NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Yauwa Zahrah nasan dama keɗin maijin magana ce, karɓa kici ko!” yaƙare maganar yana mai marairaice fuska, haɗe da kusanto da apple ɗin dai dai saitin bakinta.

Hanu tasa ta karɓi apple ɗin, a hankali take gutsuran apple ɗin kamar mai gutsuran magani, duk  da kuwa cewa taji test ɗinshi a cikin bakinta,,   tana cinye apple ɗin ya miƙo mata goran fresh milk mai sanyi.

“Ungo wannan ma ko kaɗanne kisha, nasan zai taimaka kuma idan kika sha bazanmiki allura ba!”

Saurin kallonsa tayi, don tabbatar da abun da ya faɗa, aikuwa idan dai har bazai yi mata allura ba idan tasha, to lallai zatayi ƙoƙari tasha ɗin,

“Ka tabbata bazakamin alluraba idan nasha?” tafaɗi maganar a sangarce, cikin kuma yanayi na marar lafiya,

“Bazan miki allura ba Zahrah, idan dai harkika sha, kuma koda zan miki ma kaɗan zanmiki kuma bamai zafi ba!” yaƙare maganar yana murmushi.

Take tasake turɓune fuska haɗe da turo baki.

“Nifa wasa nake miki bawata allura dazan miki !” Dr Sadeeq yafaɗa yana dariya ƙasa ƙasa.

Karɓan goran fresh milk ɗin dake hanunsa tayi, haɗe da kafa kanta tasoma sha, tun asalinta ita mai son madara ce, haka kuma fresh milk yana ɗaya daga cikin abubuwan da takeso, sabo da haka sosai tasha har saida taji cikinta yacika, take kuma  ɗan kuzari yasoma dawo mata, miƙo masa goran tayi alamar taƙoshi,

“Kishanye duka” yafaɗa a taƙaice,

“A’a naƙoshi” itama tabasa amsa ataƙaice,

“Okay to mai kikeson ci yanzu kuma?”  yatambaya yana mai tsareta da idanu.

“Babu” ta basa amsa a taƙaice,

Kansa kawai yajinjina haɗe da ɗauko drugs ɗin daya taho mata dasu yasoma ɓarewa yana bata, sai ta rufe ido haɗe da ƙanƙame jiki sannan take iya sha, shiko dariyama take basa, bai taɓa ganin mai tsoron allura da magani kamarta ba.

Yana gama bata maganin yace ta kwanta, batayi ƙoƙarin musa masa ba, ta kwanta domin kuwa kafun yace mata kwantan, idanunta harsun fara rufewa,, “Zahrah!” yaƙira sunanta, shiru babu amsa kuma bata ko motsaba sai idanunta da suke buɗewa suna rufewa a hankali, da’alama dai yabata wani magani ne mai matuƙar kashe kuzarin jiki.

Dariya yayi ƙasa ƙasa haɗe da cewa “Yarinta da daɗi” 

zuƙa zuƙan alluran daya taho dasu guda biyu, yaciro acikin ledan haɗe da haɗa komai da komai wanda ya kamata, 

Riƙe alluran yayi a hanunsa haɗe da mai da kallonsa ga Zahrah wacce take kwance lamo, a hankali yasanya hanunsa ajikinta haɗe da juyata,  saida ya rumtse idanunsa shima kafun ya’iya yi soka  mata alluran,  yana gamawa ya juyata ɗaya gefen ma yayi mata, sosai taji zafin alluran amma bata da bakin magana, sai dai hawaye da suka soma gangara daga cikin idanunta.

“kiyi haƙuri Zahrah ƴan mata, dolece tasa namiki alluran, inaso naga kinsamu lafiya ne!” Dr Sadeeq  yafaɗi maganar cikin tausasa murya, bayan yashare mata ƙwallan dake sauƙa a gefen fuskarta,  miƙewa yayi tsaye haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, bayan yatattara kayan aikinsa.

Bai taradda Inna a tsakar gida ba sai Baffa, don haka a gurguje yayi masa sallama, yatafi sbd dare yasoma rabawa.

Ɓangaren Zahrah kuwa tun kafun Dr Sadeeq yafita bacci yayi awon gaba da’ita, domin daga magungunan har alluran da yayi mata suna saka bacci.

A hankali yake tuƙin motar tasa, fuskarsa cike take da annuri, Situation ɗin Zahrah kawai yake tunawa, sosai komai nata yake burgesa, musamman ma tsoronta,  hakanan yakejin kansa cikin nishaɗi idan yana tare da’ita, baikumasan dalilin faruwar hakanba.

Koda ya yi parking motarsa kai tsaye ɓangaren mahaifiyarsa ya nufa, domin yau ko gaisawa basuyi ba ya fice daga gidan,

Koda yashiga falonnata bai isketa ba, don haka kaitsaye yanufi bedroom ɗinta domin yanada yaƙinin cewa zai taradda ita acan.

