NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Cigan Labari…

Daga Club ɗinnan Zaid baizarce ko’ina ba sai guest house ɗinsa, koda ya isa yasamu tuni Asmee tazo tana jiransa,, tundaga falo Zaid suka soma watsewa shida Asmee,, ……..

((Kuyi haƙuri jiya kunjini shiru, walƙahi wayatace ba charge.))

13/October/2019

   *MRS SARDAUNA*

????????????????????????????????????????

    *SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*

phatymasardauna
????Mrs Sardauna????

Dedicated To My Lovely Brother Khabeer

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
    *WATTPAD*

@fatymasardauna

Editing is not allowed ????

Chapter 5 то 6

Haka Zaid da Asmee suka ɓata dare suna iskancinsu, basa ko tsoron Allah mahalicci,, haƙiƙa zuciyar Zaid ta bushe ƙarau, baya ko tuna azabar da Ubangiji zaiyi masa, aduk sanda yaje garesa batare da ya tuba ba…….

Kasancewar yau basu da lecture sai 12 pm yasanya gaba ɗaya aikin gidan itatayi shi, yayin da Inna ke kishingiɗe akan tabarma,, da bala’i Baffa yashigo cikin gidan ” Wallahi ni nagaji bazan iyaba ehe, ace akan yarinya kwara ɗaya tol duk inda nagilma mutane zagina sukeyi, to bata saɓuwa, ke Zahrah inakike ne dan Ubanki ?” Baffa yaƙare maganar cikin hargowa, Zahrah dake cikin kitchine tafito jikinta a sanyaye domin tasan kwanan zancen,, “Lafiya kuwa Malam kashigo gida kana ɓaɓatu ?” Inna dake kwance tatambayeshi, ” Kema kinsani ai akan wannan yarinyar ce mana Zahrah taƙi fito da Miji tayi aure, tananan koda yaushe cikin bulayin zuwa makaranta, makarantan da ba tsinana mata komai zaiyi ba, to wallahi nagaji, ko ina gulma ake wai nakasa riƙe amanar da ɗan uwana yabani, naƙi aurar da yarinya nasata karatu, bayan nafi kowa tsanar wannan ɗan iskan karatun da takeyi ” “Ke Zahrah !!” yaƙira sunan Zahrah da kakkausar murya, batare da yabari ta amsa masa ba yaci gaba da cewa ” bazan iyawa zagin mutane ba, nabaki nanda wasu kwanaki ki fito da miji koda kuwa musaki ne na tattaraki nayi miki aure batare da wani kayan ɗakiba, kije can ki ƙarata ” Baffa nakaiwa nan a zancensa ya sakai yashige cikin ɗaki, Inna tarufa masa baya,,, ɗaki Zahrah ta koma haɗe da zama akan ƴar yalolon katifarta, ” ya Allah gani gareka kafi kowa sanin halin da nake ciki ya Allah kakawomin ɗoki ” wasu zafafan hawayene suka shiga sauƙa daga kan fuskar Zahrah, maganar kenan koda yaushe Miji Miji, wai shin ina zata samo mijin da zai aureta ? tun da take a duniya Namiji ɗaya ne yataɓa cewa yanasonta, kuma shima tundaga wannan ranan bata sake sashi acikin idanun taba, tayi imani cewa tana da tsantsar kyau da kuma sura, wanda zai iya janyo hankalin ko wani ɗa namiji zuwa gareta, amma maiyasa babu wani Namiji dake kallonta ballan tana harya furta mata kalman so ? tayi mawa kanta tambayar da bata da amsa,, jin motsin Inna a tsakar gida yasa tayi saurin share hawayenta, haɗe da ficewa daga cikin ɗakin, kuɗi Inna taciro daga kunkuminta, haɗe da miƙamawa Zahrah tace “Ungo maza kaima wa Ladidi mai adashe kice mata ga zubina na jiya ” “to” kawai Zahrah tace haɗe da nufar hanyar fita daga gidan, domin dai dama sanye take da hijab ajikinta, al’adar ta ce bata zama babu hijabi, saidai idan a ɗakinta take….

Tafiya take tana kallon ƙasa, yayinda hannayenta ke naɗe akan ƙirjinta, da gudun gaske ya shawo kwanar saura ƙiris ya doketa, Allah ne kawai yasa tayi saurin matsawa gefe,, parking motar yayi haɗe da leƙo kansa waje ta window’n motar ” Uh sorry Zahrah ina fata dai bantaka ki ba ?” ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa “A’a baka takani ba” wani irin shu’umin kallo yabita dashi haɗe da cewa “Ina zaki ne haka da tsakar rana ?” ” Aika zani ” Tabasa amsa a taƙaice,, “Okay shigo na rage miki hanya mana ” yayi maganar yana mai yunƙurin buɗe mata murfin motar, “A’a kabarshi kawai nagode” bata jirayi mai zai ceba tasakai tayi tafiyarta,, murmushi kawai Bash yayi haɗe da figar motarsa yayi gaba…..

Wacece Zahrah ?

