SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Sosai yau ta gane Lecture ɗin da akayi musu, saɓanin sauran ranakun da suka wuce wanda ba komai take fahimta daga cikin abun da ake koyar musu ba.
Fitowarsu kenan daga lecture, tafe suke su biyu, yayinda Husnah keta mita, wai jimawan da sukayi suna lecture, yasanya tanemi gaba ɗaya abincin cikinta ta rasa.
Dariya Zahrah tayi haɗe da cewa “Nikuwa kinga ɗigo na yunwa banaji, domin kuwa yau ɗure, a kamin dan dole na”
“ɗure kuma bestie? Amma badai Inna da Baffa bane sukaimiki ɗuren bako?”
“Doctor Sadeeq ne!” Zahrah tafaɗa a taƙaice.
“Doctor Sadeeq kuma? lallai kuwa Doctor yayi babban ƙoƙari, shiyasa na ganki yau kina cikin farinciki” Husnah tafaɗa tana mai ƙoƙarin gimtse dariyar da take ƙoƙarin taso ma ta, domin ita kam ta hango wani babban al’amari dangane da Doctor dakuma Zahrah.
“Maikike nufi?” Zahrah ta tambayi Husnah cikin tsare gida.
Husnah batakai ga bata amsa ba, wani mutumi ya ƙaraso garesu, hanunsa ɗauke da wata leda, sallama yayi musu suka amsa masa.
Kaitsaye ya miƙomawa Zahrah ledar dake hanunsa, haɗe da cewa “Gashi inji oga”
Take maganar da Dr yafaɗa mata ɗazu a cikin mota, cewar wani zai kawo mata saƙo, ya faɗo mata, cikin sanyin jiki ta amshi ledan, haɗe da ce masa ta gode.
“Saurin karɓe ledan Husnah tayi daga hanun Zahrah, haɗe da cewa “Allah yasa abun daɗi ne, domin yawuna haryafara tsinkewa, kinsanni ba baya bace wajen kwaɗayi”
“Wow special gift!!” Husnah tafaɗa sanda idanunta suka gane mata abun da ke cikin ledar,
“Amma ba haka naso ba, ƙawata naso ace wani abun ci ne kinga da sai na morewa bakina!” Husnah ta ƙare maganar tana mai ɓata fuska.
Dariya Zahrah tayi haɗe da sanya hannayenta ta dafa kafaɗun Husnah, cike da nishaɗi tace ” Allah ƙawata, ki rage kwaɗayi, yanzu idan abun ci ne, yazuba mana wani abu a ciki, mukazo mukaci, ya cutar da mu,kuma fa? kinga kwaɗayi ya jawo mana kenan,kuma bai mana rana ba”
“Dan Allah malama sakeni, nayarda da Dr nasan babu abun da zai ɓamu wanda zai cutar da mu, kedai kawai mugunta ne irin naki, bayan kinsan inajin yunwa, muje cafeteria muci abinci please!” Husnah tafaɗa tana mai daɗa kwaɓe fuska.
“Yi haƙuri ƙawata bani nakar zomonba, muje sai kici abincin ko” Zahrah tafaɗa cike da kulawa.
“Ungo kayan shafanki, domin kuwa cigaba da riƙesu ma, ƙaramin yunwa zaiyi” Husnah ta ƙare maganar tana mai miƙomawa Zahrah ledar dake hanunta.
Dariya kawai Zahrah tayi haɗe da amsar kayan, sarai tasan Husnah bata da haƙurin yunwa ko kaɗan.
Ice cream kawai Zahrah tasha, yayinda Husnah kuwa ta cika cikinta da shinkafa. Yau darasi biyu garesu kacal, don haka suna fitowa kowa ya yi ƙoƙarin kama gabansa.
Waige waige tashiga yi ko zata hangosa, amma babu alamar komai irin motarsa, wayarta ce ta soma ƙara alamar shigowar ƙira, Number ne ke yawo a kan screen ɗin wayar babu suna, dama kuma batayi tunanin Numbern zai fito da suna ba, domin batayi saving numbern kowa ba, wama ta sani da zatayi saving number’nsa.
