NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Inaganin nan ɗin ma yayi ai basai munshiga ciki ba” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai gyara zamansa,

Harara Zabba’u ta ɓallamasa ƙasa ƙasa batare daya gani ba, a zuciyarta kuwa cewa tayi “Inbanda Allah yaɗigamin soyayyarka a cikin zuciyata, da mai zai sanyani tsayawa, har ka wulaƙantani “

Ɗago da kansa yayi ya kalleta, cikin muryan dakewa  yace “Ni zan wuce ”  

“Haba Yaya Sadeeq maiyasa kakemin hakane wai ? ko minti 30 fa bakayi da zuwa ba, amma kuma kace zaka tafi ” taƙare maganar tana kwaɓe fuska tamkar wata ƙaramar yarinya, ko kaɗan kuma hakan baimata kyau ba, domin kuwa shekarunta ya wucewa abun da take ƙoƙarin yi, (wannan saimu nida bestyna jikar Hajiya sweet 19,lol)

Hanu yasanya a cikin aljihunsa yaciro kuɗi, aje mata yayi akan table ɗin dake gabansu, haɗe da tashi tsaye yasoma tafiya,, ganin haka yasa Zabba’u daɗa ɓata fuska, cike da ƙuncin zuciya, tarufa masa baya.

Mai gadi na  buɗe masa gate yafice da motarsa, Zabba’u naganin fitansa, tasaki tsuka cike da takaici, wai ace kamar ita babbar yarinyar da maza suke mararin samunta, amma wai  ita wani ke wulaƙantawa, kwashe kuɗin da ya aje mata akan table tayi haɗe da sakai tayi shigewarta gida…

Zahrah kuwa ba’ita tafarka daga wannan baccin da takeyiba, sai ƙarfe 6 na yamma, lokacin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba, har zuwa lokacin kuma Khausar tananan bata tafi ba,,

Koda ta tashi a baccin, ji tayi gaba ɗaya tayi sakayau da’ita, a cikin kaso ɗari na ƙunci da damuwarta, babu kaso talatin,  Allahu Akbar haƙiƙa karatun Al’Qur’ani warakace ga duk wani damuwar zuciya, harma da ta rayuwa.

Matsowa kusa da’ita Husnah tasakeyi, cike da tausasawa takama duka hannayenta biyu,

“Bazan gajiya da faɗa miki ba Zahrah, yin imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, shi’ake so ga ko wani musulmin ƙwarai,  kuma Allah baya ɗaurawa bawa abun da bazai iyaba, idan kika ƙara haƙuri ki kaɗau ƙaddaranki, to ina mai tabbatarmiki da zaki samu kyakkyawan sakamako awajen ALLAH, haƙiƙa nasan Zayd ya cutar da rayuwarki, amma Allah bazai barshi ba, da sannu Allah zai saka miki,kimin alƙawari bazaki na yawan kukaba, sannan bazakina yawan damuwa ba, duk da nasan hakan abune mawuyaci, amma idan kika daure zaki iya,  sannan kuma kuka baya maganin damuwa, karatun Al’Qur’ani kaɗai zaki riƙa, insha Allahu damuwarki zata gushe, sannan kuma, kinyi kuskure Zahrah kinbari tarin damuwar da kika shiga, ya hanaki kai kukanki ga Allah, kin manta shine maikowa mai komai, dan Allah Zahrah kimin alƙawarin cewa zaki rage sanya kanki a damuwa, duk sanda wani tunani yake shirin zuwa miki, to ki gaggauta ɗaukan littafi mai tsarki, ki karanta hakan zai sanyamiki nutsuwa !!”  Husnah tayi maganganunta cikin lumana dakuma son sawa ƴar uwarta ƙwarin guiwa,,

“Bansan mai zance miki ba Husnah, amma haƙiƙa kinwuce ƙawa ke ƴar uwace, kuma koda a cikin ƴan uwanma keɗin ta da bance,  namiki alƙawari cewa zan maid komai nawa ga Allah, haƙiƙa rayuwata tana cikin ƙunci da kuma baƙin ciki, amma nasan babu a bunda yagagari Allah, kuma da sannu rayuwata zatayi haske, duk da banda tabbacin hakan !” Hawayene kawai ke tsiyaya daga idanun Zahrah, domin sosai takejin ciwon abun da Zayd yayi mata,  yanzu tayarda cewa dama haka Allah yatsara mata, kuma zata rungumi Ƙaddaranta, har Allah yakawo ma ta mutuwarta,, amma dudduniya bata taɓa jin matsanancin tsana ga kowa ba bayan Zayd,,

