NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Dan girman Allah ƴarnan kitaimakeni, wallahi ɗiyatace nakawo ko numfashi batayi, bansaniba ma ko tamutu kotana da rai !!” Baffa yafaɗa cike da tashin hankali, ganin suna neman aje katin daya basu,

“What ! bata numfashifa kace ? ” su duka Nurses ɗin suka faɗa cikin ruɗewa, “ƙwarai kuwa ” Baffa yabasu amsa… Ai da hanzari nurses ɗinnan sukayi waje, yayinda wasu sukatafi ɗauko  wannan ɗan gadon da ake ɗaura mutanen da aka kawosu emergency akai,,     akan wannan gadon aka ɗaura Zahrah da hanzari suke turata,don kaita abata taimakon gaggawa…. duk yanda suka so ceto rayuwarta abun yafi ƙarfinsu,   ɗaya daga cikin Nurses ɗinne ta sharce gumin dake kan goshinta,  ɗan nisawa tayi haɗe da kallon ƴan uwanta, cike da gajiya tace ” gaskia inaga bazamu iya aikin nan ba, domin kuwa case ɗin fyaɗe ne, ba kuma hurumin mu bane, dole sai mundangana ga Doctor S.S domin wannan aikin sane ”    “Cab gaskia inajin tsoro mar’uda yanzufa time ɗin shin sane, kinaga yadace mukai masa wannan case ɗin ?, kuma ma idan yasan abun da muka aikata tun farko, wallahi bazamu share ba..”  wacce ke tsaye gefen Mar’uda ta faɗa,, ” gaskia saidai yayi haƙuri Aisha domin kuwa tabbas shiɗinne kaɗai zai iya kamo bakin zaren, banaje naƙirasa ” Mar’uda nakaiwa nan a zancenta tafice daga cikin emergency room ɗin…..

Zaune yake akan tankamemiyar ƙujeran dake cikin haɗaɗɗen office ɗinsa,  kyakkyawan matashin saurayine wanda aƙalla bazai wuce 30 years ba, sanye yake da riga da wando baƙaƙe, yayinda yaɗaura farin suit akai mai matuƙar kyaun gaske,,  riƙe yake da wani file ahanunsa, yana dubawa yayinda yake shan coffee  ahankali, da’alama abu mai mahimmanci yakeyi,     farine shi amma basosai ba, sannan yana da ƙawataccen saje akan fuskarsa, yana da manyan idanu dakuma dogon hanci, wanda suka taimaka wajen bayyana kyawunsa, masha Allah shima dai kyakkyawane na nunawa sa’a….

Knocking ƙofar office ɗinnasa akashi ga yi,   ajiye kofin coffee ɗin nasa yayi, haɗe da yamutsa fuska, cikin wata irin murya yace “yes, come in ”  Mar’uda ce taturo ƙofar tashigo, cike da girmamawa tace ” sorry for disturbing you sir, we have an emergency patient”

” but i have closed for today, inama ƙoƙarin tafiya gidane ” Doctor S.S yafaɗa cikin gajiyawa..

“Sir, the patient has been raped and she is unconscious !!”

” Suban Allah, fyaɗe fa kikace Mar’uda !!”  Doctor S.S ya faɗa cikin kaɗuwa,, kai Mar’uda ta ƙaɗa alamar eh,   miƙewa yayi cikin gaggawa yace  ” Muje “… Doctor S.S na gaba Mar’uda, nabiye dashi haka suka nufi emergency room ɗin,,   yana shiga cikin Emergency room ɗin yaji ƙirjinsa ya buga,   da sauri yaƙarisa kan Zahrah dake kwance tamkar gawa,   take sauran Nurses ɗin nan suka shiga cikin taitayinsu, domin sun san Doctor S.S baya wasa, musamman ma idan akan irin wannan case ɗinne na fyaɗe…  Taimakon gaggawa Doctor S.S yashiga bawa Zahrah,  bayan yasanya Nurses sun haɗa masa kayan aiki,   bakaɗan ba Doctor S.S ya tsorita, ganin irin taɓargazan da akayi mawa Zahrah a ƙasanta, domin sosai wanda yayi mata fyaɗen, ya ɓarkata,, “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un !!” kawai Doctor S.S kefaɗa acikin zuciyarsa, domin kuwa duk wanda yayi mata wannan abun yacika marar imani kuma marar tausayi,   Doctor S.S nayi mata ɗinki amma zuciyarsa ƙuna da tafarfasa takeyi, “Haryaushene za’a ɗauki mataki akan banzayen mazajen da sukeyi mawa yara mata ƙanana fyaɗe ?, har yaushe za’adaina yi mawa mata fyaɗe ?, haryaushene  wasu mazan zasu daina cin mutumcin mata tahanyar yi musu fyaɗe ?,  ako da yaushe yana matuƙar jin ciwo acikin zuciyarsa, aduk sanda yaji cewa anyi mawa mace fyaɗe, tabbas da ace yana da wani babban iko, to da ya ɗauki tsattsauran mataki ga duk wani namiji da yayi mawa mace fƴaɗe” haka dai Doctor S.S yaɗinke Zahrah tsaf, bayan yagama ɗinketa ne, yayi mata treatment ɗin goshinta wanda yake a fashe, aƙalla dai Doctor S.S yakai kusan 1 hour yanayi mawa Zahrah teatment,   allurai yayi mata kala biyu,  saida yakammala yi mata komai kafun yafice daga cikin ɗakin bayan yabawa Nurses umarnin kaita ɗakin hutu, duk dacewa bata farfaɗo ba…   “Suwaye suka kawota ?” Doctor S.S yatambayi Mar’uda fuskarsa babu alamar wasa,,  inda su Baffa da Inna ke zaune Mar’uda tayi masa nuni,,  cike da ɓacin rai Doctor S.S yanufi inda suke…

