SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Lovely Brother Khabier
????Kainuwa Writers Association
{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
Chapter 42 to 43
Suna fita kuwa ta iske Baffa yayi ɗare ɗare agaban motar Dr Sadeeq sai washe haƙora yake kai kace anmasa kyautar ƴan kuɗaɗe ne.
Dakansa ya buɗe mata murfin motar ɓangaren gidan baya, cikin sanyin jiki ta shiga cikin motar, kaitsaye yashige ɓangaren driver haɗe da mawa motar key…
Tunda suka ɗau hanyar makarantar tasu Baffa ke faman zuba kamar wani kurna, yayinda Doctor Sadeeq ke amsa masa jefi jefi, domin hankalinsa gaba ɗaya yana ga Zahrah, wacce ke zaune tayi jigum a gidan baya, akai akai yake satan kallonta tacikin madubi..
A haka dai harsuka iso cikin makarantar tasu, dai dai bakin ƙofar hall ɗin da zasu gudanar da lecture yau, ya yi parking motar tasa, domin dama already ansanar dashi cewa yau a wannan hall ɗin zasu gudanar da lecture.
A hankali ta buɗe murfin motar ta fito kafaɗarta ɗauke da jakar makarantar ta, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa ta nufi cikin hall ɗin kai tsaye, ko wai gensu batayi ba, tanashiga hall ɗin kallo yadawo kanta, take taji wani irin muguwar faɗuwar gaba haɗe da karyewar zuciya, gani take tamkar kowa yana ganin abun da yafaru da ita rubuce akan goshinta.
Karab idanunta suka sauƙa akan Husnah wacce take faman aikin haɗa wasu takardu dake gabanta. wani irin sanyi taji zuciyarta tayi sakamakon ganin husnah, domin kaf makarantar bata mu’amala da kowa bayan husnah, da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah, domin koda wasa batayi tunanin ganinta ba.
“Kamar mafarki nakeyi gaskia naji daɗi sosai ƙawata!” Husnah tafaɗa cike da tarin farinciki.
Zama sukayi a tare dai dai lokacin Sir Bature yashigo cikin hall ɗin, tsit haka ajin ya ɗauka ana ta sauraran lecture ɗin dayake yi musu, a zahirin gaskia tanajin abun da yake cewa, amma kwata kwata bata fahimtarsa, awa biyu suka ɗauka chur suna lecture, kafun daga bisani yafita daga ajin, gyara zama Husnah tayi haɗe da mai da kallonta ga Zahrah cike da kulawa tace ” Yanzu ina likitan yake ?”
Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa ” Ba maganar Doctor bace damuwata Husnah, babban damuwata shine gani nake tamkar abun da Zaid yamin yana rubuce a gaban goshina, Husnah gani nake tamkar kowa yasan abun dake damuna !” Zahrah taƙare maganar cikin raunin zuciya.
” Kada kice haka Zahrah, babu wanda yasan abun da yafaru dake, kada ki ɗaga hankalinki ƙawata kinfasan kowa da irin tasa ƙaddaran, kuma zuwa yanzu na tabbatar kin mai da al’amuranki ga Allah, shima Zaid nasan kinbarsa da Allah “
Murmushi mai ciwo Zahrah tayi haɗe da kallon ƙawarta ta, cike da ƙuna tace ” Banda wata hanya wanda tawuce barinsa ga Allah, nasan nan bada jimawa ba Allah zai bimikin haƙƙina ” taƙare maganar cikin raunin zuciya,
Hannayenta Husnah ta kama suka fice daga cikin ajin, kai tsaye cafeteria suka nufa don cin abinci. Balaifi sosai tasamu nutsuwa a yau ɗin domin kuwa Husnah bata barta tayi kaɗaici ba. Ƙarfe 5 dai dai suka fito daga cikin lecture ɗin ƙarshe na ranan yau ɗin, kasan cewar ta kwana biyu bata zo makarantar ba, sai take jinta gaba ɗaya duk ta gaji, cikin nutsuwa take takunta yayinda kanta ke duƙe a ƙasa, ba abun da zuciyarta keyi banda bugawa, gaba ɗaya tsoron fita daga cikin school ɗin takeyi, gani take tamkar tana fita za’a kamata, da ƙyar take iya ɗaga ƙafafunta, dagani kasan bason tafiyar take ba. a hankali ta matsa gefe, haɗe da waigowa don ganin waye wannan ya matsa mata da horn ɗin motarsa, karab idanunta suka sauƙa akan sa, kasancewar gilasan motar tasa gaba ɗaya a sauƙe suke, sam batayi tsammanin ganinshi ba, murmushi yasakar mata haɗe da cewa ” Da baki matsaba ai dana take ki !” yafaɗi maganar cikin yanayin tsokana, ɗan guntun murmushi itama tayi haɗe da taɓe baki, “ai idan haka ta kasance zanfikowa jin daɗi ” Zahrah tafaɗi hakan da iya gaskiyarta.
