NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Shine yayi mawa Zahrah fyaɗe !” Dr S.S yafaɗa murya a kausashe,

Gaba ɗaya idanunsa Baffa ya zaro, alamar maganar ta dake shi, “Zaid fa kace likita !” Baffa yafaɗa cikin kaɗuwa,

“Ƙwarai kuwa domin kuwa jiya ta ambaci sunansa, nakuma ji da kunne na, amma tunda kace ba zaku kai case ɗin kotu ba, bakomai ni zan wuce” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai  miƙewa tsaye, bayan yaciro damin kuɗi ya a jewa Baffa kan tabarma,,

“A’a hadda ɗawainiya haka likita? to to munagodiya!” Baffa yafaɗa cike da farinciki, 

(hmm mai hali dai baya fasa halinsa)

“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Malam hayaƙi, hayaƙi Malam a ɗakin Zahrah !!” Inna tafaɗa cike da tashin hankali, ai da sauri Dr Sadeeq da baffa, suka nufi ɗakin Zahrah’n wanda hayakin haryasoma cika tsakar gidan, dayake ƙofar bata da wani ƙarfi duka ɗaya Dr S.S yayi mawa ƙofar ɗakin tabuɗe,  gaba ɗaya ɗakin yaturnuƙe da hayaƙi yayinda wuta kecin wasu kaya dake aje tsakiyar ɗakin, gefe da kayan kuma Zahrah ce durƙushe tana kuka, har wutan yakusa ƙarasowa gareta,

Cikin zafin nama, Dr Sadeeq yasanya hanunsa, ya janyeta daga tsugunnen da take,   kai tsaye waje yafito da’ita, domin kuwa hayaƙin yasoma shiga cikin maƙoshinsu, Baffa da Inna kuwa ruwa suka ɗebo suka kashe wutan,

Riƙeta yayi gam yayinda ya kafeta da idanunsa da suka rune tsabar ɓacin rai,

Baisan meyake damuntaba, rashin hankaline ko kuma sangartane baisaniba, yasan cewa tanajin ciwo a cikin zuciyarta, amma abun da take ƙoƙarin aikata mawa kanta, kama yake da taɓin hankali,  ƙoƙari yayi wajen danne zuciyarsa, haɗe da saisaita muryarsa, “Maiyasa Zahrah ? bazaki ɗau ƙaddaranki ba ?” yayi mata tambayar cikin tausasa murya,   hawayene suke gudu haɗi da ambaliya akan fuskarta,  gaba ɗaya jitakeyi duniyar najuya ma ta, dawowanta gida yasake tada mata da mikin dake maƙare cikin zuciyarta, duk da kuwa dama cewa mikin  bai wau ya kwanta ba ne,,

Saurin saketa yayi  sakamakon ƙarasowar Baffa da Inna wajen, zamewa tayi aƙasa dabas tana mai sakin kuka,

Kallon Baffa Dr Sadeeq yayi, kafun Baffa yace komai Dr Sadeeq yace, “Baffa ni nawuce sai nasake zuwa “

“To Likita mun gode ka gai da gida ” Inna da Baffa suka haɗa baki wajen faɗa, da “To”  kawai Dr Sadeeq ya amsa musu haɗe da sa kai yafice daga cikin gidan,

Kama hanun Zahrah Inna tayi suka zauna akan tabarma, cike da damuwa Inna tasoma cewa “Maiyake damunkine Zahrah ? sai kace akanki aka fa ra yin fyaɗe? gaba ɗaya duk kinbi kinɗaga hankalinki, muma kin ɗaga mana namu hankalin, a gaskia nida Baffanki munsoma gajiyawa da wannan halin naki, bayan kinso caka mawa kanki almakashi, likita ya hana, yanzu kuma ƙona kanki kikesonyi, wai kina  cikin hankalinki kuwa Zahrah?”

“Gaya mata dai Salame, domin nima nan nasoma gajiya da rarrashi,  yanzu dakika ƙona kayayyakin daya baki, shiɗin kika ƙona ne? tambayanki nake shiɗin kika ƙona ?” Baffa yafaɗa cikin faɗa faɗa, domin ya lura idan suka biyewa Zahrah tofa bazata taɓa daina yunƙurin kashe kanta ba..

Zuciyar Zahrah ne tasakeyin rauni, ” Allah sarki ni, komai nayi, ganin laifina suke, shin bancancanci rarrashi da kulawaba? fyaɗe akayimini amma hakan baiwani shiga jikin kowa ba, natabbata idan da iyayena suna da rai, to tabbas da bazasu taɓa kwantar da hankalinsu ba, kuma nasan dolene sai sun ɗaukarmin fansa,  bakuma zasu taɓa gajiyawa daniba, wayyo Allah na mutuwa tayi mini yankan ƙauna daku iyayena !!” maganar  da Zahrah take faɗa kenan a cikin zuciƴarta, hawayenta ne suka sake tsananta zuba,  sai yau ta tabbatar cewa Maraici bashi da daɗi, sai yau tasake tabbatar da cewa Allah ne kaɗai gatan ta,  Zaid ya cuceta, yayi mata babban tabo wanda hargaban abada ba zata taɓa mantawa dashi ba, “maiyasa Zaid ?” tasake tambayar kanta bayan kuma tasan bata da amsa,,

Haka Inna da Baffa suka wuce ɗaki suka barta zaune a tsakar gida tana tsiyayar hawaye, babu mai rarrashi.

