SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

ZARAH ! ZARAH !! wata mata dake zaune kan tabarma keta kwaɗa gira,, “Na’am” wacce aka ƙira da suna Zarah ta amsa tana mai fitowa daga cikin wani ɗaki,, wata kyakkyawa matashiyar budurwa wacce bazata wuce 20 year ba tabayyana gaban wannan matar da ke aikin ƙwaɗa ƙira, cike da girmamawa tace Inna gani,, “Au dama tunɗazu kinajina iskancine yahanaki amsa ƙirannawa kome ?” matar tafaɗa tana mai gallamawa yarinyar dake duƙe a gabanta harara,, cikin tausasa murya Zarah tace “Kiyi haƙuri Inna wallahi, banjiki bane inacan ciki ina shirin makaranta, yau muna da lecture’n safe banso na makara ” “Uwar Lecture kuke dashi da ubansa, inkinga kinfita agidannan to wallahi kinga mamin aiki nane ” Inna tafaɗi haka tanamai tsakace haƙoranta da tsinken dake riƙe a hanunta,,,, cikin sigar lallami Zahra tace “Dan Allah Inna kiyi haƙuri idan nadawo sainayimiki duk abun dakike so ” “Zaki tashi kisoma aikin dana saki ko kuwa saina mangareki banza mai kama da aljanu ” Inna tafaɗa cikin faɗa , cikin sanyin jiki Zahra tatashi daga gaban Inna…. Wanke Wanke tafarayi sannan tayi sharan tsakar gida dana ɗaki,, saikuma hurawa Innar wuta, koda takammala aikin nata har 9 tayi, sam bataso ace yau tayi latti ba domin kuwa suna da lecture 8:00am, shikenan yauma lecture’n Sir Adam yasake wuceta kamar dai yanda yawuce ta wancan satin….. hijab ɗinta mai launin ruwan ƙasa tasanya, haɗe da saɓa jakarta a ƙafaɗanta, fitowa tayi tasamu Inna nazaune, bakin murhu tana ɗumamen tuwo, “Inna nizan wuce makaranta ” Zahra tafaɗa,, “To uwar ƴan boko saikin dawo, aikin kenan bacas ba as saidai zuwa makaranta, da Mijin aure kika fito dashi, kikayi aure aida nahuta da wannan wahalar taki ” Inna tafaɗa cike da bala’i.. Itadai Zahra batasake ce da’ita ƙalaba, tasakai tafice daga cikin gidan, tana fitowa ƙofar gida, zazzafan hawaye suka gangaro daga cikin idanunta, dasauri tasanya hanu tashare hawayenta, kana tacigaba da tafiyarta………
((Wanene Zaid ? Wacece Zahra ? saigaba zakuji kosu ɗin suwayene, Wace alaƙace ke tsakanin Zaid da Zee ? mata da mijine kokuwa, iskancinsu kawai suke ? kubiyoni don sanin gaskiar al’amari… ))
11/October/2019
*MRS SARDAUNA*
????????????????????????????????????????
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written by*
phatymasardauna
????Mrs Sardauna????
Dedicated To My Lovely Brother Khabeer
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
*WATTPAD*
@fatymasardauna
Editing is not allowed ????
Chapter 3
(sorry a chapter 2 nayi mistake nasa guest house ɗin Zaid na G.R.A, to ba G.R.A zansaba mistake ne, guest house ɗin Zaid na Maitama ne ba G.R.A )
Har takawo bakin titi bata samu abun hawa ba, gashi yau antashi da wani irin zafin rana, duk da cewa taran safe ne amma hakan baihana ranan bayyana zafin taba, tsaye tayi abakin titi tanamai ƙaremawa motoci da mashunan dake wucewa akan titin kallo, har izuwa yanzu mai adaidaita sahu ko ɗaya baizo yagil ma akan titin ba, takusan minti 12 tsaye a wajen kafun tasamu wani mai adaidai ta yaɗauke ta, kaitsaye babban jami’an da take karatu suka nufa…. Kamar koda yaushe abakin titi tace mai adaidaita ya sauƙeta domin dokace ba a shiga jami’an da motar haya, saidai idan motar kanka kokuma machine, nanma saidai in mallakin mutum ne… Ɗalibai ne iri da kala ke gudanar da harkokinsu acikin makaranta, wasu na hira da samari wasu kuwa na karatu, kamar dai yanda kukasan ƴan jami’a keyi,, kaitsaye tanufi gindin wata ƙatuwar bishiya wanda anan ƴan course ɗinsu ke tare, da’alama dai fitowarsu kenan daga lecture…. Da sallama ɗauke a bakinta taƙarasa garesu, bako wanne daga cikinsu bane suka amsa sallaman nata ba sai ƴan tsiraru, wasu ko da kallon banza suka rakata,, musamman ma ƴan matan dake wajen, koka ɗan hakan bai dameta ba domin dai hakan ba sabon abu bane a wajenta, musamman ma idan tayi la’akari cewa ita da su ɗin akwai banbanci, domin dukansu ƴaƴan manya ne itakuwa ƴar talaka ce futuk, shiyasa ma koda wasa bata yunƙurin haɗa kanta dasu,, zama tayi a gefen Aminiyarta Husna… ” Yauma saida kikasakeyin missing lecture, anya kuwa Zahrah wanan exam ɗin da zamuyi baza’a samu matsala ba ?” Husnah tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,,
ajiyar zuciya Zarah ta sauƙe, haɗe da cewa ” Bansan yazan yi ba Husnah wallahi dole ce take sawa nayi latti gashi unguwarmu a kwai ƙarancin abun hawa ” Zahrah ta ƙare maganar daidai lokacin da take ciro wani hand out a jakanta, “shikenan mukoma gefe saina koyar dake abun dana gane, domin ni wallahi lecture ɗin Mr Adam sam bana ganesa ” Husnah tafaɗa tana mai yunƙurin miƙewa tsaye…. Duk da cewa tazo latti amma tafahimci darasin da Husnah takoyar da’ita, tamkar ma tananan akayi…….
