SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

16/November/2019
MRS SARDAUNA
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written by
phatymasardauna
????Mrs Sardauna????
Dedicated To My Lovely Brother Khabier
????Kainuwa Writers Association
”'{United we stand and succeed; our ambition is to entertein & motivate the mind of readers}”’
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
Chapter 31 to 32
Dai dai ta ɗaura hanunta kan handle ɗin ƙofar kenan, aka turo ƙofar daga waje, cikin rashin sa’a ƙofar ya bugeta a goshi, saurin ja da baya tayi haɗe da rumtse idanunta gam, ji takeyi tamkar ta shaƙesa ya mutu, ta tsani ganin kowani irin namiji ne a rayuwarta, musamman ma shi,domin kuwa yanayinsu yana ma ta shige da Zaid, kuma gani take tamkar kowani namiji irin halin Zaid garesa,,
“Ganinki tsaye anan yatabbatarmin cewa guduwa zakiyi, Miye ribarki a rayuwa idan kika gudu daga gaban i yayenki ? nasan duk inda zaki bazakiyi rayuwa mai kyauba, idan kika zaɓi tafiya can wata uwa duniya mai zaki tsinta? ina mai tabbatarmiki cewa babu wani abun da zaki tsinta sai, zallan takaici, dakuma ƙuncin rayuwa, zaman bariki kikeso kiyi? kokuwa zaman kanki kike so kiyi? ” da sauri taɗago manya manyan idanunta dasuke cike tab da ƙwalla ta watsa masa wani irin mugun kallo…
“Babu abun daya shafeka da rayuwata, idan naga dama nayi kowacce irin rayuwa ma baishafeka ba, duk ba kune kuka jefa rayuwata acikin matsanancin duhu ba, wallahi na tsani naji koda kalmar farkon sunan kune a cikin kunnuwana, ballan tana aƙira sunan Namiji akusa dani, natsaneku! natsaneku!! ” wani irin kukane ya ƙwace mata maicin rai,
“Kacuceni Zaid! Kacuceni! natsaneka tsana mafi muni! mai nayi maka dana cancanci wannan sakamakon a wajenka? mai na aikata maka wanda yasanya ka cutar da rayuwata? bazan yafe maka ba Zaid! kacutar dani, karuguzamin duk wani buri nawa, ka tarwatsamin rayuwata, mai yasa saini kazaɓa maiyasa!!!” taƙare maganar cikin ƙaraji da matsanancin kuka, tamkar wanda takama Zaid ɗin a gabanta..
Wani irin mugun tausayin tane yaji ya daki zuciyarsa, haƙiƙa Zahrah abar tausayice, domin kuwa tanacikin wani hali wanda take buƙatar abokin rarrashi da kuma mai kwantar mata da hankali,,, juyawa kawai yayi yafice daga ɗakin, domin kuwa jin kukanta yake har tsakar kansa.
Nurse yaturo tazo tayi mawa Zahrah alluran bacci, domin idan ba alluran bacci akayi mata ba yana da yaƙinin cewa kwana zatayi tana ruskar kuka..
Duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa, hakan ya gagara domin kuwa duk juyin da zaiyi wani irin matsanancin tausayin Zahrah ne ke cika masa zuciya, baisan wani irin tausayawa yake mawa Zahrah ba, amma tabbas yasan tausayinta da yakeyi, yayi ƙarfi a cikin zuciyarsa, da ƙƴar dai yasamu ya yakice tunanin Zahrah, a cikin zuciyarsa ya samu yayi bacci, wanda rabin mafarkansa ya kasance na Zahrah ne…
Wanene Dr S.S. ?
