SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Dafa kafaɗunta Inna tayi cike da tausayawa tace “Kiyi haƙuri Zahrah komai yayi farko yana da ƙarshe, ki barwa Allah lamuranki insha Allah, Allah zai saka miki”
duk iya rarrashin da Inna tayimawa Zahrah, taƙi ji, kuka kawai takeyi tamkar ranta zai fita, ankawo mata abinci ma, taƙi koda kallonsa ne balle su sa ran cewa zataci, lokaci ɗaya idanunta sun kumbura suntum dasu, da ƙyarma take iya buɗesu, ga wani irin masifaffen zazzaɓi daya rufe ma ta jiki alokaci guda, take ta fara masassara, tana cikin wannan yanayin aka soma ƙiraye ƙirayen sallan magriba, dakanta ta ɗauro alwala tazo ta gabatar da salla, duk da kuwa irin ciwo da kanta keyi mata,, koda takai sujjadan ƙarshe, wani irin matsanancin kukane ya ƙwace mata, saida tayi mai isarta kafun ta ɗago da ga sujjadan, da ƙyar dai tasamu ta iya sallame sallan, tamiƙe akan sallayan kenan, wani irin juwa ya ɗebeta, take tayanke jiki tafaɗi, da hanzari Inna tayo kanta, jijjigata tashiga yi, haɗe da soma ƙiran sunanta, dai dai lokacin wata nurse tashigo cikin ɗakin,, “yauwa likita dan Allah zoki dubamin ita gatanan jikin yaƙi daɗi!” Inna tafaɗa cike da damuwa… Da taimakon nurse ɗin suka ɗaura Zahrah a kan gado, zuwa yanzu da ƙyar take iya fidda numfashi, jitakeyi tamkar kanta zai fita tsabar ciwo, ƴan gwaje gwaje nurse ɗin tayi mata, ganin abun bawani babba bane, yasa tayi mata allura, haɗe da bata wasu drugs tasha, cikin mintuna ƙalilan bacci yayi awun gaba da ita.
tun da Dr S.S yabar ɗakin bai zarce ko inaba, sai office ɗinsa, tattare duk wani abu dayasan zai buƙata yayi, haɗe da jawo office ɗinnasa ya rufe, kai tsaye motarsa yashige bai zarce ko inaba, sai gidan Aunty Raliya (babbar yayarsa)…
Yana shiga cikin gidan, su Meenal da Affan, sukayo wajensa da gudu, suna cewa “oyoyo Uncle S.S!!” cike da farinciki Dr S.S yaɗaga su sama, fuskarsa cike da annuri yace “Oyoyo babies ɗina, yakuke, ya school ?” “lafiya ƙalou Uncle ya office ?” Meenal ta tambaya cike da iyayi, murmushi yayi haɗe da jan kumatunta cikin dariya yace “hinyau su Meenal angirma, har wani iyayi kika iya ko?” dariya suka sanya dukansu, hadda wata kyakkyawar mata da tafito daga cikin kitchine, wanda a ƙalla bazata wuce 35 years ba,
“Manya sai yau kaga daman leƙomu?” matar tafaɗa dai dai lokacin da take zama akan kujera.
“Auntƴ Raliya bazaki gane bane, ayyuka ne sukai min yawa, a office shiyasa !” yafaɗa cike da gajiyawa.
“hmmm daman nasan haka zakace ai, kai dai koda yaushe cikin aiki kake tamkar inji.”
“Saudat! Saudat! kawo mawa Uncle drinks ” Aunty Raliya tayi maganar cikin ɗagawar murya..
mintuna ƙalilan Saudat mai aikinta, tacika masa gabansa da drinks hadda dangin su snacks, domin kuwa duk wanda yasan sa, to yasan abun dayake so…
cake ya ɗauka yakai bakinsa, haɗe da lumshe idanu, “Um gaskia Aunty cake ɗinnan yayi daɗi!” Dr S.S yafaɗa yana mai jinjina kai, alamar cake ɗin yasamu karɓuwa a wajensa,,
Dariya Aunty Raliya tayi, haɗe da cewa “yakamata na sa maka waiji, domin na lura nan da mintuna kaɗan zaka faɗo daga kan kujeran nan, tsabar santi “
Dariya suka sanya dukansu,,
Gyara zama Aunty Raliya tayi haɗe da cewa “Waini Uncle (Uncle shine sunan da take ƙiransa) ya maganan Aurenka da Zabba’u ne ? naji shiru ba ka sake ɗago zancen ba, ince dai komai lafiya?”
Take fuskar Dr Saddiq ya sauya,daga walwala zuwa akasinta…
(( kuyi haƙuri yau nayi typing ɗin, cikin yanayin rashin jin daɗi????, please kuyi haƙuri da abun da kuka samu, dan ko editing banyi ba.
