NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tayi kyau sosai cikin blue rover gown ɗin dake jikinta,  wata baƙar lufaya ta sanya a jikinta wanda yataimaka wajen ƙarawa shigar tata kyau da armashi,  batayi wani kwalliya akan fuskarta ba, ta dai shafa man leɓe dakuma kwalli, amma duk da haka tayi kyau, dama mai kyau ko baiyi kwalliya ba kyawunsa baya ɓuya.

Kasancewar yau baza su jima a makaranta ba, yasanya bata ɗauki jakaba, sai wasu ƴan littatafai da ta ɗauka a hanunta, sai kuma wayarta,      koda ta fito tsakar gidan zaune a bakin  murhu ta iske Inna tana tuyan ƙosai, wanda Baffa yace ayi na karyawa.

“Inna ni zanwuce makaranta” Zahrah ta faɗa tana mai ƙoƙarin gyara zaman lufayan dake jikinta.

“Bazaki tsaya ki karyaba Zahrah”
Baffa dake fitowa daga cikin ɗakinsa ya faɗa.

Ɗan guntun murmushi Zahrah tayi haɗe da shafa cikinta “Banajin yunwa sosai Baffa, kuma ina tsoro kada na makara!”

“Eh kina da gaskiya, kinga kuwa tun ɗazu likita, yazo yana jiranki, bayanda banyi da shi ba akan yashigo, amma sam yaƙiya, don haka gwamma ki hanzarta, a dawo lafiya ”  Baffa yaƙare maganar yana mai yunƙurin komawa cikin ɗakinsa.

“Ameen Baffa nagode!” Zahrah tafaɗa cike da farinciki, domin kuwa karo na farko kenan a rayuwarta da taga tsananin kulawan Baffa a kanta.

Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushinsa,  ga mamakinsa sai yaga itama ta sakar masa murmushi, wanda yayi matuƙar taɓa masa zuciya, domin kuwa bakaɗan ba tayi kyau, da tana murmushin.

“Saiyanzu ki ka ga daman fitowa? kinshanyani kamar kin aje dutse” Doctor yafaɗi maganar yana mai turo baki gaba, tamkar ƙaramin yaro.

Dariya sosai Zahrah ta shiga yi, domin yanayin yanda yayi maganar yazama dole wanda ya gani ya dara,   hangame baki Dr yayi yana kallon yanda take dariyan, abun da bai taɓa gani ba kenan, tun haɗuwar su da’ita, bai taɓa ganinta tana dariya ba sai yau, ashe ma duk kyawunta da yake gani, bai ga komai ba, domin da tana dariyan tafi  masa kyau.

Hanunta tasanya ta toshe bakinta, haɗe da tsagaita dariyan da takeyi, kallonsa tayi haɗe da cewa “Bakaga yanda kazama yaro ba dakana maganan nan, tamkar ɗan shekara takwas!”

Murmushi yayi haɗe da jefamata hararan wasa, cikin yanayin da yayi magana ɗazu yakuma cewa “Shine kikemin dariya ko? sai na faɗaki da mamana!”  ai kamar yaƙara mata fower’n da riyan nata ne,  nan take taci gaba da dariyanta, hadda ɗan guntun ƙwalla a idanunta,  wani irin sanyi da nishaɗi yaji yana huda zuciyarsa, tabbas bashida wani buri da yawuce yaga Zahrah tana cikin farinciki Alhmdlh, yau gashi ta sanadiyarsa tana dariya dakuma nishaɗi,

“Kayi haƙuri, bazan sake shanyaka ba, amma gaskia ka iya shagwaɓa da yawa!” Zahrah tafaɗa dai dai lokacin da tayi mawa kanta mazauni acikin motar, haryanzu dariyane kwance akan fuskarta.

“Wato dai yau mugunta kike ji dashi, dariya hadda hawaye!” Doctor yafaɗa cikin nishaɗi.

“Bahaka bane, kai ɗinne dai kawai kabani dariya!” itama ta basa amsa cikin nishaɗi.

“Dagaske kike, saboda ni kike wannan nishaɗin? ” Dr ya tambayeta cike da zaƙuwa, duk da kuwa cewa yasan sabo da shiɗinne take nishaɗin.

“Eh mana, saboda kaine, kasan kaban dariya sosai, kuma nasan bama ni kaɗaiba, duk wacce takalleka a irin wannan yanayin dole zatayi dariya”

Ajiyar zuciya Dr ya sauƙe haɗe da murza key ɗin motar, suka ɗau hanyar da zata sadasu da titi.  

“Idan kina dariya kinfi ko yaushe kyau ƴan mata na!” Dr yafaɗa cikin muryar nutsuwa.

Saurin maida kallonta garesa tayi, jin abun da yafaɗa tayi kamar wani almara,  sai kuma taga yanayinsa tamkar bashine yayi maganar ba.

