NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

WAYE ZAID ?

Zaid tantirin Mazinaci ne kuma ɗan giya, uwa uba baida mutumci ko ƙaɗan, sannan kuma komai kayi masa baka burgesa, Zaid yana da Munanan halayya, Zina shine babban ciwon daya riga yayi mawa jiki da zuciyarsa ƙawanya, Zaid Mazinaci ne na ƙarshe, iskancin sa yake zubawa babu mai hanasa, domin dai iyayensa sunriga da sungama shagwaɓasa, bayajin maganan uban kowa, duk wata haɗɗɗiyar mace wayayya dake cikin garin Abuja babu wacce batasan Zaid ba, domin iskancinsa ya shahara yayi ƙarfi, kasan cewarsa kyakkyawan saurayi mai wanka da naira, yasanya wasu ƴan mata ke matuƙar ƙaunarsa, sannan kuma suke burin mallakansa, amma saidai sama yayiwa yaro nisa babban ma saidai kallo….

  *MRS SARDAUNA*

????????????????????????????????????????

     *SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*

phatymasardauna
????Mrs Sardauna????

Dedicated To My Lovely Brother Khabeer

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
    *WATTPAD*

@fatymasardauna

Editing is not allowed ????

Chapter 4

Alhaji Ma’aruf Chanji shine sunan maihafin Zaid, Babban mutum ne da ake da mawa dashi acikin Nigeria, yana da kuɗi sosai, sannan mutum ne mai kyautatawa na ƙasa dashi, bashi da rowa ko kaɗan, matarsa ɗaya Hajiya Safara’u kuma itace ma haifiyar Zaid, daga Alhaji Ma’aruf har Hajiya Safara’u shuwa arab ne, Allah yayi musu baiwar kyau ga dukiya, shekaransu biyu da Aure Allah ya azurtasu, da haihuwan ɗa Namiji, wato Zaid, Zaid dai kyakkyawan gaske ne, domin tsananin kyawunsa ke sawa yake shiga ran jama’a, Zaid tun yana ƙarami yataso da wani irin Shu’umanci, ga mugunta, haka zalika baruwansa da shiga harkan kowa, hatta iyayensa kuwa, gaisuwa kawai keshiga tsakaninsu, duk yanda suka so yasake dasu amatsayinsu na mahaifansa, amma abun yaci tura, Sosai Iyayen Zaid ke nuna masa tsananin ƙauna, da tattali, asalin sana’ar Alhaji Ma’aruf shine Chanjin kuɗaɗe, yayi ƙaurin suna a sana’ar, sannan kuma yatara maƙudan kuɗaɗe, ganin harkan nasa natayin gaba dukiyarsa na ƙara yawa, yasanyashi tattarawa yakoma America da zama, can ya cigaba da business ɗinsa, duk ko yanda yaso Hajiya Safara’u tabiyo sa America suzauna ƙiyawa tayi, saidai Zaid yayarda yabi mahaifinsa, inda a can yasoma karatun sa,, Zaid yanada shekaru goma a duniya mahaifiyarsa ta haifa masa ƙanwa maisuna Labisat, Labisat dai kyakkyawar yarinyace suna kama da Zaid, saidai a gaskia Zaid yafita kyau sosai, domin idan kaga Zaid zakai tunanin ba ɗan Nigeria bane,,,, acan America mahaifin Zaid kasuwancinsa kawai yasa a gaba, amma sa’i da lokaci yana zuwa Nigeria duba iyalansa,, Yanayin yanda yake gudanar da kasuwancinsa a America yasanya bashida wani kyakkyawan lokacin da zai kula da ɗansa wato Zaid, kullum Alhaji Ma’aruf idan yafita office baya dawowa sai dare, shikuwa Zaid rayurwasa yakeyi da turawan abokansa, wanda yayisu acikin school ɗin dayake, kunsan dai su turawa, babu wani abun daya damesu iskanci sun maidashi kamar ruwan sha, domin dai dayawansu ba addinin Allah suka sani ba balle su kiyaye, tun Zaid na da shekara 17 yafuskanci abokansa na school suna neman mata, shikuwa sam alokacin mata basa gabansa, duk da kuwa cewa suna kawo masa tallen kansu, amma baya sauraransu, duka abokan Zaid turawa ne, sai mutum ɗaya wato ABID Abid cikekken ɗan Nigeria ne cikin garin Abuja shima gidansu yake, sannan babansa shine Minister’n Man Fetur na Nigeria gaba ɗaya, Abid hatsabibin ɗan iska ne kuma tantiri domin kuwa tun yana ƙaraminsa yasan yanda zai jagwalgwala mace, Zaid da Abid a bota suke sosai, domin jininsu yazo ɗaya,, duk da cewa Zaid yana da ƙarfin sha’awa amma bayabin mata, saidai wani zubin yakan ɗan mawa mace kiss da dai sauransu,, lokacin da Zaid yake matakin lavel 2 na degree ɗinsa lokacin yana da shekara 21, Allah ya jefomasa ƙaddaransa kuma Hargitsi mafarin halakarsa,,, wata rana sunje yawon shaƙatawa shida saiɗanun abokansa, ya haɗu da wata ƴar iskan baturiya mai suna Nicky, abun daya fa ra ɗaukar hankalin Zaid game da Nicky shine kyawu da surarta, Nicky irin fitinannun matan nanne, shu’umai wanda idan suka ɗiga tsamansu akan abu tofa sai sun sameshi, tunda Nicky tayi ido huɗu da Zaid gaba ɗaya hankalinta yatashi, domin kuwa Zaid yayi mata hundred percent, bawani ɓata lokaci tabayyana masa soyayyarta a gareshi, Zaid kuwa dake ɗan izza ne saiya soma ja mata aji,, daga ƙarshe dai daya tabbatar da cewa itaɗin bata bibiyar maza sai ya amsa soyayyarta suka cigaba da shan love ɗinsu,,