Knocking ƙofar bedroom ɗinnata yashigayi a hankali,   jin knocking ɗin ya tsananta ne yasa taba wa mai knocking ɗin umarnin shigowa, domin dama tana da yaƙinin cewa shiɗinne kasancewar taji ƙaran shigowar motarsa cikin gidan.

Zaune ya’isketa akan sallaya, da’alamu idar da sallan nafilanta kenan.

Harƙasa ya durƙusa ya gaidata cike da girmamawa,  cikin sakin fuska itama ta amsa masa gaisuwarsa haɗe da cewa ” Ina kashigane yau tunsafe ?”

Ƙeyarsa yashiga sosawa a hankali, yayinda fuskarsa ke ɗauke da ɗan murmushi.

” Am Hajiya aikin office ne ya ɓoyeni, dana tashi kuma sai na biya ta gidansu Zahrah domin duba jikinta, to danaje sai nasamu batajin daɗi !” ya faɗi maganar fuskarsa ɗauke da  alamar damuwa.

“Gidansu Zahrah kuma Sadeeq ?, to Allah ya sauwaƙa, a kwai a binci, a derny saika ɗebi iya yanda zaka iyaci, domin daganinka bakasa komai a cikin ka ba” Hajiya tafaɗi maganar cike da kulawa,

“To Hajiya zanci insha Allah” yaƙare maganar yana me miƙewa tsaye,  sallama yayiwa mahaifiyartasa kafun yasakai yafice daga cikin ɗakin.

Yana fita Hajiya tasaki ƙwafa haɗe da cewa
“Nasan maganinka aure zanyimaka ko da baka shiryaba, natabbatar hakan zai sa ka rage yawan kaiwa dare a waje, kullum kai baka da hutu aiki tamkar engine, duk kuma rashin iyali shiya jawo hakan “.

Yana isa ɗakinsa yasoma rage kayan jikinsa, ɗan ƙaramin towel ya ɗaura haɗe da faɗawa bathroom yasakar mawa kansa shower,   cikin zuciyarsa kuwa cunkushe take da tarin tunanuka kala kala, haƙiƙa yasan cewa yana buƙatar mace akusa dashi, domin dai shiba dutsi bane da zai zauna haka ƙiƙam ko da yaushe, dole yana buƙatar wacce zata na taimakawa wajen enjoying life ɗinsa,  tun ba yauba yagane cewa yana ɗaya daga cikin maza masu yawan buƙata,  amma kuma sosai yake ƙoƙari wajen shan pills wanda zasu sama masa relief,   a gurguje yayi wankan yafito, wata brown ɗin jallabiya mai kyau yasanya bayan yatsane ruwan dake jikinsa,    kulan abincin daya ɗauko a falon Hajiyarsa yajawo haɗe da buɗewa, jallof ɗin shinkafa ne sai coslow, kaɗan ya tsakura a cikin plate  yasoma ci,  gaba ɗaya tunanin Zahrah yacika masa zuciya wani irin feeling yakeji a kanta,  idan yatunota sai yaji nishaɗi ya sauƙa acikin zuciyarsa,  yanason komai nata, idan tana kuka tanayimasa kyau sosai, haka ma idan ta kwaɓe fuska bakaɗan ba take kyau, gaskia tana da abubuwan burgewa da yawa,   da tunaninta yasamu ya kammala cin abincin duk da cewa baiwani ci mai yawa ba, saida yafita ya ɗanƴi exercise kafun ya dawo ya kwanta, domin a matsayinsa na likita yasan illan dake cikin kwanciya daga cin abinci..

Washe gari

Alhamdulillahi tatashi da ƙarfi a jikinta, sai dai ɗan abun da baza a rasa ba, tun tashinta da haushinsa ta tashi,  domin jiya tanaji tana gani haka ya yaudareta yayi mata allura, bayan yagama kashe mata jiki da ƙwayoyin da ya bata,   don haka bakinnan a ɗane yake ita adole tana fushi da likita.

Kasancewar yau Asabar babu aiki, yasanya bai tashiba harsai 9 na safe,  wanka yayi yashirya cikin kaya masu kyau haɗe da baɗe jikinsa da daddaɗan turare, motarsa yanufa direct bayan yafito daga ɓangaren Hajiyarsa,   JABI LAKE yanufa inda yayiwa Zahrah siyayya sosai.
(hmm readers kunaga zaƙewar doctor batayi yawa ba kuwa ????)

Yaukam har zauren cikin gidan yashiga anan yatsaya yasoma kwaɗa sallama,  Cike da zumuɗi Inna dake zaune a tsakar gida tasoma amsa sallaman nasa, domin tasan bazai shigo hanu rabbana ba, sauran kayan maƙulashen da yasa yawa Zahrah jiyama ita tacinyesu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button