Yi tayi itama kamar bataji mai yace ba, mai da kallonta tayi ga titi, tana mai kallon yanda ababen hawa suke gudanar da hada hadansu.

“Maiyasa ki ka ƙi cin abinci? ko kinfiso ki zauna da yunwa ne?” Doctor ya jefo mata tambayar da batayi zato ba.

Kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kanta gefe, “Banjin yunwa ne, sannan kuma banaso na yi latti”
tafaɗi maganar a taƙaice.

Baice da’ita komaiba, saima buɗe ɗan ƙaramin drowern dake jikin motar yayi, wani haɗaɗɗen cake dake cikin wani ɗan ƙaramin kwali ya ciro, haɗe da ɗaura mata akan cinyarta,  ” Kici, kuma banson musu” yanayin yanda yayi maganar zai tabbatar ma da cewa, ba wasa yake ba.

“Nagode, amma zanci idan muka fito a lecture” itama ta faɗa kai tsaye.

“Yanzu nakeso kici, umarnine bawai shawara ba”  yakuma faɗi maganar  cikin yanayi mai nuni da cewa da gaske yake maganar.

Batason yi masa musu, domin koba komai yayi mata halacci a cikin rayuwarta,  a hankali take gutsuran cake ɗin tana kaiwa bakinta, duk da cewa cake ɗin yayi mata daɗi. 
Duk abun da takeyi yana lure da’ita, yanayin yanda take tauna abincin shiyafi komai burgesa.

Saida taci cake ɗin fiye da rabi, kafun ta dawo da kallonta garesa, “Naƙoshi” tafaɗa tana mai yatsine fuska.

“Dole sai kin cinye, domin kuwa ni idan nabawa mutum abuna, bai isa yacemin ya ƙoshi ba, dole sai yacinye koda kuwa ya ƙoshin”

Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa “Dagaske nake naƙoshi, amma da alama dole kakeson min”

“Dolen dole ma kuwa” yafaɗa dai dai lokacin da yagama parking motar tasa, domin kuwa harsun kawo cikin makarantar tasu, hanu ta ɗaura akan murfin motar da niyar buɗewa ta fita, tuni ya dannawa ƙofofin luck,  saurin kallonsa tayi domin bata fahimci hakan da yayi me  yake nufi ba.

“Babu inda zakije, matuƙar baki cinye cake ɗin nan ba” yafaɗi hakan yana me jingina bayansa a jikin kujeran da yake kai.

Ƙwaɓe fuska Zahrah tayi cikin sigar lallashi, tace “Kayi haƙuri, naƙoshi, idan naci da yawa, bazan iya karatu yanda ya kamata ba!”

“Um,Um, naƙi wayon, saura kaɗanne fa please kicinye shi mana Zahrah!” Doctor Sadeeq yaƙare maganar cikin lallashi.

“Um, Um, na ƙoshi, gaskiya idan naci zai cutar dani, zanyi ƙatuwa da yawa, ni kuma banaso nayi ƙatuwa!” cikin zallan shagwaɓa Zahrah tayi maganan.

Dariya sosai Dr Sadeeq ya sanya, domin kuwa maganar Zahrah ta bashi dariya, wai ita bataso tayi ƙatuwa hmm.

“To ai yaune kawai, kuma kinga bazakiyi ƙatuwa ba, nima banso kiyi ƙatuwa da yawa, amma inaso kiyi ƙatuwa kaɗan!” yanayin yanda yayi maganar  kaɗai ya isa sanyawa mutum mutuwar jiki.

Batace dashi  komaiba, domin bata fahimci inda maganar tasa ta dosa ba, ɗaukan ragowan cake ɗin tayi, tashiga turawa acikin bakinta, tamkar wacce aka bawa guba. 
Dariya Doctor Sadeeq yashiga yi mata ƙasa ƙasa, domin kuwa yanda takecin cake ɗin, dagani kasan dole a kayi mata bawai a son ranta bane. tana cinyewa ya miƙomata goran ruwa, ai kuwa ba musu ta karɓa ta shiga sha, domin dama duk cake ɗin ya shaƙeta.

Cikin yanayi na shagwaɓa da ɓata fuska tace ” Na cinye yanzu zan iya tafiya!” 

Dariya Dr yayi haɗe da cire luck ɗin da yasanyawa ƙofofin motar “Zaki iya tafiya, amma kikula da kanki sosai, sannan idan kun fito a lecture wani zai kawo miki saƙo daga nine ki amsa”

“Wani saƙo?” Zahrah ta tambaya cike da ɗaurewar kai.

“Zakiyi latti,kiyi sauri kije” Dr yafaɗi hakan don kawar da tambayar da tayi masa.
Bata sake cewa komai ba tabuɗe murfin motar tafice, yauma dai sai da yaga shiganta cikin hall ɗin kafun yatada motarsa yabar cikin makarantar, direct shima asibiti ya nufa, domin yau yanada aiki sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button