SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Kuka sosai Zahrah keyi haɗe da sanya ƙarfinta tashiga dukan glass ɗin motar, tana mai ihun neman taimako amma babu kowa a wajen balle tasaran za a temaketa, domin kuwa wajen parking space ne.
“Ashe duniya cike take da azzaluman maza, ashe itakam rayuwarta a haka zata ƙare? wayyo Allah itakam ƙaddaranta kenan” abun da take faɗa kenan acikin zuciyarta tana kuka mai tsuma zuciya,domin a zaton ta hotel ya kawota zai kuma lalata mata rayuwa.
Daidai lokacin Doctor Sadeeq ya dawo hanunsa ɗauke da manyan manyan ledodi guda biyu, yana shiga cikin motar yakuma danna mata luck haɗe da mawa motar key da gudun gaske ya hau titi.
Zahrah kam muryanta har ya dashe kukanma harya daina fita domin gaba ɗaya ta gama sadaukar da cewa yau ce ranar mutuwarta, kukantane yasoma tsagaitawa ganin sun nufi hanyar unguwarsu, a hankali hawayenta suka daina zuba, yayinda tashiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, bakomai yasa hakanba face ganinsu da tayi sun shigo cikin unguwarsu tsulum, a bakin ƙofar gidan nasu yayi parking cike da kulawa yajuyo da kallonsa ga Zahrah wacce take ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, alamar taci kuka ta ƙoshi.
“Banga laifin kiba Zahrah, domin dole zakiji matuƙar tsoro, a iya tsawon rayuwata bantaɓa cutar da wata mace ba, kuma bazan fara akan ki ba, bazan taɓa iya cutar dake ba Zahrah, inaso ki yarda dani, ban kuma yi haka don na cutar dake ba, nabiya dake ta mall ɗinne don inaso muje kiyi sayayyan abubuwan dakikeso da kanki, amma sai naga gaba ɗaya kinfirgita, kiyi haƙuri na tsorataki ko ƙanwata !!” Doctor Sadeeq yafaɗi maganar cikin tsananin tausayawa da kuma lallashi ga Zahrah’n..
Kuka kawai Zahrah takuma fashewa dashi haɗe da cusa kanta cikin cinyoyinta, a hankali ya kama hanunta haɗe da matsewa a cikin nasa hanun, “Banason kuka Zahrah, bana ce kiyi haƙuri ba!” Dr yafaɗa cikin damuwa.
“Bakaine zaka bani haƙuri ba likita, nice zanbaka haƙuri, nayi maka mummunar fahimta, dan Allah kayi haƙuri, wlh tsoro nakeji banso wani abu yasake faruwa dani…!” taƙare maganar tana kuka sosai.
“Idan kinaso nayi haƙuri to kidaina kuka kinji ƙanwata!” yafaɗi maganar yana mai ƙare matse hanunta a cikin nasa hanun.
A hankali tashiga share hawayen dake ambaliya akan fuskarta, ji takeyi zuciyarta tayi mata sanyi.
“Bakya kyau idan kina kuka, kinfi kyau idan kina dariya, kije gida kiyi wanka ki huta, banso kisake zubar da hawayenki kinji Zahrah, ungo wannan ledan kishiga gida, akwai waya a ciki na samiki sim da komai, akwai games dayawa a ciki,nasan zai ɗebe miki kewa, banson ganinki cikin damuwa Zahrah, kije gobe zanzo na kaiki school dakaina, Allah yasa bazakimin gardamaba ” yaƙare maganar yana ƴar dariya.
Murmushi itama Zahrah tayi haɗe da ƙarɓan ƙatuwar ledan dayake miƙo mata, batare da tayi masa gardama ba, cikin rashin kuzari ta buɗe murfin motar tayi ficewarta, harsai da yaga shigewarta cikin gida kafun ya ta da motar tasa ya bar unguwar tasu..
