SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Saƙare haka tayi tanakallonsa domin wannan shine karo na farko a rayuwarta da wani ɗa Namiji ba muharraminta ba ya taɓa yunƙurin bata abinci a baki,
Kai tagirgiza masa alamar bataso haɗe da kawar da kanta gefe,
“Kinaso muyi faɗa kenan, kuma hakan nanufin baki ɗaukeni ɗan uwaba, nasan wunin yau bakisa komai a cikin kiba, sbd haka banason gardama, idan kuwa kikace bahaka ba, to akwai alluran da na taho da’ita, yanzu sainasa Baffa da Inna su riƙemin ke na yi miki har guda uku!! ” yaƙare maganar in a serious tone, aikuwa ya faɗar mata da gaba domin kuwa tsoron alluran da takeyi haryazarce tunanin mutane, “Haaaa” Dr Sadeeq yafaɗa still yana kusanta hanunsa ga bakinta, tamkar dai za abawa ƙaramin yaro abinci.
“Basaikabani ba zan iya ci!” Zahrah tafaɗa cikin raunanniyar muryarta,
“To ci ingani” Shima yafaɗa yana mai turo mata kwanon abincin gabanta, ahankali ta sa hanu ta tsakuri abincin, tamkar wacce akace ta tsakuro garwashin wuta da hanunta, daƙyar ta iya buɗe baki ta kai loman abincin bakinta, murmushi yayi haɗe da sanya hanunsa acikin kwanon abincin yasoma ci, duk da cewa ba daɗin abincin yakejiba, adole Zahrah take kai loman abincin bakinta bayanda ta’iyane kawai,,
Lomanta huɗu ta soma kwarara amai a wajen tamkar zata amayar da ƴaƴan hanjinta, miƙewa tayi daga tsugunen da take domin tasoma ɓata jikinta da amai, aikuwa wani irin jiri ne ya ɗe beta take ta faɗa kan Dr Sadeeq dashima yake yunƙurin tashi tsaye,, gaba ɗaya yatarota tafaɗa cikin ƙirjinsa, yayinda aman dake jikinta ya gogu ajikin kayansa,,
Da sauri su Inna da Baffa suka ƙaraso wajen domin tundaga ɗaki sukejin ƙaran amannata, “Lafiya likita maiyasameta kuma ?” duka suka tambaya cikin ƙosawa, da’alama dai sungaji da lamuranta.
” Bakomai inaga olsa (ulcer) ce kawai ke damunta ” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai ƙoƙarin shimfiɗeta a akan tabarman da suke zaune,
Saidai gaba ɗaya ba ƙarfi a jikinta, saboda haka duk ta narkemasa a cikin jiki, yayinda shikuwa zuciyarsa ke tsananta bugawa, addu’a yake a zuciyarsa Allah yasa ba abun da yake zargi bane ke damun Zahrah idan kuwa abun da yake zargine tabbas babban tashin hankali na gaba…
(Wani tashin hankali munbanu readers ????, Allah yasadai bacikine da ita ba, da Zaidu ya yi aiki mai tsada ???? )
Breakfast na baku kuji daɗinku
23/November/2019
*Voted, Comment, and Share please….follow me on Wattpad @fatymasardauna
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Lovely Brother Khabier
????Kainuwa Writers Association
{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
Chapter 38 to 39
A hankali Doctor ya kwantar da ita, cikin sanyin jiki yanufi motarsa don ɗauko jakarsa ta aiki, domin dama daga office yake yabiyo tagidannasu,, Allah yasa ba abun dayake hasashe bane yake shirin faruwa, lallaiko idan har ya zamana Zahrah ciki ne da ita, to fa shikansama yashiga tashin hankali, bawai ita kawai ba, domin yasan ɗan guntun tsarin daya shirya rugujewa zaiyi, to ina kuma ga Zahrah wacce bata gama warkewa daga ciwon dake jikinta ba, kuma ace taƙara faɗawa cikin azabar wani ciwon, tabbas yasan tashin hankalin da zata shiga sai ya take wanda tashiga a baya,, jiki a saluɓe haka Dortor Sadeeq yadawo cikin gidan, zuwa lokacin har Inna ta ɗauketa takaita cikin ɗaki.