Malam Adamu Muhammad haifaffen ɗan jihar Yola ne, su biyu ne a wajen iyayensu shida ƙaninsa Hayatu, Malam Adamu yakasance mutum mai mutumci da kuma karamci, Matarsa ɗaya Zainab, Zainab, asalinta buzuwar Niger ce fatauci yashigo da mahaifanta Nigeria, Mahaifan Zainab dana Malam Adamu suna da kyakkyawan alaƙa kasancewarsu maƙotan juna, tun Zainab na ƙarama Allah yasanya mata soyayyar Malam Adamu acikin zuciyarta, kasancewarsa kyakkyawan bafulatani, duk da dai tafisa kyau nesa bakusa ba, cikin ikon Allah Zainab nakai lokacin daya kamata ace anyi mata aure, iyayenta suka Aura mata Malam Adamu, zama sukeyi na lafiya da ƙaunar juna,, watarana iyayen Zainab suka shirya don zuwa Niger, ahanyarsu ta zuwa sukai gamo da ƴan fashi, suka harɓesu, sosai Zainab tayi kukan rashin iyeyenta, da ƙyar dai Malam Adamu yasamu ya rarrasheta, akwana a tashi kwatsam ciki yabayyana ajikin Zainab, sosai sukayi murna da samun ƙaruwa da Allah yayi musu, cikin Zainab nada Wata Tara tahaifo kyakkyawar ɗiyarta mai matuƙar kama da ita, saidai ita ƴar harta ɗara Zainab a kyau duk da kuwa kyau irin na Zainab, anyi shagalin suna lafiya inda yarinya taci sunan mahaifiyar Zainab wato FATIMA ana ƙiranta da ZAHRA Zahrah tataso cikin gata da kulawar iyayenta, saidai muce masha Allah,, watarana ne Malam Adamu yatattara matarsa da ƴarsa suka koma garin Abuja da zama, cikin wata unguwa da’ake ƙira Suleja, yakama musu hayan wani ɗan ƙaramin gida,, sana’ar saida takalma Malam Adamu keyi, yana da ɗan teburinsa a nan yake kasa takalman roba da su silifas (slippers), cikin ikon Allah kuwa,Allah baya hanasa na abinci da kuma na ƴan biyan buƙatun da ba’a rasaba, Watarana Malam Adamu ya tsinci wasu maƙudan kuɗaɗe a ƙasa, daya bincika kuɗin shine yataradda adireshi (Adress) na mai kuɗin acikin jakar daya tsinci kuɗin, a shema wanda ya wurgar da kuɗin, a nan gaba da unguwarsu kaɗan yake kuma yasanshi sunansa Alhaji Umar, Malam Adamu baiyi ƙasa a guiwa ba wajen kaimawa Alhaji Umar kuɗinsa, aikuwa Alhaji Umar yaji daɗi sosai, nan yaɗauki maƙudan kuɗaɗe yabamawa Malam Adamu, amma Malam Adamu haka yaƙi karɓa acewarsa, shi don Allah yayi bawai don abiya saba, aikuwa Alhaji Umar yaji daɗin hakan, haka dai Alhaji Umar da Malam Adamu suka soma zumunci, watarana Malam Adamu na zaune, Alhaji Umar yaƙirasa yace mai yasayamasa gida anan suleja, bakaɗan ba Malam Adamu yayi farinciki, har ƙwallan murna saida yayi, gidane daidai da zaman talaka Alhaji Umar yasai mawa Malam Adamu, ɗakuna huɗu ne acikin gidan sai ɗan madaidaicin filin tsakar gida, da kitchine da kuma makewayi, Koda Zainab tazo taga gidan itama taji daɗi sosai, bawani ɓata lokaci suka tattaro suka dawo gidan,, a kwana a tashi Asaran mai rai, wata rana aka wayi gari Baban Malam Adamu ya rasu, sosai mutuwar tajigata ƴaƴansa, amma babu yanda suka iya duk wani mai rai mamacine sunriga da sunyi imani da hakan,, bawani ɓatalokaci Malam Adamu ya ɗauko mamansa suka dawo garin Abuja da zama,, baifi wata uku da dawowar Goggo (Maman Malam Adamu) Abuja ba, tace ga garinku nan, Allah sarki su Malam Adamu sunkuma jin zafin rashin mahaifiyarsu,, bayan wani lokaci Hayatu yayi aure, Malam Adamu ne yace masa yadawo nan Abuja su zauna, tunda akwai ɗaki a gidansa, Hayatu bai ƙi ba, yaɗauko matarsa suka dawo,, tundaga kan Zahrah Malam Adamu da Zainab basu sake haihuwa ba, Zahrah tanada shekara huɗu Malam Adamu yasanyata amakarantar furamari (Primary) Zahrah yarinya ce mai hazaƙa sannan kanta yana ja sosai, kwanci tashi Zahrah ta kammala makarantar furamari (primary) ɗinta, bawani ɓata lokaci Malam Adamu yasama mata gurbin cigaba da karatu (Admission) a wata junior school dai dai da ƙarfinsa,, Zahrah na aji ɗaya a junior school, Mama (Zainab) takwanta rashin lafiya, abu kamar wasa hardai takaisu ga asibiti, kwanan mama ɗaya a asibiti Allah yayi mata rasuwa, kuka kam Zahrah da Malam Adamu sunsha shi, domin kuwa sunyi rashin jigon rayuwarsu, haƙiƙa Zahrah tayi rashin uwa ta gari, shiko Malam Adamu yayi rashin mace ta gari,, sati ɗaya da rasuwar Mama Malam Adamu yakwanta jinya, abu kamar wasa saigashi ko tashi baya iyawa, Wata rana ne aka wayi gari Malam Adamu baya numfashi, Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un !! Zahrah tayi kuka bana wasaba lokaci guda tayi rashin farincikin rayuwarta,,,,, koda Alhaji Umar yazo ta aziya, baiyi ƙasa a guiwaba, cewa yayi ya ɗauki nauyin karatun Zahrah harta ƙare jami’a, yayinda riƙon Zahrah yadawo wajen Hayatu da matarsa (Baffa, Inna) sam Zahrah batajin daɗin riƙon da Baffa da Inna keyi mata domin tsananin tsangwama suke nuna mata, gahi Baffa yahau kan ɗan gadon da Babanta ya bar mata yacinye,,, Ayanzu Zahrah tana da shekara 20 aduniya, kuma harzuwa yanzu Alhaji Umar ne ke ɗaukan nauyin karatunta…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button