“Shigo mutafi!” yafaɗa cikin tsare gida.
Saurin kallonsa tayi bakinta ɗauke da tarin tambayoyi, amma kuma takasa koda motsa bakinta ne balle ta furta wata kalman.
“Kintsaya kina kallona, ba dole idan bazaki bini ba, saina yi tafiyata!” yaƙare maganar yana mai niyar tada motar tasa.
Da sauri ta zagaya haɗe da buɗe murfin motar, gefen mai zaman banza ta shiga haɗe da tamke fuskarta tamau tamkar wanda yagayamata magana marar daɗi.
Da ƙyar ya iya ɓoye dariyan dake cinsa, domin kuwa tsoro ya hango ƙarara akan fuskar Zahrah, “Naɗauka ai zakijamin ajine, da sai na tafi na barki ba ruwana!” yafaɗi hakan cike da shauƙi.
Harara ta watsa masa haɗe da sake turo baki gaba, cike da shagwaɓa wacce batasan tayi ba tace “Nifa idan surutu zakamin ka sauƙeni nayi tafiyata”
Yanzu kam kasa ɓoye dariyarsa yayi saida ya dara kafun ya ce ” Bazan sauƙe kiba ai bani na ɗauko ki na saki ba, zaki iya fita da kanki ma, ai nasan ke jaruma ce zaki iya kare kanki ako da yaushe, har ma zaki iya shiga cikin ko wani abun hawa da ƙwarin guiwarki !”
Saurin kallonsa tayi domin kuwa sarai ta fahinci inda maganganunsa suka dosa, wato dai shima ya hango zallan tsoron dake kwance akan fuskarta.
“Shikenan tunda haka kace” tafaɗi maganar tana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar ta fita.
“Haba ƴar ƙanwata, nifa wasa nake miki, kiyi haƙuri ki bari na kaiki gida kinji ko!” Doctor yafaɗi maganar cikin lallashi, domin yafahimci cewa saurin fushi ne da’ita.
A cikin zuciyarta tayi hamdala, sakamakon hanata fita daga motar da yayi, domin dama burga ce kawai tsoron dake cikin zuciyarta bazai barta ta iya tafiya ba, duk runtsi tafiso shiɗin ya kaita domin tafi yarda dashi fiye da kowa a yanzun..
Kwantar da bayanta tayi akan kujeran motar haɗe da lumshe idanuwanta, gaba ɗaya jinta take a gajiye, ga wani irin ciwon kai dake damunta, a hankali take buɗe idanunta, a zabure tatashi zaune sakamakon ganin da tayi Doctor ya nufi wata hanyar da ita saɓanin hanyar gida.
“Inazaka kaini !” Tafaɗa a razane, kuma cikin yanayin tsoro,
“Saidake zanyi!” Yayi maganar babu alamar wasa akan fuskarsa.
“Dan Allah kayi haƙuri ka sauƙeni, ka barni naji da duhun dake cikin rayuwata, kada ka ƙaramin wani bala’in dan Allah!!” tuni hawaye sungama wanke fuskarta.
Wani irin kallo Doctor yayi mata haɗe da sakin murmushi bai kuma sake ce da ita komai ba, saima maida hankalinsa da yayi ga tuƙin da yake,
Yanzukam kuka mai sauti ta sanya haɗe da soma cewa ” Dan Allah kada ka sake cutar da rayuwata, zan iya amincema ka kasheni amma bazan iya jure wa ba, idan kaci mutumcina, wlh na yarda ka wurgani kan titinnan mota ta taka ni, amma dan Allah kada kamin komai!!” taƙare maganar cikin matsanancin kuka mai taɓa zuciya. Daidai lokacin suka iso gaban wani makeken mall wanda yagaji da ƙawatuwa,
yana parking motar baiko kalletaba yayi saurin ficewa daga cikin motar haɗe da dannawa gabaki ɗaya ƙofofin fita a motar luck, domin yasan dole zatayi ƙoƙarin fita daga cikin motar,