SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi, domin dudduniya a yanzu babu abun da zai ɗaga mata hankali kamar ace wai wani naƙiranta a waje, sam itakam tagama cire ƙauna da sake zuwa ƙiran wani, bata ƙaunarma koda sake fita waje ne,
“Wai ba magana nakeyimiki bane Zahrah kin shareni kuma bayan kinajina!” Baffa yafaɗa cikin faɗa faɗa,
Kuka Zahrah tafashe dashi haɗe da ɗago idanunta, ta kalli Baffa cikin muryan kuka tace “Baffa kataimakeni dan Allah, wallahi banso wani abu yasake faruwa da rayuwata !! “
“Ikon Allah, Malam kajita ko zata sake ɓarar mana da daman da muka samu na biyu, saikace akanta aka fara yin fyaɗe!” Inna tafaɗa cikin ɗaga murya,,
Da gudu Zahrah tajuya ta shige cikin ɗakinta haɗe da faɗawa kan gado tashiga rera kuka mai sauti, itakam batasan yanda zatayi da rayuwarta ba, batasan wasu irin iyaye bane Baffa da Inna, son zuciyarsu tayi yawa, kansu kawai suka sani, anya kuwa zasu rabauta da rahamar Allah ? cutar da maraya abune wanda ba kyau, kuma sunsani amma suke take saninsu, “Ya Allah kataimakeni !” tafaɗa cikin muryar kuka,
“Banni da’ita Salame nida itane, ai inbazata fita ba shi zaishigo cikin gidan ” Baffa yaƙare maganar yana mai nufar ƙofar fita daga gidan.
Dr Sadeeq ne tsaye a jikin motarsa yasha sky blue ɗin shadda sai tashin ƙamshi yake,
Baffa yafito fuska a sake kai tsaye yanufeshi, “Yauwa likita ka’iso saikuyi maganar acikin gida ko, kasan mutumiyar taka sai a hankali” Baffa yafaɗa still washe da baki, like namesake ɗina (fatiwasha lol), ba musu Dr Sadeeq yarufa masa baya suka shiga cikin gidan.
Yauma dai a tsakar gidan yazauna duk da cewa babu yawancin haske a tsakar gidan amma akwai hasken farin wata.
“Wai Zahrah bazaki tashi kije bane, nacemiki gashi yashigo har cikin gida, dan Allah Zahrah kada ki watsamana ƙasa a ido, kidubi girman mutumcin dayayi miki sanda kike ciwon hauka kitashi kije ” Inna tafaɗa cikin lallami.
“Ciwon Hauka kuma Inna?” Zahrah ta tambaya cike da mamaki domin dai ita a saninta batayi wani ciwon hauka ba,
“Ƙwarai kuwa kedai tashi kije kawai” Inna ta faɗa still cikin lallami, bawai don tasoba haka tasanya hijab haɗe da ficewa daga cikin ɗakin.
Tun fitowarta a cikin ɗakinnata ya kafeta da idanunsa, har taƙaraso can gefe dashi ta zauna, haɗe da takurewa waje ɗaya tana matsan ƙwalla,
“Saiyaushe zaki daina kuka ne?” Dr Sadeeq yatambaya cikin tattausar murya,
Shiru tayi bata amsa masa ba domin jin kalamansa take tamkar zuban narkakken dalma acikin kunnuwanta,
“Matsowa yayi gaf da ita, har tana iya jiyo ƙamshin turarensa, babu wani tsoro kokuma ɗar ya sanya hannayensa akan kumatunta yashiga share ma ta hawaye, sosai jikinta yaɗauki rawa domin tayi matuƙar tsorata da hakan,
“Banason kukanki Zahrah, nasani dole kina buƙatar ayi miki uzuri, kinajin ciwo da damuwa a cikin ranki, kuma kinada buƙatar kyakkyawan kulawa, kidaina min kallon wani bare kokuma na daban, kiyi mini kallon ɗan uwanki, wanda zaki iya gayawa damuwarki, inaso kifaɗamin duka damuwarki kinji ƙanwata, nasan zakiji sanyi idan kika faɗi ko kaɗanne daga cikin damuwarki !!” Dr Sadeeq yayi maganar cikin lallashi dakuma tausasawa,
Kuka takuma sanyawa mai sauti, domin kuwa tabbas abun daya faɗa ɗin hakanne, tana buƙatar mai kulawa da’ita, tana buƙatar ɗan uwa mai ɗaukar damuwarta, saurin ɗago da kanta tayi ta kallesa, sakamakon jin hannayensa da tayi akan nata,
