SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Alhmdlh anyi mawa Zahrah gwadin ƙwaƙwalwa lafiya, saura kawai ajira fitowar result.
Babu abun dayake ɗaga mawa Dr S.S hankali a yanzu, kamar yanda take yawan firgita, gashi hawaye sun kasa daina zubowa daga cikin idanunta, babban abun damuwar kuma shine bata um balle um um, ko motsawa bakinta bayayi, sannan kuma waje ɗaya idanunta suke kallo, wato sama.
Result ɗin gwadin da’akayi mata yafito, kuma masha Allah, ƙwaƙwalwarta tana nan lafiya, babu abun daya sameta, kawai dai tashiga halin firgici ne, kuma dama ana yawan samun irin haka…
“Likita ya sakamakon, Allah yasa bata samu wani matsala a ƙwaƙwalwarta ta ba ? ” Baffa dake zaune cikin office ɗin Dr S.S ya tambaya.
“ku kwantar da hankalinku, sakamako yayi kyau, domin kuwa brain ɗinta nanan lafiya”
“Alhamdulillah, Allah mungodema !” Baffa yafaɗa cike da jin daɗi,
“Kaine Babanta mahaifi ?” Dr S.S yatambaya sanda yake ƙoƙarin cike wani file dake gabansa.
“A’a bani na haifeta ba, ƴar ɗan uwana ne da ya rasu, amanarta yabarmin, gashi yanzu bansan wani tsinannen bane ya aikata ma ta wannan abun ba !” Baffa yaƙare maganar yana matsan ƙwalla.
Kallon sa Dr S.S yayi na tsawon wasu mintuna, kafun ya kau da kansa gefe, “Dawa take mu’amala, saurayi ko aboki ?” Dr S.S ya kuma tambaya.
“Bata mu’amala da kowa sai wani yaron arziki, shine ma yace yana sonta, kuma hargida yataɓa zuwa ya gaisheni, a zahirin gaskia bana tunanin shi zai yi mata wannan aika aikan” Baffa yafaɗa da ƙwarin guiwarsa.
“Maiyasa kake tunanin shi bazai iya yi mata haka ba ?” Dr S.S yakuma jefo mawa Baffa tambaya,
“Saboda shiɗin yaron kirkine kuma ɗan babban gida ne, mutane masu dattako” (readers kuji Baffa fa da sharri )
“Zaka iya tafiya, anjima zanzo na bata maganinta” Dr S.S yafaɗa a taƙaice, domin kuwa wani irin taƙuƙin takaicin Baffa ne ya cika masa zuciya,
Sumi sumi haka Baffa yafice daga cikin office ɗin, yana matsan ƙwalla.
“Wai maiyasa mutane suke wasa da amana ne ? idan har ɗan uwanka bazai iya riƙe maka ahalinka, idan baka raye ba, to waye zai iya riƙe maka su da gaskia dakuma amana? ƴar ɗan uwanka tamkar ƴa take a wajenka, idan baka nuna ma ta soyayya ba, to wazai nuna ma ta? irin su Baffa ne suke ɓatawa mutane suna, kuma suke tozarta marayu, ya Allah kabamu ƴan uwa masu amana, wanda zasu kula da namu ko bama raye Ameen.” Dr S.S yafaɗa acikin zuciyarsa,
Yau kwanan Zahrah Biyu kenan bata magana, hawaye har sun gaji da fitowa daga cikin idanunta sun kafe, duk kuwa yanda su Baffa suka so ta faɗi koda kalma ɗaya ne, hakan ya gagara, domin kuwa ko kallonsu batayi balle su sa ran zatai musu magana. Sosai Dr S.S yake ƙoƙari wajen kulawa da’ita, baya wasa da lokacin shan maganinta, domin yana da yaƙinin zuwa yanzu, ɗinkin da akayi mata a ƙasanta ya warke.
Zaune yake a kan ɗaya daga cikin kujerun falon mahaifiyar sa, sanye yake da riga da wando na maroon ɗin bugaggiyar shadda, bakaɗan ba kuwa yayi kyau acikin kayan, kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa a kwai damuwa a tattare dashi, domin kuwa tun ɗazu aka aje masa plate ɗin snacks a gabansa, amma yakasa ɗaukan ko da ƙwaya ɗaya ne, yakai bakinsa, duk da kuwa snacks ɗin abune mafi soyuwa a garesa,,
Hajiya ce tsaye a kansa, tayi kusan minti ɗaya da zuwa amma sam baisan da zuwan nata ba,
“Saddiq!” Hajiya taƙira sunansa.
“Na’am, Hajiya sannu da fitowa!” Dr S.S yafaɗa cikin girmamawa.
Zama Hajiya tayi haɗe da kallonsa cike da kulawa tace ” Wai meke damunka ne Saddiq ? ina lure da kai gabaki ɗaya kwana biyunnan bana gane kanka, idan kafita aiki baka dawowa da wuri, ga yawan tunani da kakeyi, meke faruwa ne ?” Hajiya ta tambaya.
