SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Kansa kawai ya jijjiga batare da yacemusu komai ba, yayi ficewarsa daga cikin ɗakin,, direct office ɗinsa ya nufa, da kansa ya haɗa tea mai kauri, kaitsaye ɗaki na musamman ɗin daya sa aka kai Zahrah yanufa, riƙe da kofin tea ɗin a hanunsa, baitaradda su Baffa a cikin ɗakin ba, don haka kansa tsaye yanufi gaban gadon nata,, kwance take flat daganinta kasan babu wani wadataccen ƙarfi ajikinta, saidai hawayene kawai ke ambaliya yana gangarowa ta gefen idanunta,,, “Zahrah” yaƙira sunanta, duk da yasancewa bazata taɓa amsa masa ba, saboda batacikin nutsuwarta…
Aje ƙofin tea ɗin dake hanunnasa yayi, haɗe da ɗaukar pillow yasanya a bayanta, da ƙyar yasamu ya iya jinginar da ita ajikin pillow’n, a hankali yake ɗiban tea ɗin cikin tea spoon yanakaiwa bakinta, duk yanda yaso ta buɗe baki tasha tea ɗin hakan yagagara, domin daya sanya mata ruwan tea ɗin acikin bakinta, zaidawo waje,, aje kofin yayi haɗe da harɗe duka hannuwansa akan ƙirjinsa, kallon fuskarta yashiga yi natsawon wasu mintuna, ajiyar zuciya ya sauƙe alokaci guda, haɗe da ɗaukar kofin tea ɗin yafice daga cikin ɗakin,, umarni yabawa wata nurses da tayi mawa Zahrah alluran bacci, domin duk yafahimci irin situation ɗin da take ciki a yanzun…
Gaba ɗaya ihun Zahrah ya karaɗe ɗakin, hankalinsu Inna gaba ɗaya atashe yake, kamar yanda tayi ɗazun, yanzuma haka takeyi, domin ihu da fusge fusge kawai take saidai yanzu, cewa take “Kutaimakeni, zai kasheni, wayyo Allah na, kutaimakeni !!!” abun da Zahrah take faɗa kenan cikin hargowa, da wani irin hanzari ta diro daga kan gadon, da take kwance, kaitsaye bakin ƙofa tanufa da gudun gaske, da sauri Baffa yasha gabanta, wani irin ƙara ta sanya, domin kuwa Zaid tagani tsaye a gabanta, amaimakon Baffa, wani irin ƙarfine yazomata aikuwa kyakkyawan hankaɗa tayimawa Baffa, saigashi jagwaf a ƙasa, dama bawani kuzari gareshi ba,, gaba ɗaya tayi buji buji da jikinta, ta tarwatsa gashin kanta, gudu kawai Zahrah take tsakaninta da Allah, daga zangar ta haɗu da mutane sai tasanya ihu, domin kowaye zatayi tozali dashi to fuskar Zaid take gani, akan tasa, hartakai bakin ƙofar fita daga cikin asibitin, cikin zafin nama ya cafko hanunta, wani irin ihu Zahrah tashiga kurmawa, tamkar wacce ake yankan naman jikinta, tun fitowarta mutane ke kallonta, atunaninsu mahaukaciya ce,, bai damu da ihun da takeyi ba, duka hannayen ta yahaɗe waje ɗaya, caɗak ya ɗagata haɗe da saɓata kan kafaɗarsa, yayi cikin asibitin da’ita,, wani irin ƙara tayi, take kuma jikinta ya sake numfashinta gaba ɗaya ya ɗauke,
Duk inda suka wuce sai ankallesu, wasu suna matuƙar tausayinta, da ƙuruciyarta amma hauka ta risketa, anasu zaton mahaukaciya ce..
A kan gado ya shimfuɗeta, haɗe da rufamata bargo, wasu allurai yayi mata, bayan yasanya mata drip ɗin dazai taimaka wajen bawa jikinta kuzari, koda bataci abinci ba….
“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un, ya Allah kataimaketa, haƙiƙa tanacikin mawuyacin hali, ya Allah kasa kada abun danake zargi yatabbata, Allah katsaremata ƙwaƙwalwarta, da kariyarka !!” Dr Saddiq yafaɗa cikin karyewar zuciya, haɗe da tsananin tausayin Zahrah,, sau da dama akanyi mawa yara ƙanana fyaɗe, firgici da tsoron da suke samun kansu ciki, yakan taɓa musu ƙwaƙwalwa, sai aga kamar sun zare, hakan yasa basa da wowa hayyacinsu cikin sauƙi,, a wannan rana dai Dr Saddiq da ƙyar ya iya barin asibitin, gaba ɗaya lamarin Zahrah ƴatsaya masa arai, tausayinta yakeji sosai….
