SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

WATTPAD
@fatymasardauna
Chapter 25 to 26
“Yanzu likita ya za ayi kenan ?” Baffa yatambaya fuskarsa ɗauke da damuwa, ajiyar zuciya Doctor S.S yasauƙe haɗe da cewa ” asamu wanda zai kwana da’ita, kafun gobe Idan Allah yakaimu ” yanaƙare zancen, yasoma tattare files ɗin dake baje kan table ɗin dake gabansa..
Tuƙi yakeyi amma gaba ɗaya jinsa yake wani iri, duk wata ƴar walwala da kuzarinsa sun ƙaura daga garesa, sosai fyaɗen da akamawa yarinyar yataɓa ransa, hakanan yakejin matsanancin tausayin yarinyar na ratsa zuciyarsa,gaskia wasu mazan basu da imani, ka suma ƴar ƙaramar yarinya kamar wannan, ka danneta kakuma yi mata fyaɗe da ƙarfin tsiya, idan kai akamawa taka kuma bazakaji daɗi ba, ya Allah kasakama bayinka,… Horn biyu yayi kacal maigadi ya wangale masa tankamemen gate ɗin gidannasu, a parking space yayi parking motar tasa, haɗe da fitowa, kai tsaye ɓangarensa yanufa, domin yana da yaƙinin zuwa yanzu su Hajiyarsa sunshiga, ko yaje ɓangarensu bazai tadda suba,
“SADDIQ!!” wata ƴar dattijuwar mata dake tsaye a bayansa taƙira sunansa,, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Doctor S.S yayi haɗe da juyowa, ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi yayi ya aza akan fuskarsa, “Hajiya barka da dare” yafaɗa cike da girmamawa, “Yauwa barka dai, sai yanzu kake dawowa ?” sunkuyar dakansa ƙasa yayi haɗe da sanya hanunsa abayan kansa yashiga shafa ƙeyarsa, “Hmm da kyau, duk nasan mai yajawo hakan, rashin iyali ne, kuma wallahi komai yakusa zuwa ƙarshe, a wannan karon ko kana so ko baka so,yazama dole kafitar da mata ko kuwa, in zaɓa maka cikin ƴaƴan ƙannena, bazanci gaba da sanya maka idanu ƙato dakai ace baka da mata ba !!” Hajiya tafaɗa cikin faɗa, “Kiyi haƙuri Hajiya Insha Allah nan ba da jimawa ba komai zai dai dai ta”
“Koda yaushe haka kake cewa, inanan inasa ido, idan naji shiru kuma kasan sauran ” Hajiya tafaɗa, juyawa tayi kaitsaye tanufi ɓangarenta, shima nasa ɓangaren yanufa, jinsa yake amatuƙar gajiye, wanka yayi haɗe da bin lafiyar gado ya kwanta, abu na farko daya fara ziyartan idanunsa bayan yarufesu, shine hoton fuskar Zahrah, sosai hoton fuskarta keyi masa gizo,acikin idanunsa, da sauri yabuɗe idanun na sa, a zuciyarsa yana mai mamakin faruwar hakan, dayaga abun bana ƙare bane, kawai saiya dangana hakan, dacewa tsananin tausayinta ne yajawo hakan……
ZAID kuwa yana barin Zahrah kai tsaye TRANSCORP HILTON yanufa, domin dai yauma yana da meeting a can… Bayan sunkammala meeting ɗinne, kai tsaye yawuce ɗakinsa dake ɓangaren V.I.P,, yanashiga yasoma rage kayan dake jikinsa, direct bathroom yashige yasakarmawa kansa shower,, wani irin sanyi da nishaɗi yakeji a cikin zuciyarsa, tun bayan abun daya shiga tsakaninsa da Zahrah, yakejin ransa yayi fari, nishaɗi kawai yakeji acikin zuciyarsa, gaskia yau yasha zallan madarar daɗi, domin kuwa sosai ɗanɗanon Zahrah yayi masa hundred percent, yanason mace mai ɗanɗano sosai… Yana fitowa daga wanka, wayarsa dake aje kan gado, tasoma ƙara haɗe da kawo haske, alamar shigowar ƙira, saida wayar tasa takusa katsewa kafun yaɗauki wayar haɗe da karawa akan kunnensa, “Shigo ciki” Zaid yafaɗa a taƙaice haɗe da cilla wayartasa kan gado,, Abid ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo,, rungumar juna sukayi, kamar yanda suka saba koda yaushe idan sun haɗu,,
“Daga ina haka ?” Zaid ya tambayi Abid, murmushi Abid yayi haɗe da zama akan hamshaƙiyar kujeran dake gefen gadon ɗakin, ” yau nasha sweet abokina, wata babe nasamu mai zafi, inagayamaka tashayar dani zuma !!” Abid yafaɗa cike da nishaɗi,, Dariya sosai Zaid yayi hadda ƙyaƙyatawa, shiru kawai Abid yayi yatsaya yana kallon Zaid, domin dai Zaid baya dariya abanza, abune mai wuya kaga dariyansa, sai dai idan ya ƙulla wani abun… ” Final !!” Zaid yafaɗa yanamai cije laɓɓansa,, zaro idanu Abid yayi cike da mamaki yace ” what ! ? badai kanaso kacemin harka gama da Zahrah ba ??” ƙayataccen murmushi Zaid yayi haɗe da cewa “Tuntuni harma anwuce wajen ” dariya Abid yayi haɗe da cewa ” Har yau bansan kai wani irin mutum bane Zaid, idan kaso abu, to ko ta wani hali sai ka sameshi, Allah sarki, Innocent girl, tanacan tana fama, nasan kabata kaya da yawa, may be ma haryanzu bata san awace duniya take ba ” Abid yafaɗa… Still murmushi Zaid yayi haɗe da gyara zamansa, wayarsa yajawo yashiga latsawa, amma fuskarsa ɗauke take da murmushi… Ganin haka yasa Abid sha re maganar domin yafahimci me abokinnasa yake nufi,, Jefi jefi suke hira da Abid…..
