NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali Zahrah taɗago idanunta dasuyi jajur tamkar anwatsa musu garin barkono, ta kalli Husnah, sosai maganar Husnah yadaki zuciyarta, sai dai yazame mata dole shiga ƘUNCIN RAYUWA,   da ace zata buɗewa mutane ƙirjinta suga, cikin zuciyarta, to tabbas da tayi hakan, domin tasan duk wanda yaga ciwon dake mamaye da zuciyarta, to tabbas  dole ne zai koka mata, domin kuwa wani irin danƙareren ciwone yabaibaye zuciyarta, wanda batasa ran zata warke har gaban abada,

” Ashe babban kuskurene ɗaukar soyayya ka bawa wanda yafika?  menene aibuna dan nafito a mace? me maza sukaɗauki mata ne? a she dan kana talaka shikenan kai bakomai bane? bakuma ka da ƴanci? ya ketamin haddina da ƙarfin tsiya, yanunamin ƙarfi da kuma fifiko, duk dan kawai ina mace,  maiyasa ya tsalleke dukkan mata yazo kaina nida banda kowa sai Allah?  nayi masa kuka, nayi masa magiya, na roƙesa amma ya toshe kunnuwansa, yacire duk wani imaninsa ya cutar da rayuwata, kigayamin miye laifina dan nafita cikin hayyacina ? ki faɗamin shin bancancanci in haɗiyi zuciya in mutu ba, f…ya…ɗ…e fa yayi mini Husnah!!!” Zahrah tafaɗi maganar  cikin matsanancin kuka,

Duk yanda Husnah taso ta sake danne zuciyarta kasawa tayi, kawai sai ta sake sakin kuka haɗe da rungume Zahrah ƙam acikin jikinta,

Saida sukayi kuka sosai, kafun suka soma sakin ajiyar zuciya, take zuciyar Husnah tayi sanyi, amma banda ta Zahrah, domin babu wani sanyi daya ragewa zuciyar Zahrah.

A hankali Husnah tashiga shafa bayan Zahrah, wacce haryanzu sheshsheƙan kuka take,

” Ki tsaida kukanki Zahrah, kuka baya maganin komai, sai dai ya sanyamiki ciwon kai, addu’a ita kaɗai ce magani, nasanki Zahrah, inakuma da yaƙinin cewa baki kai kukanki ga Allah ba, kiji rani inazuwa ” Husnah tafaɗa tana me miƙewa tsaye, kaitsaye ficewa tayi daga ɗakin, yayinda Zahrah tafaɗa kan katifa taci gaba da kukanta,,,

Mintuna kaɗan Husnah tashigo ɗakin hanunta riƙe da wasu magungunan da likita ya kawowa Zahrah, wanda takarɓo wajen Inna,,

Ledan da tashigo dashi ta jawo, haɗe da ƙarasowa wajen Zahrah, tamkar ƴa da uwa, haka Husnah  ta jawo Zahrah jikinta, cike da tausayi haɗi da rauni tace ” Kidaina kuka dan Allah Zahrah, kinga ko na tahomiki da abincin da kikafi so,  Shinkafa da Kifi,  Mom ce ta dafa ” Husnah taƙare maganar tana mai buɗe  wni kula, wanda ta ciro a cikin ledan da tazo dashi,

“Nasan bakici komaiba, kuma koda nace kici ma, cemin zakiyi kin ƙoshi, amma dan Allah kici ko kaɗanne zanji daɗi Zahrah, baki da kowa sai Allah, amma kada kimanta nidake tamkar gudan jini muke, damuwarki damuwata ce ” Husnah tafaɗa tana mai zub da  ƙwalla,

Kallonta Zahrah tashigayi, take kuma zuciyarta ta karye, sai kawai tafaɗa jikin Husnah, tashiga sauƙe ajiyar zuciya,,

Cike da lallami  Husnah  tashiga bawa Zahrah shinkafa da kifin da takawo, duk dacewa maɗaci yafi abincin daɗi a bakinta, amma hakanan ta daure takeci, badon komaiba sai don  Husnah tacancanci tayi mata komai a rayuwarta, itace mace ta farko data fara bata kyakkyawan kulawa wanda tunda abunnan yafaru da ita babu wanda yabata, sai likita..

Duk da cewa bata wani ci mai yawa ba, amma zaiyi mata amfani,   domin kuwa cikinta yajima ba’asa mai komai ba  a cikinsa,,

Husnah  nagama bata abincin, ta ɗauko musu Al’Qur’ani guda biyu,  miƙawa Zahrah ɗaya taƴi, haɗe da buɗe mata fejin farko,  cemata tayi su karanta a tare,  duk da cewa da ƙyar muryarta yake fita amma sosai tayi ƙoƙari wajen karanta Al’Qur’ani,n.