Sosai Husnah tabawa Zahrah shawara masu amfani, wanda zasu taimaka wajen cireta a damuwa,, saida akayi sallan Isha kafun driver’n gidan su Husnah yazo ya ɗauketa…

Tiryan tiryan Baffa ya ɗebi ƙafa, har ofishin Alhaji Umar, gaba ɗaya abun da yafaru da Zahrah, Baffa ya kwashe ya faɗa masa, bakaɗan ba hankalin Alhaji Umar ya tashi, domin kuwa shi Zahrah tamkar ƴa yaɗauketa, saboda mahaifinta yayi masa taimako sosai,  cikin faɗa da hargowa Alhaji Umar kecewa zai kai case ɗin koto,  saurin dakatar dashi Baffa yayi, haɗe da yagyara zama,    ban baki  Baffa yashiga yi wa Alhaji Umar, akan cewa kada yakai case ɗin kotu, domin kuwa yaron yafi ƙarfinsu, sannan kuma idan har aka kai case ɗin kotu, tofa sunan Zahrah ne zai sake ɓaci, wanda basusan an ma ta fyaɗe bama zasu sani, sannan kuma zata rasa mijin aure, domin wasu zasuce ba fyaɗe aka mata ba, ita takai kanta, kuma dole su zasukwan a ciki, domin basu da kuɗi, a yanzu yanda rayuwar duniyar nan  take,  mai kuɗi shine sarki,  kuma mai kuɗi shi kaɗaine mutum, haka wasu suka ɗauka, ko shari’a ake mai kuɗi shiyake nasara,,   sosai jikin Alhaji Umar yayi sanyi, domin kuwa tabbas maganganun da Baffa yafaɗa haka yake, kuma yasan duk kuɗinsa bai isa yaja da wanda suka fisa ba, domin shi ɗan ƙaramin mai arziki ne akan wasu…

((Sau dayawa akan cutar damu ƴaƴan talakawa,   amma bamu isa mu kai ƙara ba,  mune da gaskia, amma mu’ake bawa rashin gaskia, maiyasa ? saboda mu bamu da kuɗi, wanda bashi da kuɗi kuma ba mutum bane a wajenku ko?  anacin zarafin ƙananan yara dakuma ƴan mata,  amma ba a iya ɗauka musu mataki, saboda kawai wanda suka aikata abun masu hanu da shuni ne, mukuma an maidamu ko’oho, Allah sarki Allah ka’iyar mana, kabimana haƙƙinmu gaduk wani wanda yazaluncemu Ameen.))

    
        20/November/2019

    
       Voted, comment, and share please… Wattpad @Fatymasardauna
????????????????????????????????????????

       
           SHU’UMIN NAMIJI !!

      Written By
Phatymerhsardauna

Dedicated To My Lovely Brother Khabier

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

            WATTPAD
      @fatymasardauna

*( Masha Allah! ina matuƙar tayaki murnan kammala daddaɗan book ɗinki my sweetheart (Ladingo Ummu Fareesa) Allah ya baki ladan dake ciki, yakuma yafe miki kurakuran dakikayi aciki, haƙiƙa kinyi ƙoƙari sosai Sweetheart, kuma littafin HATSABIBIYA RAMLAT ya nishaɗantar, yakuma faɗakar, fatan mu Allah yaƙara miki basira da hazaƙa Ameen, ina miki fatan alkhairi My Sweetheart.)

Chapter 36 to 37

  A hankali yake tafiya da motarsa har yakawo ƙofar gidan,  dai dai tsayawur motar tasa, Baffa ya fito daga cikin gida.    

cikin hanzari ya ƙaraso inda motar Dr Sadeeq ɗin ke fake, “A’a likita kaine da yammacin nan haka ?” Baffa yafaɗa fuska cike da annuri,

“Eh wlh nine Baffa, tun safe naso zuwa, to aikine yayimin yawa ”  Dr Sadeeq yafaɗa yana mai ƙoƙarin fitowa daga cikin motar tasa.

“To muje nayi maka iso zuwa cikin gidan ko, aikuwa mutumiyar taka tanacan ta kulle kanta a ɗaki, tana karatu “

“Karatu kuma Baffa? badai ta dawo normal ba ?” Dr Sadeeq ya tambayi Baffa cikin sakin fuska, domin har yaɗanji sanyi a cikin zuciyarsa daga jin maganan Baffan,

“Ƙwarai kuwa likita, ai yanzu duk wannan hargowan kukan ta dainashi!” Baffa yafaɗa dai dai sanda suka kawo cikin gidan,

Da fari’a Inna ta tarbi Dr Sadeeq,  haɗe da baje masa tabarma a ɗan madaidaicin tsakar gidan nasu,   shima cike da mutum tawa ya gaida ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button