Kai ya jinjina mata batare da yace da ita komaiba, yana kallonta tayi kuka harta ƙoshi, a hankali take sauƙe ajiyar zuciya, kofin ruwan dake gefensa ya ɗauka, haɗe da kawai bakinta, babu musu taɓuɗe baki ta soma sha, domin kuwa yanda zuciyarta ta bushe tana buƙatar ruwan,, saida tasha fiye da rabi kafun ta tsagaita da shan ruwan, sosai taji zuciyarta tasoma dawowa daidai nutsuwarta kuma yasoma sauƙa,,
“Yaushe zaki koma makaranta ?” Yajefomata tambayar kansa tsaye, kallon mamaki tabisa dashi, domin kuwa ko a wasan mafarki bata sake kawo sake zuwa makaranta acikin zuciyarta ba, itakam ai duk wani farinciki yawuce mata,
“Kada ki yarda da abun da zuciyarki takecewa, ba’akanki aka faraba, haƙiƙa abune mai ciwo amma idan kika daure zuciyarki, zaki iyayin rayuwar farinciki kamar kowa” Dr Sadeeq yafaɗa cike da son ƙarafafa mata guiwa,
“Kada kayi ƙoƙarin yaudarana domin kuwa sam banda wani sauran farinciki, yaruguzamin duk wani burina, to yanzu inaso kasanar dani shin menene amfanin karatuna bayan zuciyata cike take da ƙunci? kuma miye amfanin farincikina bayan rayuwata ke waye take da duhu ?, zanfaɗama damuwata domin nayarda dakai, inajin ciwo mai zafi a zuciyata bankuma san ranan warkewarsa ba, shin maiyasa zaka ce nayi farinciki bayan kasan cewa bazantaɓa samuba ?”
Ɗan gajeren murmushi yayi haɗe da matse hannayenta gam acikin nasa, “Saboda inada yaƙinin baki farinciki mai ɗorewa, amma saikin daina sakanki a damuwa “
Wani irin kallo tawatsa masa wanda yake nuni da cewa tana buƙatar ƙarin haske akan maganganun nasa.
“Zahrah ke yarinyace mai ɗauke da tarin ƙuruciya, kinaga yadace kibar rayuwarki tatafi a haka ?”
Dr Sadeeq yatambaya yana mai kafeta da idanu.
“Haka Allah yatsaramin, BAZAN BUTULCE BA, yadda da ƙaddara yana da kyau, NAYARDA DA ƘADDARA TA, saidai kuma bazan mantaba har abada, babu mai aurena, babu kuma mai tallafawa rayuwata, zanƙare rayuwata acikin ƙunci, idan har kaɗaukeni ƴar uwa kamar yadda kafaɗa, to inaso ka yi tunani shin wacce ta tsinci kanta acikin mummunar ƙaddara irin tawa akwai sauran farinciki da yarage mata?, ni yarinyace haryanzu bangama sanin rayuwaba, amma tabbas nasan mai kyau dakuma marar kyau, saboda haka rayuwata a gurɓace take, yariga daya ruguzata, bakuma zata taɓa kafuwa ta tsaya da ƙafafunta ba har abada, BANI DA ZAƁI likita amma akwai Allah ya isarmin komai!!” gaba ɗaya hawaye yagama wanke mata fuska, wannan karan ba iya zuciyarta bace tayi rauni hadda tashi zuciyar, lallai ƙaddaran Zahrah mummuna ce, amma kuma yazama dole yatsaya yakawar mata da duk wani duhu dake rayuwarta shi mai iya dawo mata da farincikin tane idan harzata amince, amma yasani Zahrah ta yanke ƙauna gaduk wani ɗa namiji,
“Likita ga abinci ko” Inna takatsemusu tunanin da sukeyi su dukansu.
Inna tana aje abincin tajuya tashige cikin ɗaki, kallonsa yamaida kan ɗan ƙaramin bakinta dake bushe, sannan yakuma maida kallonsa kan idanunta, a matsayinsa na mutum mai karantar yanayin ɗan adam, take yakaranci halin da take ciki, bayajin yunwa ko kaɗan domin saida yaci abinci kafun yafito, amma saboda dalili ɗaya yasa yajawo kwanon abincin gabansa, shinkaface ƴar gida jalof, ko mai batajiba ballantana albasa, amma haka ya share, yakai loman abincin cikin bakinsa, taunawar farko yaci karo da dutse amma haka dolensa ya basar (readers likitafa yagamu da girkin manya Inna, lol????).
“Zo muci” yafaɗa a taƙaice,
Saurin kallonsa tayi haɗe da girgiza kanta, domin ita yanzu abinci baya gabanta, damuwarta ma abincine a wajenta,,
Babu alamar wasa akan fuskarsa kaitsaye yanufi bakinta da hanunsa wanda yake ɗauke da ƙwayoyin shinkafa domin da hanu yakecin abincin,,