Basu suka kammala lectures ɗin dasuke da shiba harsai 5 pm, a gajiye take liƙis uwa uba ga yunwa dake ƙwaƙulan cikinta, rabonta da abinci tun 10 am nan ma Husnah ce tasaya musu snacks da drinks a Cafeteria, ɓatare da ta tsaya wani abu ba tashiga Adai dai ta sahu tayi yo gida…
MAITAMA
Zaid da Zee kuwa ayar su suka sheƙe sosai, domin Zee har kuka saida tayi mawa Zaid, wanda hakan kuma ba baƙon al’amari bane wajensa, domin sau da dama idan yayi sex da Zee tofa saitayi masa kuka, na azaba ko na daɗi wannan ne kuma baisani ba,, tsaye yake agaban dressing mirror dagashi sai towel ɗaure a ƙugunsa, hankalinsa gaba ɗaya yana kan busar da gashinsa da yakeyi da hand dryer, Zee dake kwance akan makeken gadon ɗakin shame shame, kuwa ƙura masa idanu tayi, itakam Allah yasani, Zaid yana matuƙar burgeta, tanajin son gayen har cikin zuciyarta, saidai tasan cewa ko sama da ƙasa zasu haɗe, Zaid bazaitaɓa auren ta ba, saidai tana godemawa Allah ahakan ma daya bata daman raɓansa, domin raɓan Zaid ma sai mai sa’a, kuma sai macen da ta amsa sunanta mace ƴar gayu da aji….
Tsab yagama shiryawa haɗe dayi mawa kansa feshin turare mai daɗin ƙamshi,, Car key ɗinsa ya ɗauka haɗe da wayarsa, hanu yasa acikin aljihun wandonsa, kuɗi ya ciro bandir ɗin ƴan dubu dubu, ya cillamawa Zee akan cinyarta, batare da ya kalleta ba yace ” Kada ki tafi sai kin kimtsamin gado na ” yanakaiwa nan azancensa, yasakai yafice daga cikin ɗakin bakinsa ɗauke da fito,,, a maimakon Zee taji haushin yanda yamata, saima murmushin da tayi haɗe da lumshe munafukan idanunta, afili ta furta cewa “Allah kamallakamin Zaid amatsayin mijina”…..
Tundaga Zauren gidan nasu ta ke jiyo tashin muryan Inna dana Baffa da’alama dai sana’artasu ta kullum sukeyi wato faɗa,, shahada kawai tayi tadoshi cikin gidan, domin dai tasan tana shiga tofa kanta faɗan zai dawo… Aikuwa a rubuce yake tana sawo kai cikin gidan, Inna ta ce “Kekuma uwar gantali saiyanzu aka tashi daga makarantar ?” cike da ladabi Zahrah ta rusuna haɗe da cewa ” Baffa ina wuni “….”Daban wuni ba zaki ganni ? nace daban wuni ba zaki ganni ?? Baffa yakuma faɗa cikin tsawa, kai kawai zarah ta girgiza haɗe da nufar ɗakinta,, kwanciya tayi luf akan ƴar katifanta, zuciyarta cike da tunanin halin rayuwa dakuma yau da kullum….
Koda Zaid yabaro guest house ɗinsa bai zarce ko’ina ba sai wani babban Club ɗin dake cikin garin abuja, makeken Club ne mai kyau da tsaruwar gaske, irin Club ɗin nan ne daba kowa ke zuwanshi ba sai wane da kuma ɗan wane, Club ne na manyan guys, da kuma manyan ƴan mata, kamar ƴaƴan shugaban ƙasa da sauransu, amma idan dai har kai ba wani bane kuma ubanka ba kowa bane to fa baka isa shiga wannan haɗɗɗen Club ɗin ba, Zaid kuw yamaida wannan Club ɗin kamar ɗakin baccinsa, domin kuwa zaiyi wuya ace ya kwana ɗaya baijeba…
Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun da aka ƙawata tsakiyar Club ɗin dasu, yana zama wata ma aikaciyar Club ɗin tanufu inda yake hanunta ɗauke da tire na glass wanda samansa ke ɗauke da glass cup guda biyu, da kuma zungureren tsadaddiyar kwalban giya, kasancewa duk wani ma’aikaci dake cikin hotel ɗin yasan, abun da Zaid ɗin ke sha idan yazo wajen… Duk yanda ma aikaciyar Club ɗin nan ke kwarkwasa Zaid baiko ɗaga idanunsa ya kalleta ba, domin shi baimaga macen dazai kula ba kaf cikin Club ɗin, balle kuma ita banza mai aiki…. Cike da nutsawa Zaid yakafa kansa ya kwankwaɗi giya son ransa, saida yayi tatul tukun yabar cikin club ɗin, bayan yayi waya da Asmee ƴar wani minister dake cikin Naija, cewa tazo ta samesa a guest house ɗinsa……