Dr Sadeeq yakasance ɗa na biyu a cikin gidansu, Alhaji KHABEER SARDAUNA shine mahaifinsa, Alhj Khabeer wanda ake ƙira da Alhj Sardauna, mutum ne mai matuƙar karamci da kuma kyautatawa na ƙasa dashi, hakan yasa talakawa suke matuƙar sonsa, kasancewarsa ɗan siyasa, Hajiya Habiba itace mahaifiyar Dr Sadeeq, mace ce itama mai tsananin karamci dakuma kyauta, tana da kyakkyawan hali wanda kowa yashaida hakan, Dr Sadeeq shine ɗa na biyu a cikin gidansu, yanada yaya wacce ake ƙira da Aunty Raliya, Aunty Raliya dai, tana aure ne a cikin garin Abuja, tana kuma zaune a unguwar Wuse Zone 2, bayan Dr Sadeeq a kwai ƙaninsa Samad, Samad dai baya zaune a Nigeria yana zamane a Australia, a can yake da karatunsa, tun Dr Sadeeq yanada shekaru 20, Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa, mutuwar da ta matuƙar girgizasu, amma babu yanda suka iya dole su ɗauki dangana domin kowani bawa da kalan tasa ƙaddaran.. yanzu tsawon shekaru biyu kenan Hajiya Habiba tana matsawa Dr Sadeeq, a kan cewa yafito da matar aure, amma abun yagagara, da anfara maganar aure sai abun yalalace, ko daga baya yace baison yarinyar, ko yace bata da nutsuwa, da haka dai magana zata ɓalakuce,, yanzu ne Hajiyarsa ta hura masa wuta akan cewa lallai tabasa nanda kwana kaɗan yafito da matar aure dan bazata ci gaba da zuba masa idanu babba dashi ace bai aje iyali ba….
Washe gari..
Ƙarfe 3 da rabi na yamma Dr Sadeeq da kansa ya rubutawa su Zahrah sallama, domin ya fahimci cewa matuƙar bai sallamesu ba, za a iya nemanta a rasa, bakuma zai so hakan ba.
Koda suka fito daga cikin asibitin, duk yanda yaso Zahrah tashiga cikin motarsa ya kaisu gida ƙiyawa tayi, dole haka yanaji yana gani suka tari mai taxi, baiyi ƙasa a guiwaba wajen shiga motar tasa ya rufamusu baya…
Suna isa bakin ƙofar gida, idanun Zahrah ya sauƙa a dai dai wajen da Zaid yake faka motarsa kullum idan yazo, wani irin muguwar faɗuwar gaba taji, take kuma zuciyarta tayi rauni, kuka ne ya kuma ƙwace mata, da sauri tafice a cikin motar dagudu tanufi cikin gida,, saida Inna suka sallami mai taxi kafun suka lura da Dr Sadeeq dake tsaye a bayansu yana ƙarewa yanayin unguwar tasu kallo, “A’a Likita dama kana biye damune ?” Baffa ya tambaya washe da baki,,
“Eh Baffa ina biye daku, dama gani nayi yakamata ace nasan gidan saboda magungunan ta basu ƙareba, nakuma san basha zatanayiba matuƙar ba’a tilasta mata ba”
“Ƙwarai kuwa likita ai taurin kai gareta, dole saida takurawa, to mushiga daga ciki mana ” Baffa yaƙare maganar yanamai yi mawa Dr S.S nuni da ƙofar shiga gidan.. Baiyi musu ba haka yabi bayan Baffa suka shiga cikin gidan,
Inna ce ta baje masa wani ƙaton tabarma ya zauna akai, yayinda ta ɗebomasa ruwa a kofi ta aje mai.
Gyara zama Dr S.S yayi haɗe da cewa “Baffa inaso muyi wata magana ne idan har bazaka damuba ”
“Faɗi maganarka kai tsaye likita, kada kaji wani shakku” Baffa yafaɗa yana mai dawo da hankalinsa ga Dr Sadeeq.
“Maiyasa bazaku kai case ɗin Zahrah kotu ba? yakamata ace amatsayinta na marainiya a bimata haƙƙinta, bai kamata ace wani ƙaton banza ya keta mata haddi ba, sannan kuma abarshi yaci gaba da walwala, inaga yakamata ayi wani abu akai” Dr Sadeeq yafaɗa cike da damuwa.
Nannauyar ajiyar zuciya Baffa ya sauƙe haɗe da jinjina kansa, cike da rauni yace “Bazanƙi shawaranka ba likita, sai dai a gaskia bazan ɓoye maka ba, hakan da kake so bazai samuba, domin yanda ka ganmu nan haka muke rayuwarmu, mu talakawa ne, cin yau da ƙyar na gobe da ƙyar, kuma maganan nan ma da nake maka, bansan wanene yayi mawa Zahrah fyaɗe ba, to ka ga kenan babu batun ma ɗaukar fansa”
“Wanene ZAID ?” Dr S.S ya tambayi Baffa.
Washe da baki Baffa yace ” shine yaron da Zahrah ta amince dashi, yake zuwa zance wajenta, idan kuma bazaka mantaba ai nafaɗa maka shiɗin yaron kirkine, na tabbatar da cewa baisan haka yafaru da ita ba, da nasan dole zaizo” Baffa yaƙare maganar yana mai jinjina kai..