Tsaf yagama shirya kansa cikin wasu mayun riga da wando, masu kyau da tsadar gaske, bakaɗan ba yayi kyau sai tashin daddaɗan ƙamshi jikinsa yake, SHU’UMIN NAMIJI kenan ganinka babu alkhari acikinsa, ƴar ƙaramar trolly bag ɗinsa ya shiga ja, bayan yaɗauki wayoyinsa da kuma duk wani abu dayasan zai buƙata,, wannan karan ko ɓangaren mahaifiyarsa bai jeba, motarsa ƙirar BUGATI yashige, yayin da driver yabamawa motar wuta, kaitsaye airport suka nufa, domin dai alƙawari Zaid yaɗauka yau bazai kwana acikin Nigeria ba, yawon shaƙatawa zai tafi New York City (America).. Yana shiga cikin jirgin baiwani jimaba, jirginnasu yaɗaga zuwa sararin samaniya…..
((kuyi haƙuri page ɗin yau baida yawa…))
12/November/2019
_____________
MRS SARDAUNA
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
phatymasardauna
Dedicated To My Loveƙy Brother Khabier…
????Kainuwa Writers Association
”'{United we stand and succeed our ambition is to intertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
Wannan Page ɗin gabaki ɗayansa kyautane a gareku.
UMMIEE-ZARIA.
MRS MAI LAWAL.
MAMAN TEEMAH.
ZEE BLACK.
AYSHA HUMAIRA.
SA’ADAH GALADIMA.
MY ADIZATOU (Ummu Adnan.)
MARIYA…❤.
Chapter 27 to 28
Tunda Zahrah tasume, bata sake sanin inda kanta yake ba, sai ƙarfe shida na yamma, alokacin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba, wannan karon sam batayi wannan iface ifacen da kuma fusge fusgen da tasaba yi ba, sai dai idanunta da ta tsayar waje ɗaya,wato kan ceiling ɗin dake saman ɗakin, hawayene kawai kefitowa daga cikin idanun ta, yana mai sauƙa a gefen fuskarta, “Zahrah !” Inna dake gefe taƙira sunan Zahrah.
Ko gizau Zahrah ba tayi ba, balle Inna tasaran zata amsa mata, gyra tsayuwa Inna tayi haɗe da jinjina kanta, tabbas tasan koma meyafaru da Zahrah sune sanadi, domin kuwa basu riƙe amanar da iyayenta suka basu kafun su rasu ba.
Dr Saddiq ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo, bakinsa ɗauke da sallama, yayinda Baffa ke biye da shi a baya, “Yauwa likita kazo ko? ta farka amma kwata-kwata bata magana!” Inna tafaɗa cike da damuwa.
Ɗan guntun murmushi kawai Dr Saddiq yayi,haɗe da nufar inda Zahrah’n ke kwance, kallonta yayi na ɗan wasu mintuna, kana yajuyo da kallonsa wajen su Baffa… “Inaso Za’ayi mata gwajin ƙwaƙwalwa, domin sake tabbatar da lafiyarta, saboda haka zanturo Nurses su ɗauketa ” Dr Saddiq yafaɗa.
Sosa kai Baffa yashiga yi, cike da damuwa yace “To kamar nawa ake buƙata likita? kuma naga tunda mukazo ka ke bata kulawa, amma banji anyi min maganar nakawo ko sisi ba, fatana Allah yasa gwajin ƙwaƙwalwar bashi da tsada !” Baffa yafaɗa cikin karyewar zuciya, domin kuwa idan gwajin yana da tsada tofa sai dai ahaƙura, saboda bashi da kuɗi.
Kallonsa kawai Dr S.S yayi batare da yace dashi ƙalaba, ya sa kai yayi ficewarsa daga cikin ɗakin.
Mintuna kaɗan da fitarsa, wasu nurses su biyu suka shigo, ɗaukan Zahrah sukayi, suka ɗaurata kan wani gado mai ƙafafun taya, suka fice da’ita, ba don idanunta da suke buɗeba, tabbas da idan ka ganta zakayi zaton gawace, domin kuwa babu abun dake, motsi a jikinta, sai hawaye kawai dake ambaliya a cikin idanunta…