NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kaje kawai ka sallamesu, nikam bana ma buƙatar ganinsu, mata duk a bubbushe, ba wani diri mai burgewa, sai kace 1, kaje can kata fama idan zaka iya” Zaid yafaɗa cike da ƙuncin rai,

Dariya sosai Abid yayi,  haɗe da tashi kawai yafita daga falon, gaba ɗaya kwana biyun nan yarasa maiyake damun Zaid..

Abid na fita Zaid yagyara zamansa, haɗe da lumshe idanunsa, gaba ɗaya fuskar Sugar Babynsa ne yake yimasa gizo a cikin idanun nasa.

Abuja Nigeria

Zahrah ce zaune akan ƴar yaloluwar katifarta,  ta tanƙwashe ƙafafunta, yayinda kanta ke kallon sama,  ruwan hawayene kawai ke gangarowa daga cikin idanunta,   kallo ɗaya zakai mata wata irin muguwar tausayinta yadaki zuciyarka, domin kuwa wani irin muguwar rama ce ta bayyana a jikinta,

Da sallama Khausar tashigo cikin ɗakin,   kamar daga sama  haka Zahrah taji muryar aminiyarta ta wato Khausar, tana kai kallonta bakin ƙofa taga Khausar ɗin tsaye tayi turus,,
Ai dagudu Zahrah taje tafaɗa jikin Khausar, haɗe da sakin wani sabon kuka mai sauti,   duk da cewa Khausar batasan abun dayake faruwa ba, amma tasan cewa ba lafiya ƙawartata take ba, kawai itama sai tafashe da kuka, hakanan taji wani irin tausayin Zahrah’n yacika zuciyarta, rungumeta tayi da kyau a jikinta,   ko kaɗan Khausar batayi yunƙurin hana Zahrah   kuka ba,  saida Zahrah tayi kuka sosai, kafun ta tsagaita, a hankali take sauƙe ajiyar zuciya,, hanunta Khausar takama suka zauna akan katifar Zahrah’n,,

“Zahrah!” Khausar taƙira sunanta cikin sanyin murya, Zahrah bata iya amsa mata ba, sai ɗago idanunta da suka kumbura suntum tsabar kuka, tayi ta kalli Khausar ɗin,

Zaro idanu Khausar tayi, cike da tashin hankali tace “Zahrah maiyake faruwa ne,  tun ranan nake ƙiran wayarki a kashe, nazo gida kuma bansamu kowaba, nazo yafi sau huɗu bana samun kowa acikin gidan, dan Allah ƙawata kifaɗamin maiyake faruwa ?” Khausar tayi maganar cikin damuwa.

“Rayuwata taƙare Khausar, yacuceni,ya yi mini babban illa, dakuma tabo wanda bazai taɓa gogewa ba, ya nakasamin rayuwata, ashe haka ƙaddara zata zomin mummuna? nayarda cewa kowani bawa da’irin tasa ƙaddaran amma ni tawa ƙaddaran tafi takowa muni,  danasan haka zata faru dani, dana roki Allah daya kasheni kafun yanzu na….” Saurin toshe mata baki Khausar tayi, cike da ruɗani haɗi da tashin hankali,  Khausar tace “Kada kiyi saɓo Zahrah,  kinsani acikin duhu, kisanar dani maike faruwa dan Allah,  gaba ɗaya kinsani cikin tashin hankali !” Khausar tafaɗa cikin ƙosawa,

“Za..i..d yayi min fyaɗe Khausar !!!” Zahrah tafaɗa tana maisake rushewa da kuka,,

Tamkar anwatsamata ruwan zafi haka Khausar taji ajikinta, lokacin da maganan Zahrah yadaki dodon kunnenta,   “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Fyaɗe fa kikace Zahrah ?” Khausar ta tambaya cikin matsanancin tashin hankali, lokaci guda hawaye suka shiga sauƙa daga cikin idanunta, take jikinta yayi sanyi laƙwas,,

“Yacutar da rayuwata Khausar, ashe haka soyayya ta ke? rama alkhairi da cuta, ashe haka duniya take cike da azzaluman bayi? maiyasa yayi min haka Khausar? mainayi masa? yaruguzamin duk wani farincikin rayuwata,  wayyo Allah na Khausar ki karɓi wuƙannan ki kasheni dashi ko da zansamu sauƙi da salama acikin zuciyata !!” Zahrah taƙare maganar tana mai miƙomawa Khausar wata wuƙa da ke aje gefenta,,

Matsanancin kuka Khausar tasanya, haɗe da jawo Zahrah jikinta, ta rungumeta ƙam,  kuka suka shiga yi wiwi, babu mai lallashin ɗan uwansa…