Gyara zama Dr S.S yayi, domin sam baya ɓoyewa mahaifiyar tasa matsalarsa,ko ta me cece kuwa, cike da damuwa yace “Hajiya wata yarinya aka kawo hospital ɗinmu, duka dukanta bazata wuce 18 to 19 year ba, yarinyar tana matuƙar baƙatar taimako, domin kuwa, wani ne yayi raped ɗinta, ahalin da ake ciki yanzu, ko magana batayi, narasa wace hanya zanbi nashawo kan lamarin!” Dr S.S ƴafaɗa cike da raunin murya,
“Subanallahi fyaɗe kuma Saddiq ?”
“Eh Hajiya, shiyasa abun yake damuna” Dr S.S yafaɗa,
“Allah sarki! Allah ubangiji ya cigaba da tsare mana ƴaƴanmu, amma iyayenta sun maka case ɗin a kotu ne ?” Hajiya ta tambaya.
“A’a Hajiya banjin zasu kai case ɗin kotu, domin kuwa talakawa ne basu da wani ƙarfi ” Dr S.S ya faɗa cike da tausayawa.
“To Allah yabata lafiya, amma miye na jefa kanka acikin damuwa haka Saddiq? irin wannan matsalolin naga dama an riga da an saba kawo muku, sai dai Allah yarufa asiri kawai, bakaci snacks ɗinba mai yasa ?”
“Zanci Hajiya ko zuwa anjima ma” Dr S.S yafaɗa lokacin dayake miƙewa daga kan kujeran dayake zaune,
“A’a ina zaka kuma ?” Hajiya ta tambaya.
“Lokacin shan maganin Zahrah yayi Hajiya, zanje ne na bata” yaƙare maganar yana mai duba wrist watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.
“Zahrah! wacece kuma Zahrah ?” Hajiya ta tambaya,
“Itace yarinyar da akayi raped nata dana gaya miki”
“To to adawo lafiya”
“Ameen Hajiyana!”
Yana fita yashige cikin motarsa kaitsaye hanyar asibitinsu ya ɗauka….
Kamar koda yaushe zaune take akan gado, yayinda idanunta ke kafe a waje ɗaya, ruwan hawayene kawai ke tsiyayowa daga cikinsu,
Da Sallama ɗauke a bakinsa yaturo ƙofar ɗakin, harya ƙaraso tsakiyar ɗakin, batasan ma da zuwan sa ba,
Aje abubuwan dake hanunsa yayi akan ƴar ƙaraman drowern dake gefen gadon, “Zahrah!” yaƙira sunanta cikin kwantar da murya, bata amsaba kuma bata juyo zuwa garesa ba, dama kuma yasan hakan zai iya faruwa, domin bata taɓa amsawa idan yaƙirata, bakuma ta tankamai komai zaice, duk da kuwa yasan tanajinsa.
Magungunan da yakamata tasha ya ɓare, haɗe da zubasu acikin hanunsa, goran ruwan daya shigo da shi yaɗauka, haɗe da ƙarasawa gareta, hanunta yakama yana ƙoƙarin sanya mata maganin , wani irin firgita tayi haɗe da fasa ƙara, wanda yajanyo hankalin Baffa da Inna dasuke zaune a waje, da hanzari suka shigo cikin ɗakin, da gudu Zahrah taƙarasa jikin Inna ta rungumeta, wani irin kuka mai tsananin ban tausayi tashiga rerawa,, sai kawai Inna ma ta fashe da kuka, tana mai tausayin Zahrah har cikin zuciyarta, domin kuwa lokaci ɗaya gaba ɗaya ta lalace, ta rame har duhu saida fatarta tayi, “kice su fita Inna dan Allah! kice masa kada yasake zuwa inda nake natsanesa! natsani duk wani Namiji! na tsanesu kice su fita, ko kuma inkashe kaina!!” Zahrah taƙare maganar tana mai ɗaukar wani Scissors dake aje kan wani ɗan ƙaramin table.
“Suhanallahi Zahrah mekikeyi haka ?” Baffa yafaɗa yana mai ƙoƙarin matsowa gareta,
Ihu Zahrah tasanya mai ƙarfin gaske, haɗe da saita scissors ɗin dai dai saitin cikinta, da iya ƙarfinta taɗaga zata cakawa kanta, cikin matuƙar zafin nama, Dr S.S ya murɗe hanun ta, haɗe da bata wani kyakkyawan mari akan kumatunta, “saboda hauka zaki kashe kanki ne? wani irin rashin hankaline wannan!!?” yatambaya cikin faɗa.
Zamewa tayi ƙasa tana mai rushewa da wani irin kuka mai cin rai da taɓa zuciya, shikenan itakam rayuwarta tagama lalacewa, komai nata ya tarwatse bata da wani saurin farinciki a cikin rayuwarta..
Ransa amatuƙar ɓace yafice daga cikin ɗakin, yayinda Baffa ya rufa masa baya…