Tuƙin mota yake amma gaba ɗaya hankalinsa yanaga yanda yabaro Zahrah,  tsantsar tausayinta yakeji, yanason taimaka ma ta amma to tayaya? ta wacce hanya? duk alokaci ɗaya ya tambayi kansa,  wayarsa ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira,  Zabba’u shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da ɗaukan wayar yakara a kan kunnensa, 

“Cike da sangarta Zabba’u tayi masa sallama, amsa sallaman yayi a daƙile haɗe da cewa “Ganinan zuwa” ƙit yakashe wayar haɗe da cillata kan kujeran mai zaman banza, shi sam baisan yanda zaiyi da Zabba’u ba, amma a zahirin gaskia ɗabi’u da tarbiyanta basu masa ba,duk da kuwa cewa ƴar uwa take a garesa.

New York City

Tsaye yake agaban wani tangamemen cupboard paper, wanda yake liƙe ajikin wani abu kamar allo,  sanye yake da 3 guater jeans, yayinda yabar gaba ɗaya surar jikinsa a waje, kasancewar baisanya rigaba, babban abun  ɗaukar hankali ajikinsa shine lafiyayyun, 6 packs ɗinsa, dake kwance raɗa raɗa akan cikinsa, riƙe yake da wani dogon pen a hanunsa da’alama dai wani abu yake zanawa mai mahimmancin gaske,, ƙayataccen murmushinsa yasake, haɗe da ɗaukan glass cup ɗin da wine ɗinsa ke ciki, yakai bakinsa, saida ya shanye duka wine ɗin dake cikin kufin, kafun ya aje kofin kan wani ɗan ƙaramin table dake kusa dashi,

Hanunsa yasanya akan kyakkyawar fuskar daya zana a jikin cupboard paper ɗin, a hankali yashiga shafa zanen , hanunsa yakai dai dai saitin bakinta, haɗe da shafawa, idonsa ɗaya yakashe haɗe da lasan laɓɓansa, 

“Kinkasa barina My Sugar Baby, maiyasa ? ” yayi tambayar yana mai tsare zanen dake jikin cupboard papern da ido,

“Bazaki amsaminba ko? fushi kike dani ko sugar baby na?”

Yasake tambayar wannan zanen dake jikin cupboard paper’n.

Murmushi yakumayi haɗe da matsawa daf da cupboard paper’n bakinsa yaɗaura adai dai kumatun ta yamanna mata kyakkyawan kiss, “Kikulamin da kanki kinji My Zahrah!!” yafaɗi maganar cikin shauƙi,,  sai alokacin nalura ashe zanen fuskar Zahrah ne raɗau ajikin cupboard paper’n, bakaɗan ba kuma zanen yayi kyau,, kyakkyawan ƙyalle yasanya yarufe zanen, haɗe da ɗaukar wayarsa yafice daga cikin ɗakin…

Yana fita falo Abid dake tsaye tun ɗazu yana zaman jiransa, ya saki tsuka, haɗe da cewa ” Wai don Allah maika tsaya yi ? tun ɗazu fa kasan nakejiranka, amma ka shanyani “

Zama Zaid yayi akan kujera haɗe da jawo kwalbar wine ɗinsa, yashiga shan abunsa, ganin haka yasa Abid sauƙe ajiyar zuciya haɗe da girgiza kai, wato dai yau ƴan halinne suka motsa, gaskia Zaid yanada wuyan sha’ani, bakoda yaushe kake gane gabansa da bayansa ba, duk da kuwa tsananin sabon dake tsakaninsu, amma shi kansa wataran idan Zaid ya juye tofa baya iya gane masa.

“Kana yawan shan wine Zaid, baka tunanin zata iya janyomaka matsala nan gaba ?” Abid ya tambaya cike da kulawa, domin kuwa, shi ko za’a kasheshi bazai iya shan rabin wine ɗin da Zaid yakesha a rana ba,

“Maiyashafeka da shan wine ɗina ?sanin kankane natsani sa’ido ” Zaid yayi maganar cikin haɗe fuska,

Dariya Abid yayi, domin kuwa yanzu yatabbatar cewa Shu’umin cin nasa ne ya motsa, “Okay i’m sorry bazanƙara ba, amma yakamata ace musauƙa ƙasa, babes ɗin nan fa suna jiranmu ”   Abid yafaɗa yana mai duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button