SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Iso mana likita, ai dakazo kawai ka iso, bawani nuƙu nuƙu nanma fa gidan kune !!” Inna tafaɗa fuska a sake,
Ɗan murmushi kawai Dr Sadeeq yayi haɗe da ƙarasa shigowa cikin gidan, akan tabarma ya zauna kamar koda yaushe,
Yana zama Zahrah tafito daga cikin banɗaki, daga ita sai ɗaurin zani a ƙirji sai kuma ƴar ƙaramar lufaya dake jikinta, kallo ɗaya zaka mata kasan cewa daga wanka take, saurin ɗauke idanunsa yayi daga gareta, yayinda ita kuma tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, sam bata zaci ganinsa ba awannan lokacin. Sumi sumi haka ta raɓa tashige cikin ɗakinta.
Bayan sungama gaisawa da Inna ne ya yayi shiru haɗe da sunkuyar da kansa ƙasa, sarai Inna tasancewa wajen Zahrah’n yazo don haka kai tsaye tace masa yashiga yasamu Zahrah’n aciki.
Shikam harga Allah bayason shiga ɗakinta, domin kaɗaituwar mace da namiji a waje ɗaya hatsarine, amma ya ya’iya tunda yalura cewa iyayen riƙonnata ƙaramin tunani garesu.
Tsaye take atsakiyar ɗakin, saka rigarta kenan ko zip ɗin rigarma bata gama jaba, jin sallamansa yasa tayi saurin dawo da kallonta bakin ƙofar, harta fara zaton ko kunnenta ne yaji hakan ba sallamarsa bane, sai kuma taga yashigo cikin ɗakin, da sauri ta matsa jikin bango ta manne bayanta, domin gaba ɗaya bayanta a waje yake,
“Uh sorry nashigo kinasa kaya ko” Dr Sadeeq yafaɗa yana mai kallonta.
Harara ta gallamasa haɗe da turo bakinta gaba, dagani kasan fushi take.
Dariya yasanya harsai da fararen haƙwaransa suka bayyana,
“Fushi kikeyi dani ko?, to ai balaifina bane, dolece tasa nayi miki alluran don ki samu sauƙi, yanzuma kuma wasu alluran nazo nayi miki” yafaɗa yana gimtse dariyarsa.
Kuka Zahrah tasanya haɗe da sake matsewa ajikin bango,
“Dan Allah kada kamin, banason allura kataimakeni!” tafaɗa cikin muryar kuka da tsoro.
“Shiiii kada kitaramana jama’a madam, ni ba allura zanmiki ba wasa nake miki ” Dr yafaɗa yana mai ɗaura yatsansa ɗaya akan laɓɓansa alamar tayi shiru.
“Ni bazansake yarda dakai ba, ai jiyama cewa kayi ba allura zakaminba, amma kuma shine kabani wani abu nasha kamin, ni bazan sake yarda dakai ba!” Zahrah tafaɗa tana matsar ƙwalla daga idanunta.
“Hahhh to ya’isa haka yanzu kam dagaske ba allura zanmiki ba, juyo na jamiki zip ɗin kinji ƴar ƙaramar ƙanwata !” Dr Sadeeq yafaɗa cikin tsokana,
“Dan Allah kafita banaso, zanzo na sameka, domin ni ba wani namiji da zai sake taɓamin jiki ehe !” Zahrah ta faɗa cike da shagwaɓa.
Wani irin zubawa tsikar jikinsa yayi, domin yanayin yanda tayi maganar kaɗai ya isa sanya jarumin namiji faɗawa cikin wani yanayi,
(Hahhhh likita bokan turai, to Zaid ma yafaɗa a wani hali, balle kai da bakasan salon mace ba ????)
(Manage yau baida yawa sosai bacci nakeji kuma dama banda enough charge, wata acikin ku tataimaka ta tsammin charge pls ????.)
25/November/2019
Voted, Comment, and Share please. Follow me on Wattpad @fatymasardauna
1:58 pm
????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
phatymasardauna
Dedicated To My Lovely Brother Khabier
????Kainuwa Writers Association
{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
( My Lovely, My Sweetness, My Happiness, My Best Friend ever, inasonki sosai da sosai ƙawata rabin raina, wannan page ɗin gabaki ɗayansa kyautane a gareki HAUWA Kulun MAJADAN ????, JIDDATUL HUSSARY kiji daɗinki ki mo re ƙawata takaina HOUWER )
Chapter 40 to 41
Nannauyar ajiyar zuciya Doctor ya sauƙe, haɗe da zura hannayensa a cikin aljihun wandon sa, “Shikenan to tunda kince haka, na baki two minute kacal kisameni a waje, idan kuwa bakifitoba zan dawo na sake iskeki, kuma wlh sai na danneki na jamiki zip ɗin da ƙarfin tsiya” dagajin yanda yayi maganar kasan cewa tsokana ce kawai.
