NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi yayi mata haɗe da soma takowa harzuwa inda take tsaye.

“Baki tsammaci ganina a dai dai wannan lokacin ba ko?” yatambayeta kansa tsaye yana mai kafeta da idanu.

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa “Ina kwana”

“Lafiya ƙalau, yakika tashi?”

“Lafiya” tabasa amsa a taƙaice, haɗe da sunne kanta ƙasa, domin hakanan taji yamata wani irin kwarjini.

“Muje kada kiyi latti ko” Doctor yafaɗa yana mai yi mata nuni akan cewa tashige gaba.

Bazata iya musa masa ba, domin kuwa yayi mata kwarjini sosai, don haka cikin sanyin jiki tanufi wajen motar tasa, shikuma yarufa mata baya, gaba ɗaya jitayi jikinta yayi sanyi, alƙawarin da ta ɗaukawa kanta nacewa zata faɗa masa yafita a rayuwarta gaba ɗaya ya ruguje, domin kuwa tanaganinsa taji bakinta yamutu murus, tana shiga cikin motar ta lumshe idanu, domin kuwa wani irin daddaɗan ƙamshi cikin motar keyi, cike da nutsuwa yake tuƙin nasa, yayinda jefi jefi yake satan kallon Zahrah, wanda gaba ɗaya hankalinta yana ga ababen hawan da suketa hada hada akan titin.

“Maiyasa ki kaƙi kunna wayar dana baki?”

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi haɗe da soma wasa da yatsun hanunta,  “Babu” tafaɗi hakan cikin sanyi murya.

“Ko kuma dai bakyason kyauta daga gareni ba “

Saurin kallonsa tayi, jin abun da yace, ai kuwa karab idanunsu suka haɗe a waje ɗaya, saurin sadda kanta ƙasa tayi, domin batason haɗa idanu dashi kokaɗan,    “Bahaka bane, kawai dai  banson rayuwata tasake cutuwa ne” tafaɗi hakan da iya gaskiyarta.

Kansa ya jinjina haɗe da cizon lips ɗinsa,  “Eh ta wani wajenma kina da gaskia, amma ai bada wata manufa na baki ba, amma idan kinaga zaki takura to shikenan saikiyi abun da yadace”  shima yayi maganar da iya gaskiarsa.

Daga haka dukansu basu sake ce da junansu komaiba, har suka iso cikin makarantar, yauma har gaban lecture hall ɗin su ya kaita, sai da kuma yaga shiganta cikin hall ɗin kafun yayi tafiyarsa.

Koda aka tashi yauma shiya zo da kansa ya ɗauketa,  sai dai tunda suka kama hanya harsuka isa gida babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu.

A daidai ƙofar gidan su ya tsaida motar, haɗe da juyo da kallonsa gareta ƙoƙarin fita tasomayi daga cikin motar, cikin wata irin murya mai sanyi yace “Inason magana dake”

Kallo ɗaya tayi masa ta kau da kanta gefe,  “Wace irin maganace ?”

“Maganace mai matuƙar mahimmanci , amma kuma tana buƙatar ishashshen lokaci ” Doctor yaƙare maganar yana mai duban agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.

“Inajinka” Zahrah tafaɗa a taƙaice,

“Bakina jina zaki ce ba,  hankali da tunaninki nakeso kibani “

Gyara zamanta tayi haɗe da ɗan satar kallonsa, batare da tace komaiba.

Kwantaccen sajen dake kan kumatunsa ya shafa, haɗe da cewa ” No kada kiyi zaton wani abu zance, dama  alluranki ne banƙara sa miki ba, kuma akwai matsala idan banyimiki su ayau ba!”

Gaba ɗaya idanunta ta ƙwalalo su waje, yayinda tsoro yacika zuciyarta, “Dan Allah kayi haƙuri wallahi na warke, yanzu banajin komai ajikina!” taƙare maganar lokacin da muryarta ke rawa, alamun zatayi kuka.

“A’a ni gaskia banyarda da cewa kin warke ba, saboda naga kina yawan sanya kanki a damuwa kuma jiya ma dana riƙe hanunki naji zazzaɓi a jikinki, don haka kawai zan ƙarasa miki yanzu” yaƙare maganar yana mai shirin buɗe wani ɗan ƙaramin drower dake cikin motar, take allurai suka bayyana, ai a ɗari Zahrah ta buɗe murfin motar haɗe da rugawa zuwa cikin gida,  ko tsayawa ɗaukar jakarta batayi ba.
Dariya sosai Doctor Sadeeq yasanya, hadda riƙe ciki, shi dama burinsa yaga yanayin tsoronta, domin idan tana cikin wannan yanayin tsoron sosai take burgesa,  ɗaukar jakar nata yayi haɗe da fita acikin motar kai tsaye yanufi cikin gidan. Yana sallama Inna ta tarbesa da fari’a, haɗe da cewa “Ai dama nasan tare kuke domin daganin yanda tashigo a guje nasan cewa ba ita kaɗai bace”  ɗan guntun murmushi yayi haɗe da cewa ” waifa dan nace zanmata allurane, shine duk tabi ta ruɗe, kuma yau bazan bar gidannan ba harsai na mata alluran nan, ko yakikace Inna?”