Washe gari… Har 9:00 am Zahrah bata farfaɗo ba, Doctor S.S yazo yasake dubata, yakumayi mata duk wani abu daya kamata, amma still ko motsawa batayi ba… Abu kamar wasa tun anasa ran farfaɗowar Zahrah har dai akasoma cire rai, domin kuwa yau kwananta biyu batasan inda take ba… Sosai Doctor Saddiq yake bawa Zahrah kulawa, kuma yau yake da yaƙinin farfaɗowarta insha Allah…
Ƙafantane yafara motsawa, sannu a hankali idanunta suka soma ɗan buɗewa, ƙwaƙwalwarta ne tashiga tariyo mata duk wani abu daya faru da’ita, wani irin ƙara Zahrah tasanya wanda yayi matuƙar firgita su Baffa da Inna dake zaune gefe da gadon da take kwance,, “Subahanallahi !!” Baffa ya faɗa cike da tashin hankali,,, ihu kawai Zahrah ke yi haɗe da fisge fisge, tamkar dai mahaukaciya,, Dagudu Baffa yayi waje don ƙiran likita,, duk yanda Inna taso riƙe Zahrah abun yagagara domin kuwa duk ta fusge ƙarin ruwan da akayi mata, cikin hanzari Doctor Saddiq yaƙaraso cikin ɗakin, cak yatsaya ganin yanda Zahrah ke ihu tana ta fusge fusge, wani irin mugun tausayinta yaji ya daki zuciyarsa,, tattaro duk wani kuzarin sa yayi yaƙarasa gareta, wani irin fusga Zahrah tayi, ai kuwa saiga Inna dake riƙe da ita, tafaɗi ƙasa warwas,, da hanzari ya kama hannayenta duka biyu, yana mai ƙoƙarin nutsar da ita, wani ihun takumayi wanda sautinsa ya zagaye kowani kusurwa na ɗakin, fuskar Zaid kawai take hangowa akan ta Dr Saddiq,
“Wayyo Allah na, Baffa kataimakeni zai kasheni, zai kasheni, wayyo !!!” abun da Zahrah take ta faɗa kenan cikin hargowa da son ƙwace kanta daga wajen Doctor Saddiq,, duk yanda Dr Saddiq yaso tayi shiru abun yacitura, domin da alama bata cikin hayyacinta,, wani irin cizo Zahrah ta gantsara masa ahannu, sosai yaji zafin cizon amma yasan tabbas yana saketa, guduwa zatayi, ko kuma ma tayimawa kanta rauni,, wani irin ƙara ta callara tana mai shirin turesa ta gudu, yayi saurin rungumeta ƙam acikin ƙirjinsa, wasu lafiyayyun cizo Zahrah tashiga gantsara masa akan ƙirjinsa, sake rungumeta yayi ƙaƙam acikin jikinsa, haɗe da rumtse idanunsa, yakuma datse lips ɗinsa da haƙoransa,, sosai yakejin zafi har cikin ƙwaƙwalwarsa, domin kuwa da iya ƙarfinta take cizon sa,, ganin cizo bazai wadatar ba yasanyata sanya hannayenta, duka biyu ta shiga dukansa tako ina,, tabbas duk wanda yaga abun da Zahrah takeyi yasan cewa bata cikin hayyacinta,, da ƙyar Dr Saddiq ya’iya danneta yayi mata wata allura wacce take kashe jiki, ta kuma gusar da ƙarfin jikin ɗan adam,, take tayi laƙwas haɗe da sulalewa daga jikinsa tafaɗa kan gado, kallonta yashiga yi gaba ɗaya tayi buji buji da tulin gashin kanta, gashi duk taɓalle maɓallan gaban rigarta, wanda hakan yabayyana kyakkyawar surar ƙirjinta,, saurin ɗauke idanunsa yayi daga kan ƙirjin nata, haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, juyo da kallonsa yayi zuwaga kan su Baffa da suke tsaye cirko cirko, gaba ɗaya sunyi wani tsuru tsuru dasu, tamkar ace musu as su antaya a guje, bama kamar Inna,,