Kai kawai ta iya jinjina masa alamar cewa taji zata fito ɗin,
Ɗan gun tun murmushi Dr yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin.
Yana fita ta sauƙe nannauyar a jiyar zuciya, haɗe da sanya hanunta a bayanta, taƙarasa jan zip ɗin rigarta, zunbuleliyar hijabinta ta zura akan rigar haɗe da ficewa daga ɗakin, saboda tasan idan bata je bama tabbas zai biyota.
Zaune ta iskesa a cikin rumfar dake barandar gidan nasu, can gefe dashi ta zauna haɗe da kawar da kanta gefe domin kuwa ta lura gaba ɗaya idanuna akanta suke,
“Banason wasa matso kusa kisha maganinki !” yafaɗa babu alamar wasa akan fuskarsa.
Ɗan ƙaramin bakinta tacunno gaba haɗe da sake ɓata fuska, Allah ya sani ta tsani magani sosai da sosai, batama so ayi mata ko da zancen magani ne.
Batare da ya sake ce da ita komaiba yashiga ɓallo ƙwayan maganin daga jikin tablet ɗinsu, yana sawa a hanunsa, har sai da yagama ɓare iya wanda zatasha a yau ɗin, miƙo mata maganin yayi haɗe da bata goran ruwa,
Fuska a daƙune haka ta karɓi magananin saida ta rumtse idanunta sosai kafun ta iya haɗiye maganin, gashi dama irin magani mai ɗacin nan ne,
“Kishirya next week zaki koma makaranta ” Dr Sadeeq ya faɗa yana mai latsa wayar da dake riƙe a hanunsa, bakuma alamar wasa akan fuskarsa.
Saurin dawo da kallonta garesa tayi, haɗe da girgiza kanta, “A gaskia ni bazan sake komawa makaranta ba !” Zahrah tafaɗa cikin ɓata rai,
“Maiyasa ? ” Dr Sadeeq ya tambaya kai tsaye.
“Saboda babu amfanin hakan, ana karatune don a inganta rayuwa, to nikuma tawa rayuwar tajima da rugujewa, mai yasa zanɓata lokacina wajen gyara abun da bashi da kyau, bakuma zai gyaruba, na haƙura da komai zanjira mutuwata kawai !” Zahrah taƙare maganar cikin yanayi mai nuni da cewa zuciyarta tagamayin rauni,
” Idan ginin gida ya ruguje, ƙoƙari ake a sake gyarasa, akuma sabuntasa har yafi nada ɗin daya ruguje kyau, da kuma ƙawatuwa, shin kinsan maiyasa ake yin hakan? ” Dr Sadeeq ya tambayeta bayan yamai da gaba ɗaya nutsuwarsa gareta.
“A’a” tafaɗa a taƙaice.
“Saboda yanada matuƙar amfani gamasu shi, sannan kuma yana da kyau idan karasa dama ta farko, kasake neman wata damar, domin sau dayawa anasamun nasara ne a gaba, bawai a farko farko ba, idan kika ci gaba da kashewa kanki ƙargin guiwa, to zuciyarki zata zama mai tsananin rauni, babu amfani idan kikace bazaki inganta rayuwarki ba, amma inaso kisanar dani fa’idan yin hakan, nuna kin yarda da ƙaddara yana ɗaya daga cikin mantawa da komai, idan kika zauna a gida, bazaki taɓa samun cigaba ba, nasan abun da Zaid yayi miki har yau yana cikin zuciyarki, kuma inada tabbacin cewa idan kinsamu wadataccen ilimi nan gaba, zaki iya yaƙi da azzalumai irin su Zaid, please Zahrah kada kicemin a’a, nayi hakanne saboda samamiki sauƙi, da kuma cireki a kaɗaici !” Dr Sadeeq yaƙare maganar cikin muryan tausasawa, dason ƙara mata ƙarfin guiwa.
Hawayen da suka shiga ambaliya akan fuskarta ta sanya hanu ta share
” Yar zuwa yau banajin akwai wani sauran farinciki daya ragemin a gaba, da wani ido mutanen duniya zasu kalleni? wasu zasu ɗauka cewa ni nakai kaina garesa, wasu zasumin dariya wasu ko zasumin Allah ya daɗa, babu wani namiji da zai tunkareni da sunan soyayya, rayuwata a yanzu tana gudana ne tamkar ruwan shayin da aka sa ma sa lipton amma ba asanya sugar da madara acikin saba, dan Allah kada ka matsa akan cewa lallai saina koma…..”