Idanu Zahrah tasake gwalowa jin abun da yake cewa,  gaskia ita daya mata allura gwamma yabata magani amma sam batason allura, kuma ita taji sauƙi, amma su sundage akan cewa wai bataji sauƙi ba,  kafun ta gama zancen zucin da takeyi taji muryarsa a bakin ƙofar ɗakin yanacewa Inna ta ɗauko masa ita….

(Kuyi haƙuri jiya kunjini shiru,  muna biki ne, yauma a daddafe nayi muku typing bacci nakeji)

         30/November/2019

*Voted, Comment & Share please….Follow me on wattpad @fatymasardauna

????????????????????????????????????????

                   SHU’UMIN NAMIJI !!

      Written By
Phatymasardauna

  
Dedicated To My Lovely Brother Khabier

????Kainuwa Writers Association

{United we stand and succeed;our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

           WATTPAD
      @fatymasardauna

Editing is not allowed????

(Ina mai baku haƙurin rashin jina kwana biyu da kukayi, insha Allah hakan bazai sake faruwa ba)

Chapter 44 to 45
 

Sake matse jikinta tayi ajikin bango, haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.   

“ZAHRAH!” taji muryarsa yana ƙiran sunanta,  cikin tsoro da ɗar ɗar, ta   buɗe ƙofar ɗakin nata, kallo ɗaya yayi mawa cikin idanunta yakau da kansa gefe, domin kuwa wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa tayi, gaskia Zahrah tana da abubuwan ɗaukar hankalin ɗa namiji da yawa a tattare da’ita.

Batare da yakuma kallonta ba, ya miƙomata jaƙarta dake riƙe a hanunsa, da sauri ta fusge jakar haɗe da komawa cikin ɗakin ta,ta kuma  datse ƙofar,  murmushi kawai Doctor Sadeeq yayi haɗe da girgiza kansa, kallonsa yakomar ga Inna, cikin girmamawa yayi mata sallama, bayan ya cika mata hanunta da alkhairi,  cike da farinciki Inna tayi sallama dashi, don tsabar daɗi ma har kusan ƙofa ta rakasa, tana mai zabga masa godiya.

Tafiya yake amma shi kaɗai yake murmushi, sosai Zahrah take burgesa, yanason komai na yarinyar, fushinta, dariyanta, tafiyarta, nutsuwarta, dama duk wani abu nata, tabbas Zahrah tana ɗaya daga cikin irin matar da yake fatan mallaka a matsayin matarsa ta sunna,  ko dai zai jarrabane ?” ya tambayi kansa, saurin dukan seterin motar tasa yayi haɗe da cije laɓɓansa,  “Ka dawo cikin hankalinka Sadeeq, maikake shirin aikatawa ne haka?” yatambayi kansa a fili.

“No baikamata nayi haka ba, dole zanyi haƙuri !” yafaɗi hakan cikin karyewar zuciya, dai dai lokacin kuma ya iso gaban makeken gate ɗin gidansu, mai gadi yana gama wangale masa gate ɗin ya cusa motar tasa zuwa cikin gidan.

Saida tagama ƙaremawa wayar kallo kafun ta danna madannin da zai sanya  wayar ta kawo haske,    nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe, haɗe da jingina bayanta da jikin bango,  “Yazama dole kikawo sauyi acikin rayuwarki   Zahrah,  kada ki bari abunda Zaid yayi miki, yazama sanadiyar lalacewar duk wani farinciki dake cikin rayuwarki”  zuciyarta ta faɗa mata hakan cike da ƙarfafa mata guiwa, “Amma tayaya hakan zai kasance, bayan banda wani ginshiƙi dazai taimakamin ?” Zahrah tatambayi kanta,  sake gyara zamanta tayi haɗe da ɗaukar wayarta, kai tsaye tashiga wajen dazai sadata da apps ɗin wayar,  Word Charm shine game ɗin daya ɗauki hankalinta, duk cikin apps ɗin dake wayar, dama tanason game ɗin, don haka kaitsaye tashiga tasomayi, take taji kewa da kaɗaicin da take ji sun soma ragewa, a wannan rana dai  Zahrah batayi wani dogon tunani  da takura kanta ba, dazaran taji ta takura zata ɗauki wayarta tasoma buga game,  idan ta gaji  da buga game ɗin kuwa, sai ta shiga Instagram shima sosai yake rage mata kewa (nima haka, lol)..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button