“Kunkuwa san mekukeyi ? taya zakubanzatar da ɗiyarku, har aimata mummunan fƴaɗe irin wannnan ?, ko kunsan wani irin haɗari ƴarku tashiga, a sanadiyar wannan fyaɗen da akayi mata ?, maiyasa iyaye kuke sakaci da rayuwar ƴaƴayenku mata ne?, shin bakusan cewa ranan gobe, Allah zai tambayeku game da amanarsu daya baku ba ? “.. Doctor S.S yajero musu tambayoyi cikin matsanancin ɓacin rai,, jikin Baffa da Inna ne yayi laƙwas, domin su sam basuma san cewa fƴaɗe akayimawa Zahrah’n ba sai yanzu, take Inna tasoma share ƙwalla hadda shashsheƙar majina,, wani irin kallon tsantsar takaici Doctor S.S  yayi mawa su Baffa haɗe da cewa “Kubiyoni Office ” yanakaiwa nan a zancensa yanufi hanyar office ɗinsa,, haka su Baffa suka rufa masa baya jiki ba ƙwari, domin kuwa dukansu sun kaɗu dajin cewa wai fyaɗe akayimawa Zahrah, to waye ? suka tambayi kansu…  Zama yayi akan kujera gaba ɗaya jin zuciyarsa yake ba daɗi, wani irin masifaffen haushin iyayen yarinyar ma yakeji, da ƙyar ya iya daure zuciyarsa,  yace “Ya akayi abun yafaru ?”   gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa “Wallahi likita bansani ba, nidai natafi wajen sana’ata, dana dawo kuma sai bantarar da Zahrah a gida ba,  shine kuma daga baya nataradda ita yashe a ƙofar gida !” Baffa yaƙare maganar yana matsan ƙwalla,    laɓɓansa ya cije cike da takaici,  domin gaba ɗaya abun ma yalura rashin kula ne yajawo, amma tun da shi ba ɗan sanda bane bai dace yatsare su da tambayoyi ba,   ”  Yanzu dai maganar gaskia ƴarku tana cikin hatsari, tana matuƙar buƙatar taimako, wanda yayi mata fyaɗe yayi mata rauni sosai a gabanta, wanda yaja dole akayi mata ɗinki, amma ba’anan matsalar take ba, ba lallai ƴarku, ta farfaɗo  yau ba, zata iyakaiwa gobe koma fiye da haka, sannan baizama lallai ta dawo cikin hayyacinta ba kodama ta farfaɗo ɗin, saboda ana yawan samun irin waƴannan matsalolin, dayawan mata idan aka musu fyaɗe yakan taɓa musu ƙwaƙwalwa, sai dai ako dayaushe fatanmu shine komai yazo da sauƙi “…. Bakaɗan ba hankalin su Baffa yatashi jin abun da Doctor ke cewa, ya ilahi wani irin iftila’i ne ya faɗo cikin rayuwarsu haka ????……

((Kuyi haƙuri jiya kunjini shiru abubuwane sukaimin yawa, Zee black nagode da kulawa…))

    10/November/2019

     MRS SARDAUNA
????????????????????????????????????????

         SHU’UMIN NAMIJI !!

     Written By
phatymasardauna
       ????Mrs Sardauna????

Dedicated To My Brother Khabier….

????Kainuwa Writers Association

((United we stand ans succeed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers))

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button