Babu abun da yagagari Allah, Al’Qur’ani littafine mai cike da tarin  haske, yana wanke zuciyar maikarantasa, yanasanya nutsuwa ga ma’abocin karantashi,  take ƙuncin dake maƙare acikin zuciyar Zahrah yasoma ragewa, sunacikin karatun wani irin bacci ya yi gaba da’ita,, take ta kwanta a wajen tahau bacci,,
Murmushi kawai Husnah tayi haɗe da ɗaukar Al’Qur’ani’n, dake riƙe a hanun Zahrah ta aje gefe,

“Kayafe ma ta ya Allah! domin nasan tsananin tashin hankali da damuwa, su sukayi tasira a cikin zuciyarta, wajen mantar da’ita kai kukanta gareka!” Husnah tafaɗa tana mai kallon sama, gudun kada ta tashi Zahrah a bacci yasanya tasoma karatun nata ƙasa ƙasa…

((Ƙawaye: bawai nishaɗantarwa kaɗai shine amfanin muba, mu mata ne, kuma mu ƙawayen juna ne, yana da kyau, mu ƙaunaci junanmu, tsegumi, ƙyashi, baƙinciki, hassada, duk banamu bane,  kamar yanda akace ciwon ƴa mace na ƴa mace ce, yana da kyau muɗauki hakan da matuƙar mahimmanci, du kanmu zamuso ace munsamu ƙawa kamar Husnah, to amma ta yaya zamu samu ƙawa kamar Husnah? dole ne mu tsarkake zuciyoyin mu, mudaina mawa junanmu ƙyashi da hassada, mudaina bawa junanmu mugayen shawara, mudaina zuga wasunmu sukai kansu zuwaga halaka,  kada ki bata gurguwar shawara wanda zata cutar da’ita, wai don takawo kanta gareki domin kibata shawara, kada ki zugata akan cewa ta aika ɓarna, idan har bazaki faɗa mata alkhairi ba, to kada ki faɗa mata sharri, dukanmu mata ne, kuma dukanmu zuciyoyin mu suna da rauni,  ta yarda dake, saboda kunyi shekara da shekaru kuna tare, hakan yasa ta ɗauki duk wani sirrinta ta zazzage miki, maiyasa tayi haka? saboda ta ɗaukeki ƴar’uwa,  tunda ta sanar dake duk wani sirrinta, mai yakamata kiyi? saiki riƙe mata amana, ki tsare mata sirrinta, amma saiki kaje ki ka tona mata asiri a wajen mutanen duniya, idan kikayi haka kincancanci a ƙiraki da suna ƙawa? maiyasa muka ɓata kanmu ? mukaraba kan abotanmu ? saboda bama iya riƙe sirrin juna, kuma bamaso kowa ya ƙaru, ko ya samu buɗi, saimu kaɗai,  yana da kyau muriƙe abotarmu da kyau, domin a matsayinmu na mata idan bamuyi abota da junan muba, da waye zamuyi? da maza? suda basusan yanda zasu magance mana matsalolinmuba, sirrin mace fa sai mace ƴar uwarta, please Sisters dan Allah muyi ƙoƙari wajen gyara zuciyoyinmu, domin mukasance abokai na ƙwarai, masu rufa asirin juna.))

Zaune yake a katafaren wajen shaƙatawa dake farfajiyar gidan, sanye yake da riga da wando na jamfa hadda hulansa, bakaɗan ba yayi kyau, kasancewarsa matashi mai jini a jika, sannan kuma dama akwai kyau ɗin tubarkalla, Wayarsace ƙirar iphone Xs Max riƙe a hanunsa yana faman latsawa da dukkan alamu abu mai mahimmanci yakeyi, ƙamshin turarenta ne yafara cika hancinsa, a hankali yaɗago kansa yakai dubansa zuwa gareta, sanye take da doguwarriga na atamfa wanda yakama jikinta sosai, yayinda ta saƙala wani ɗan ƙaramin vail a wuyanta, balaifi tayi kyau, tunda dama kyakkyawace.

cike da takun ɗaukar hankali taƙaraso wajen dayake zaune bakinta ɗauke da sallama,

Amsa mata sallaman yayi yana mai ɗauke idanunsa daga gareta, domin komai najikinta bayyane yake a fili.

Kujeran dake kusa dashi ta ja, ta  zauna, cikin sauyawa murya amo  tace,  “Barka da zuwa Jarumi na”

Kai kawai yaɗaga mata alamar yaji, batare daya Kuma kallon taba,  sake lanƙwasa murya tayi, takuma cewa “Yakamata mu’isa falon baƙi ai, sai nake ga kamar zaman mu anan baiyiba, kasan fa kai ɗin maidaraja ne baidace ace nabarka anan ba” taƙare maganar tana mai kaɗa idanunta, alamar yanga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button