Tana kwance akan ƴar katifarta, sai faman sauƙe numfashi take a hankali, dagani kasan aman da tayi ya galabaitar da’ita sosai, zama yayi gaf da’ita, haɗe da kama hanunta, lokaci guda yaji jikinta yaɗau zafi sosai, kayan aikinsa dake cikin jakarsa ya ciro ya fara yi mata ƴan gwaje gwaje,
Wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe sakamakon gano abun dake damun Zahrah da yayi, duk da cewa baiyi mata gwajin ciki ba, amma a iya ɗan bincikensa da yayi ya gano cewa bata ɗauke da ciki, ulcer ce kawai tayi mata mummunan kamu, sakamakon yunwa daya samu mazauni acikin cikinta.
Kallonsa yamaida kan Baffa haɗe da cewa ” Bawani babban damuwa bane ulcer ce, yanzu zanje na ɗauko wasu allurai a asibiti sainazo nayi mata, insha Allah komai zaiyi dai dai”
“To likita Allah yayi albarka muna godiya sosai !” Baffa yayi maganar cike da yabawa ƙoƙarin Dr Sadeeq.
Miƙewa Dr Sadeeq yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, yana fita su Inna ma suka mara masa baya.
Kwanciya tayi lamo tamkar wacce ruwa ya ƙare mawa a jiki, gaba ɗaya jinta takeyi bata da kuzari, gawani irin zafi da ƙuna da ƙirjinta keyi mata,,
Koda Dr Sadeeq ya ɗauko magunguna da Alluran da yakamata ace yayi mata, sai da ya biya ta wani katafaren wajen sai da kayan marmari yasaya mata dangin su apple da su inabi hadda abarba, bai tsaya anan ba hadda fresh milk saida yabiya ya saya, gudu yashiga sharawa akan titi, burinsa ɗaya shine yaje yabata taimako mai kyau, sosai yakejin tausayinta, saboda ta cancanci a tausaya mata, daga wani ɓangare na zuciyarsa kuwa idan yatuno da cewa ba ciki bane da’ita, sai yaji wani irin sanyi da nishaɗi na ratsa zuciyarsa, wanda ya alaƙanta hakan da cewa bayason tasamu ciki saboda zata sake shiga wani hali marar daɗi. (kuji shifa???? wai hakane reaɗers?)
Mintuna ƙalilan ya iso ƙofar gidannasu.
Koda yanemi Inna da tayi masa iso zuwa ɗakin Zahrah’n, cewa tayi yashiga kai tsaye ai anzama ɗaya su yanzu ɗan uwa suka ɗaukeshi (hmm)
Yanda ya barta haka yataradda ita sai dai yanzu idanunta a lumshe suke, “Zahrah!!” yaƙira sunanta dai dai lokacin da yake ƙarasawa kusa da’ita.
A hankali ta buɗe idanunta tasauƙesu a kansa, ɗan guntun murmushi yayi mata, wanda yasanya gabanta mugun faɗuwa, domin kuwa murmushin nasa yatuna mata da murmushin Oga Babba (ZAIDU manyan maza, lol), take taji wani irin abu ya toshe mata maƙoshi, yayinda zuciyarta tayi ƙunci.
Aje ƙatuwar ledan dake hanunsa yayi, haɗe da zama akan katifarta ta, “Tashi ki zauna” yafaɗa yana mai kafeta da ido, kai kawai ta girgiza masa alamar bazata iya tashi ba, ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya ɗagota zaune, duk da cewa yana matuƙar jin shock idan yataɓa jikinta, amma babu yanda zaiyi dole hakan shine mafita.
Ledar daya shigo da’ita ya buɗe, haɗe da ɗauko apple guda ɗaya ya miƙa mata, kallonsa kawai tayi haɗe da kau da kanta gefe,
“Magani bazaiyi aiki a jikinki yadda ya kamata ba, harsai kinci abinci, idan kuwa kikasha magani bakici abinci ba zai wahalar dake sosai, dan Allah banason gardama Zahrah, nasan kuma kema kina buƙatar abinci, don haka ki karɓi apple ɗinnan kici, ciwon ulcer bazai taɓa sake kiba matuƙar kina zama da yunwa!!” yaƙare maganar cikin lallashi.
Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da ɓata fuska, sam batason cin wani abu daga garesa, amma yana ƙoƙarin tursasata dole, kuma yayi gaskia dayace tana buƙatar abinci, tabbas ita kanta tasan tana buƙatar abinci.