Watarana Zaid yana kwance a ɗakinsa, sai ganin Nicky kawai yayi sanye da wani irin ɗan iskan kaya wanda yabayyana komai na surarta a fili, ganin da yayi mawa Nicky a haka baƙaramin ɗaga masa hankali yayiba, wata irin sha’awa yakeji mai ɗaga hankali, koda Nicky tafahimci haka saita yi amfani da damanta tasake ruɗa Zaid da irin salonta, jawo Nicky yayi jikinsa yashiga sun batarta tako ina, a rannan sheɗan yaribaci Zaid har yakusanci Nicky, tun da yake a duniya baitaɓa sanin ya daɗin Sex yake ba sai awannan ranan, baisan ya ƴa mace take ba shidai kallon su kawai yake, amma sai gashi yau yasani,, wani irin gamsuwa Nicky tasamu da Zaid a ranan wanda bata taɓa samun irin shi da ga wani ɗa Namiji ba,, tundaga Wannan rana Zaid yazama mashahurin ɗan iska kullum yana tare da Nicky suna aikata Zina, arana sai Zaid yayi Sex da Nicky sau Biyar,

Zaid mutum ne mai ƙyan ƙyami, shiyasa kwata kwata baya neman sauran matan turawa domin yasansu kowa buɗe ma ƙafa suke yashige,, Nicky ce kaɗai abokiyar watsewarsa, itama dan yafuskanci cewa bata mu’amala da kowani na Miji ne, sannu ahankali Zaid yasoma shan giya, koda Abid yafuskanci cewa abokinnasa ya soma baza iskancinsa, sai yasake haɗasa da wasu ƴam mata gangariya, aikuwa Zaid baiƙiba, nanfa iskancinsa yaci gaba da tumbatsa, haryazo ya fi ƙarfin Nicky, Ƙaurin isknacin Zaid har yaɗara na abokansa,domin ko Abid yanzu Zaid yafisa sanin kan mace da kuma iya iskanci,,,, duk wannan halin da Zaid ke ciki Dadynsa Alhaji Ma’aruf baisaniba, yanacan yasa harkan kuɗinsa a gaba, yakuwa mallaki dukiya masu mahaukatan yawa,, akwana atashi Zaid ya kammala degree ɗinsa, cikin ikon Allah kuwa yasamu kyakkyawan result, domin dai yanada ƙoƙari sosai, iskancinsa baisa yadaina karatu ba,, bawani ɓata lokaci Zaid yawuce London domin yin masters ɗinsa acan, hmmmm zuwansa London yaƙara masa iskanci sosai, shima Abid biyosa london ɗin yayi suka ci gaba da zuba iskancinsu acan,, Zaid yazama tantirin shu’umi idan yaga mace matuƙar tayi masa tofa saiyayi sex da’ita,, duk wannan tsawon shekarun da Zaid yaɗauka aƙasashen duniya, sauɗaya tak yazo Nigeria nanma satinsa biyu kacal ya tattara ya koma,,

Kwanci tashi Zaid yakammala Masters ɗinsa, take kuma wani Babban banki dake london suka nemi da yayi aiki dasu, sam bai amince da buƙatarsu ba, domin shi yafiso yayi kasuwanci, maƙudan kuɗaɗe Dadynsa yasanya masa wajen gina masa wani katafaren kamfani a London, shahararren kamfani aka gina masa na ƙera takalma da jakakkuna new styles, masha Allah cikin ƙanƙanin lokaci kamfanin Zaid ya shahara a faɗin duniya domin, kaya masu kyau da inganci suke bugawa,, Zaid yana karatu kuma yana kasuwancinsa harya kammala P.H.D ɗinsa, isakanci kuwa yaci uban na da,, wasa gaske saiga Zaid ya mallaki Company’s a ƙasa she da dama, lokaci ɗaya Zaid yayi wani irin mahaukacin kuɗi, baiyi ƙasa a guiwa ba ya dawo Nigeria yakuma gina wani kamfani’n da ake ƙera gyalelluka wato vails, tunda ya dawo Nigeria baisake komawa ko wacce ƙasa ba, domin yaji ƙasar tasa wato Nigeria tayi masa daɗi, company’s ɗinsa na ƙasashen waje kuwa, yasanya amintattun mutanensa suna kula masa da su……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button