Next page zakuji labarin shu’umi ZAIDU????))
14/November/2019
MRS S.S ????????????
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written by
phatymasardauna
????Mrs Sardauna????
Dedicated To My Lovely Brother Khabier
????Kainuwa Writers Association
”'{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
(A gaskia ina matuƙar jin daɗin haɗin kan da kuke bani, bantaɓa zaton Shu’umin Namiji !! zai samu karɓuwa, a wajenku haka ba, Alhmdlh sai dai na godemawa Allah, domin a haƙiƙanin gaskia inajin daɗin addu’arku gareni, Allah yabar ƙauna a tsakaninmu, masoyana ina tsananin son ku a duk inda kuke.????????)
Chapter 29 to 30
Take fuskar Dr Sadeeq ya sauya, daga walwala zuwa akasinta.
“Ya dai naga ka haɗe fuska, a lokaci guda? Aunty Raliya ta tambaya,
“Bakomai Aunty, kawai gajiya ne” Dr S.S yafaɗi haka don son katse zancen da sukeyi,
“yazama dole fa muyi zancen nan Uncle, domin kuwa Hajiya da kanta taƙirani jiya, kuma duk akan batun auren naka ne, wai sai yaushene zaka fito da matar aure ? yaka mata ace zuwa yanzu ka aje mata hadda ƴaƴa, amma kwata kwata ko batun aure bakaso ayi maka mai yasa ne Uncle ?
A je cake ɗin dake hanunsa yayi, haɗe da gyara zama, cikin sanyin murya yace “bawai fa banson aure bane Aunty Raliya, nima inaso nayi aure, kawai dai Allah ne baikawo matar auren ba”
“baka dai ga dama ba, amma matan aure kam a kwaisu baja baja a gari, haka kuma a kwaisu da yawa acikin dangi, idan har bakason Zabba’u, ai ga Farida nan, ƴar Aunty Mariya, mai yasa bazakaje ku magantuba ? idan ma dukansu basuyi maka ba, sai kaje gidan Baffa Amadu a kwai ƴan mata dayawa, son kowa ƙin wanda yarasa, wayayyu kuma ƴan boko, amma idan kace ba haka ba, to fa duk wacce Hajiya ta haɗaka da’ita, kada kazo kace zakamin ƙorafi !” Aunty Raliya ta ƙare maganar cikin sigar faɗa faɗa, domin zuwa yanzu al’amuran ƙanin nata yasoma isarta, shikenan aita abu ɗaya, mutum duk hanyar da kabi dashi sai ya kauce..
“Shikenan Aunty zanyi tunani, kuma zanje gidan su Farida’n insha Allah !” Dr S.S yaƙare maganar yana mai tashi tsaye,,
“Au wai saboda nayi maka faɗa shine kake ƙoƙarin tafiya ?” Aunty Raliya ta tambaya.
“Bahaka bane,dama gaisheku kawai nazoyi” yafaɗa cike da ƙosawa.
“Shikenan to, dama akwai snacks ɗin dana haɗama, bana kawo ma saika tafi dashi ” Aunty Raliya tafaɗa, tana me miƙewa tsaye.
“godiya nake, ki bamawa Meenal takawomin mota ” yana kaiwa ƙarshen zancen nasa, yasakai yafice daga cikin falon,, Saudat ce ta kawo masa snacks ɗin cike a leda, yana karɓa yayi mawa motarsa key…
NEW YORK CITY
Kishingiɗe yake akan wani kujera da a kayisa kamar gado, wanda yake aje bakin wani ƙaton beach mai kyau da ƙayatarwa, kamar yanda kowa yasani beach wajene na shaƙawatan mata da maza,gaba ki ɗaya mutanen dake kai kawo a wajen nan turawa ne, babu kuma wata suturar kirki a jikinsu, wasu daga su sai ɗan pant da breziya wasuko riguna ne ƴan fingil fingil sanye a jikinsu, abun dai ba kyaun gani, domin komai nasu tsirara ake gani, amma duk da haka basu wani damuba, domin haka ɗabi’arsu take..
Sanye yake da 3 guater jeans mai kalan baƙi, yayinda rigar jikinsa ta kasance fara ƙal, sannan irin marassa hanun nan ne (sleevless t-shirt) gashin kansa kaɗai abun kallone, domin kuwa yasha gyara, ƙyal ƙyali da kuma walwali kawai yake fitarwa, kallo ɗaya zakai masa kasan cewa yana cikin jin daɗi da tsagwaran hutu, wani zungureren glass cup ne riƙe a hanunsa yana sipping wine ɗin dake cikin cup ɗin a hankali.