inasonki sosai tawan, inakuma ji dake, kijima kiyi lasting..
Chapter 23 to 24
A ƙalla Zaid yakai kusan 50 Minute a cikin bathtub ɗin wanka, a sannu sannu yasamu ciwon kannasa ya lafa, duk da cewa bai daina ji ba, amma bakamar ɗazu ba,,,a daddafe yayi wankan tsarki dana soso da sabulu, domin kuwa wata irin muguwar kasala yakeji ajikinsa,, sanye yafito daga shi, sai rigan wanka, wacce ta tsaya iyaka guiwarsa,, kallo ɗaya yayi murmushinsa yayi haɗe da sanya hanunsa ya shafi gefen kumatun ta, ” Me daɗi na !! ” yaƙira sunanta da wata irin murya , idanunsa ɗaya yakashe tamkar dai tana ganinsa, doguwar rigarta dake yashe a ƙasa, ya ɗakko yasanya mata ajikinta, duk dacewa gaba ɗaya doguwar rigar a kece take,, wayarsa yaɗauka haɗe da karawa akan kunnensa, mintuna kaɗan wanda yake ƙira ya amsa wayar, “kuzo ku maidata inda kuka ɗauko ta ” Zaid yafaɗa a taƙaice, haɗi da datse ƙiran, har yakai bakin ƙofar fita daga ɗakin, saikuma ya tsaya cak, dawo da kallonsa yayi zuwa kan fuskar Zahrah,, murmushi yayi, haɗe da murɗa handle ɗin ƙofar yayi ficewarsa,, yana fita farfajiyar gidan, yashige motarsa ƙirar Venza haɗe da bata wuta yabar gidan… Mintuna ƙalilan da tafiyan Zaid, waƴannan mutanen da suka kawo Zahrah, suka kuma da wowa, kamar yanda yashigo da ita awuya, haka yanzuma ya ɗagata a wuyansa yayi waje da’ita, aransa yana matuƙar mamakin yanda jikinta yayi faca faca da jini, tamkar anyanka kaza….
9:50 pm… Dai dai suka ƙaraso cikin unguwar su Zahrah, sai da suka kawo daf da ƙofar gidansu, kafun suka tsaya, buɗe murfin motar sukayi, haɗe da tunkuɗo Zahrah da bata numfashi waje, take ta zube a wajen,, sukuwa banka mawa motarsu wuta sukayi suka ƙara gaba…
“Gaskia Malam nifa hankalina yasoma tashi, haba dan Allah, ace yarinya tun shaɗaya’n rana ta fita, amma har yanzu kusan goman dare bata dawo ba, gaskia duk inda Zahrah tashiga jikina yana bani ba lafiya take ba, domin kuwa sam ba ɗabi’ar Zahrah bace yin dare a waje! “
Ajiyar zuciya Baffa ya sauƙe, domin shima zuwa yanzu abun yafara da munsa, ace tun rana da ta fita haryanzu shiru babu labarinta,,
“Haba Malam kayi shiru, kamata yayi kaje makarantar tasu kaji ko lafiya, amma ka wani tsaya ƙiƙam “
“kinga dan Allah kada kici kani da bala’i, tun ɗazu kintsaya akaina sai faman ɓaɓatu kikeyi, ca nai miki bazanje makarantar tasu induba ba ko me ?, ni banson baƙar jarfa !!” Baffa yaƙare maganar cikin faɗa,,
Gum Inna tayi da bakinta,,domin tasan nasa masifar ta taka nata, inyafara bala’i, sai yakai har gobe bai gama ba…
Miƙewa Baffa yayi daga zaunen dayake haɗe da ficewa daga cikin gidan,,,, kasancewar gari yayi duhu, ga kuma matsalan wutan lantarki da ake fama dashi, kusan koda yaushe ba wuta, yanzun ma dai hakanne domin kuwa gaba ɗaya layinnasu dulum yake babu wani gida mai ɗauke da hasken lantarki,, har Baffa ya gota saikuma yaga tamkar wani ƙaton abune yashe a ƙasa, cike da ɗar ɗar yafito da ƴar ƙaramar wayarsa Nokia, ɗan madannin sama ya danna take hasken tocila (flashlight) ya bayyana,, haska tudun dayagani yayi, aikuwa mutum yagani yashe a ƙasa,, “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un !!” Baffa yafaɗa gabansa na dukan uku uku, sake matsowa yayi don tabbatar mawa idanunsa, mutum ɗinne ko kuwa, wani irin razana haɗe da faɗuwar gaba ne suka dirar mawa Baffa alokaci guda, sakamakon tozali da fuskar Zahrah da yayi, “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un, Allahumma ajirni fil masibati wa’aklifni kairan minha, subahan Allah !!,, Salame Salame !!!” Baffa yashiga kwaɗa ƙira, aikuwa dagudu Inna mai kunnen jiyau, ta bazamo ƙofar gida, domin dai dawuya kaima Inna ƙira ɗaya bata jiba…
“lafiya kuwa Malam kaketa zundumamin ƙira?, ai saika sa na…. Kasa ƙarasa maganar Inna tayi, domin kuwa idanunta ne suka sauƙa kan Zahrah dake kwance magashiyan a cikin turbuɗin ƙasa,, “ƙara Inna ta ƙwanɗara, haɗe da afkawa kan Zahrah tashiga jijjigata, “Zahrah ! Zahrah !! ” Inna tashiga ƙiran sunan Zahrah, cike da firgici,,,, kuka sosai Inna tashiga rerawa tana mai ƙiran sunan Zahrah, amma ina Zahrah batasanma a duniyar da take ba,, Baffa ne yayi ƙarfin halin sa Inna ta cicciɓota sukayi cikin gida da’ita, gudun kada jama’a su taru akansu… Cike da tsoro Inna da Baffa ke kallon busheshshen jinin dake manne a ƙafofinta, “Nashiga uku Malam mai yasameta ne? kagafa taƙi buɗe idonta !” Inna tafaɗa cikin ruɗewa, ” Ina zansani Salame ba dake muka tsintota a ƙofar gida ba, yanzu dai bana kawo ruwa ki zuba mata kozata farfaɗo “
Ruwa Baffa yakawo Inna tashiga zubawa Zahrah akan fuskarta, amma ina aiko alaman motsi Zahrah batayi ba,, ” Mun shiga uku malam, kagafa haryanzu taƙi motsawa !” Inna takuma faɗa, cikin tsoro, “Banaje nataro mai taxi sai muje asibiti !!” Baffa yafaɗa cikin gaggawa domin yatsorita da al’amarin Zahrah’n….
Mintuna ƙalilan Baffa yadawo damai taxi, wata baƙar riga Inna tasanyama Zahrah, haka suka ɗebeta, aka sanyata acikin taxi kaitsaye suka wuce asibitin cikin gari…..
Mai taxi na fakawa Baffa ya arta a guje, yayi cikin asibitin, yanashiga yataradda wasu nurses suna zaune, bawani ɓata lokaci Baffa yasoma kora musu bayani akan cewa yazo da marar lafiya ne,, taɓe baki ɗaya daga cikin nurses ɗin tayi, haɗe da yi mawa Baffa kallon rainin hankali, cike da gadara tace ” Bama karɓan marar lafiya sai anyanki kati ” jiki na rawa Baffa yace ” Kiyi haƙuri bansani bane, nawa ake yankan katin? kuma a ina ake yanka ?” bakinta takuma taɓewa haɗe da cewa ” 1k ne sannan kuma acan wajen ake yanka ” taƙare maganar tana maiyi masa nuni da wani waje,,
“menene kuma 1k yarnan ?” Baffa yatambaya,, cike da shaƙiyanci duka Nurses ɗin suka sanya masa dariya, “Hmm lallaima tsohonnan wato kai bakasan komai ba, amma kaɗauko marar lafiyanka kukazo asibitinnan, Hmm talaka baijira kansa ba, to abun da ake nufi da 1k shine dubu ɗaya ” again nurse ɗin taƙara magana tana yatsine fuska… “To to to shikenan banaje na yanka ” Baffa yafaɗa, cikin hanzari yanufi inda wannan nurse ɗin ta gwada masa, sosai Baffa yajima kafun yasamu ya yanki katin, saboda zalunci ma mai yanka katin dubu ɗaya da ɗari biyar takarɓa a wajensa, babu kuma yanda ya’iya haka yabayar, yana kawo katin yamiƙamawa nurse ɗin, yatsina fuska ta sakeyi haɗe da cewa aje katin a can, zuwa anjima maduba,,,