Zahrah tanashiga cikin gida kai tsaye ɗakinta tawuce, jakarta da ledan da Dr Sadeeq ya bata ta ajiye. Kayan jikinta tashiga cirewa, zani ta ɗaura a kirjinta haɗe da sanya hijabi tafice daga cikin ɗakin, zaune ta taradda Inna a tsakar gida, sannu da gida kawai Zahrah tayi mata, haɗe da shigewa cikin bayan gida, tana fitowa a wanka ta bi lafiyar katifarta domin dama dai bata wani jin yunwa, ledan da Doctor yabata ta jawo haɗe da buɗewa, kyawawan dogin riguna ne suka bayyana acikin ledar saikuma dangin su snacks dasu choculate, kyakkyawar kwalin wayar da tagani acikin ledar taciro SAMSUNG GALAXY S10 shine sunan da ke rubuce ajikin kwalin wayar, wani irin faɗuwa gabanta yayi take nunfashinta yashiga gudu akai akai, bazata taɓa mantawa ba shima da haka yafara, daga ƙarshe kuma ya dasa mata babban tabo acikin zuciya da rayuwarta mai wahalan gogewa, saurin sake kwalin wayar tayi haɗe dayin watsi da kayan da suke zube a gabanta, talauci bahauka bane, bazata sake bari haka yafaru da’ita ba, hawaye ne suka shiga sauƙa akan ƙuncinta, haƙika soyayya bata mata adalci ba, kwanciya tayi lamo akan katifa tana nai sauƙe a jiyar zuciya, jin da tayi zuciyarta na shirin dawowa ɗanyea shakaf ne yasanyata tashi ta ɗauko littafi mai tsarki wato Al’Qur’ani tasoma karantawa domin rage damuwar dake damunta a zuciya….
“Salima kuma Hajiya?” Doctor Sadeeq yatambaya cikin muryar damuwa.
“Ƙwarai kuwa Sadeeq, ko ita Saleema’n tana da wani aibune? ƙwarai nayaba da hankalinta dakuma tarbiyanta, saboda haka nagama yanke shawarata, gobe zanfaɗamawa ƙanin mahaifinku yaje yatambayo maka aurenta, idan ma a so nane banso bikin yawuce nanda wata ɗaya ” Hajiya tafaɗi maganar babu alamar wasa akan fuskarta.
Cike da sanyin jiki Doctor Sadeeq yace ” Shikenan Hajiya, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma dakin ƙara haƙuri, nan bada jimawa ba zan kawo wacce nakeso”
“Hmmm ai aikin gama yariga daya gama Sadeeq, nagaji dajin wannan zancennaka, koda yaushe haka kake cewa, to yanzu dai nagaji da ƙaululan dakakemin saboda haka natsaida magana,zaka iya tafiya”
Gaba ɗaya hukuncin da Hajiyar tasa ta yanke masa baiyi masa daɗi ba, amatsayinsa na Namiji bai dace ace anyimasa dole akan aure ba, shi sam Saleema ma bata ɗaya daga cikin irin tsarin matan dayakeso, amma yazaiyi tunda dai Hajiya ta kafe, yasanta da wuyar sha’ani, idan tace eh zaiyi wuya kuma tace a’a, jiki a mace haka yafice daga falonnata, kaitsaye ɓangaren sa yanufa, yanashiga cikin falonnasa direct friedge yanufa, goran ruwa mai sanyi ya ɗauko, haɗe da zama akan kujera, saida yasha ruwan fiye da rabin gora, kafun yashiga sauƙe ajiyar zuciya, wayarsa yaciro acikin aljihun rigarsa, kai tsaye lambar sim ɗin dake cikin wayar daya bata, ya danna wa ƙira, saidai yaji saɓanin tunaninsa, domin kuwa cemasa akayi wayar a kashe take, nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da aje wayartasa a gefe, “Maiyasa nadamu da’ita sosai ne?” yatambayi kansa, bayan kuma yasan baida amsa,
“Inatausayinta sosai,amma kuma bayan tausayi inajin wani abu na daban a ga me da’ita, menene wannan abun ? yazama dole nasan menene amma tabbas ina da burin inganta rayuwarta ” Ƙaran wayarsane ya katse sa daga zancen zucin da yakeyi, ganin da sabon number ake ƙiran nasa yasa bai ɗauki ƙiranba, saima tashi dayayi yawuce cikin bedroom ɗinsa…
Washe gari.
Yau tunda safe takammala shirinta, tayi kyau cikin shigar ta ta atamfa riga da sket, yayinda lufayant dake jikinta ya kasance hot pink colour, sama sama tasha ruwan shayin da Inna ta dafa, tana kammala shan ruwan shayin ta ɗauki jakarta haɗe da nufar hanyar waje. domin batamaso likita yazo yasameta, tafiso tayi tafiyarta, sam bataso yanashiga cikin rayuwarta, takuma yanke shawaran gaya masa yafita acikin rayuwarta, domin sam baikamata tasake bawa wani namiji dama ba.
Turus haka taja ta tsaya, domin kuwa tsaye tagansa ajikin motarsa, yasha ado cikin wata blue ɗin shadda, sam batai tsammanin ganinsa a daidai wannan lokacinba.