((Agaskia banson abunda wasunku sukemin,musamman masu cewa naƙara musu yawan typing, inaso kusani cewa, banda wadataccen lokaci, inazuwa makaranta, inada miji, sannan kuma nima inada wasu uzururrukan, yakamata kuna hakuri, amma wasu  har baƙar magana su ke ƙoƙarin gayamin don kawai shekaran jiya nayi muku typing kaɗan, hmm wlhy kunbani mamaki, ni bana neman faɗa da kowa, saboda banɗauki duniya komai ba,  shekaran jiya a matuƙar gajiye nake saboda naje school, amma haka na lallaɓa nayi muku typing, a she duk da haka wasunku   basu godeba, haka sukaita ƙananan maganganu,  wata har cewa take wai tagaji da wayon danake yi,koda yaushe sai nace na gaji, yes dole nagaji tun da dai ni ba engine bace, da za’ace bazan gaji ba, kuma ina da abubuwanyi.   kuyi haƙuri my real fans na zage inata faɗa, wlhy raina ne yaɓaci wasu komai kamusu baka burgesu.
Nadawo gareku sisters masu cewa Zahrah tasoma basu haushi sbd abubuwan da takeyi, yaka mata ace kufahimceta, bawai inabin bayan tabane, amma yana da kyau ku yi imagine akan ya mace za taji idan har akai mata fƴaɗe?dole za taji matsanancin ciwo, acikin zuciyarta, kuma dole ne abun zai zama babban tabo wanda bazai taɓa gogewa acikin zuciyarta ba, saboda haka kuyi hakuri kuyi mata uzuri. ))

         18/November/2019*

        
         MRS SARDAUNA
????????????????????????????????????????

            SHU’UMIN NAMIJI !!

       Written by
   Phatymasardauna

Dedicated To My Lovely Brother Khabier (My  ƙwarnafi, da mita, lol ????)

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

            WATTPAD
      @fatymasardauna

Editing is not allowed????

Kusha Sha’aninku Team ZAIDU????????

1-Rhupys khair
2-Maimunerh minah
3-Saudat 0ne
4-maryam wazeer
5-Aisha salis
6-Mar’uda
7-Oum Zahrah
8-Oum Aboul
9-Oum saddiqa
10-Oum suwaib
11-Nana jasko????
12- Halima nancy
13-Zuwaira ibraheem
14-Aminan bash
15-Saudi ghans, real tawajena
16- Surayyah
17-Shamsiyya-7 shams
18- Rauda Umar

Kunayi inajin daɗi team Zaidu ???? amma fa iyakune kawai team ɗin nasa waƴanda basa ganin laifinsa, lol, nasu Zahrah kam ba’a magana suna cikin ƙunci????, saura kuma Dr S.S.????

Chapter 33 to 35

(Kuyi haƙuri nayi mistake, ƙawar Zahrah sunanta Husnah ne ba Khausar ba, kamar yanda nasa a page ɗin baya,  Husnah nakeson sawa, to bestyna saita tsayamin arai nasa sunanta,lol.)

Kuka suka shugayi wiwi babu mai lallashin ɗan uwansa, da ƙyar Husnah ta’iya tsagaita kukanta,haɗe da daidaita nutsuwarta,  duk da cewa zuciyarta bata daina bugu ba, tamkar ƴar uwa ta jini haka ta ɗauki Zahrah, saboda haka duk wani abu daya faru da Zahrah tamkar da ita yafaru, domin kuwa abokin kuka shi’ake gayawa mutuwa, wannan abotar tasu tasamo asaline tun suna yara, haka kuma sun ƙulla abotansu cikin gaskia da yarda da juna,,

“Bazance miki kidaina kuka ba, Zahrah domin idan nace miki haka, banyi miki adalci ba, sai dai zan sake tunatarmiki cewa akwai Sarkin sarakuna, mai tausayi ga bayinsa, mai amsa addu’an bayinsa, mai basu, mai kuma hanasu, shi ishashshene akan dukkan komai, yanaji,kuma yana gani, sannan kuma shi ya wanzar da faruwar haka a gareki, tunkafun ya halicceki ya tsara, cewa  hakan zai faru a kanki, kada kiyi jayayya Zahrah, domin kuwa  babu wani bawa a duniya daya isa ruguza tsarin Allah,  Allah baya bacci, yanasane da wanda sukayi cuta, dakuma wanda aka cuta,  zaifi kyau ki miƙa al’amuranki garesa, haƙiƙa nasan cewa abun da Zaid yayi miki, abune mafi matsanancin ciwo acikin rayuwar ƳAMACE, amma kashe kai, ko kice a kasheki banaki bane Zahrah,  rungumar ƙaddara ita tafi dacewa dake, haƙiƙa nasan cewa har gaban abada bazaki mantaba, amma inaso kiɗauki ƙaddaranki, kimiƙawa Allah lamuranki, da sannu zakiga sakayya,  ke ba jahila bace, da iliminki na addini dana zamani, saboda haka inaso kiyi amfani da wannan ilimin naki wajen ɗaukar ƙaddaranki hanu bibbiyu, kada kice na faɗi haka ne don banasonki, wlhy inasonki ƙawata, inajinki tamkar jinin  jikina, kawai dai hakan shine mafita !!”  Husnah tayi maganar cikin tsananin tausayawa,  yayinda ruwan hawaye suka gama wanke fuskarta…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button