Har saida wayar ta kusa katsayewa kafun Zahrah ta ɗaga ƙiran, “Zahrah! na gaji, da yawa, aiki yamin yawa, please ga nan driver na, zaizo ya ɗaukeki ya kaiki gida, kiyi haƙuri kinji ƙanwata!!” Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin kwantar da murya, da gajin yanda muryansa take fita slow kasan cewa a matuƙar gajiye yake.
A jiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa “Shikenan kahuta lafiya”
“Yauwa Ƴan mata na, ki kulamin da kanki” ƙit ya kashe wayar, ba tare da ya tsaya ya saurari mai zata ce ba.
Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da girgiza kanta, “Hmm wai itace ƴan mata, itakam yanzu ai ta wuce a ƙirata ƴan mata saidai sauran Zaid” tafaɗi hakan a zuciyarta, take kuma taji idanunta sun kawo ruwa. Dai dai lokacin motar Dr Sadeeq ta ƙaraso inda take tsaye, kasan cewar yayi mata bayanin cewa driver’n sane zaizo ɗaukarta, dan haka batayi wani jinkiri ba, ta buɗe murfin motar tashiga, ko kallon inda driver’n yake batayi ba, “ZAHRAH!” muryan Dr Sadeeq ya daki dodon kunnuwanta, saurin maida kallonta inda taji muryan tayi, ai kuwa shiɗinne kwance a jikin kujeran gidan baya, idanunsa ɗaya ya kashe mata haɗe da ɗage giransa ɗaya sama, “Surprise!” yafaɗa fuskarsa ɗauke da murmushi.
Murmushi itama tayi masa, haɗe dayin ƙasa da kanta, domin yanayin yanda yayi mata maganan, yasanya taji jikinta yayi sanyi.
“Dawo nan muzauna, ki bar driver yayi aikinshi”
Ɓata fuska Zahrah tayi haɗe da turo baki gaba, cike da shagwaɓa tace “Ni dai kabarni na zauna anan ɗin ma yayi!”
“Nace ki dawo nan muzauna ko!” yafaɗi hakan babu alamar wasa akan fuskarsa.
Cike da sakalci Zahrah ta dawo gidan baya inda yake zaune, ko kallonsa batayi ba saima langwaɓewa da tayi a jikin kujera. Har sukayi nisa a tafiyan babu wanda yace da ɗan uwansa ƙala, cikin shagwaɓa tace “Bakace min aiki yamaka yawa ba, amma mai yasa kazo?”
“Saboda ya cancanta nazo, ina da burin baki kyakkyawan kulawa a ko da yaushe, ko bakiyi farinciki da hakan ba?”
“Nayi farinciki sosai!” Zahrah tafaɗa kai tsaye, domin kuwa sam batason irin kallon da yake yawan yi mata a wasu lokutan.
Baisake ce da ita komai ba, shima sai ma komawa da yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran motar.
A haka har suka iso ƙofar gidan su Zahrah’n, kallo ɗaya tayi masa haɗe da buɗe murfin motar tayi ficewarta, yana ganin shigewarta gida, yace driver ya ta da motar suje.
Bayan Sati Biyu….
Wani irin shaƙuwa ne mai ƙarfi yashiga tsakanin Doctor Sadeeq da Zahrah, kullum shi ke kaita mkaranta shi kuma ke ɗauko ta, sosai yake bata kulawa, baya son duk wani abu da zai ɓata ranta, ko ya sanya taji ba daɗi, ɓangaren Zahrah ma, sosai take kiyayewa dashi, tana iya ƙoƙari wajen ganin bata musa masa idan ya umarceta da tayi abu, ko kaɗan batajin wani abu a dangane dashi, tana dai yi masa biyayya tana kuma ganin girmansa, domin kamar yanda yace ta ɗaukesa, a matsayin ɗan uwa, to a matsayin ɗan uwan ta ɗaukesa, domin kallon yaya take masa, sannan kuma sosai wayarta take ɗe be mata kewa, yakanyi ƙoƙari wajen ganin ya ƙirata a waya, a kowani dare, sai dai hiran tasu bata tsayi suke sallama da juna, sosai rayuwarta tasamu canji, bakamar da ba, duk da cewa abune mawuyaci manta abun da ya faru da’ita, amma takanyi ƙoƙari ƙwarai wajen ganin ta gusar da duk wani damuwarta.
Tsaye yake a gaban tangamemen dressing mirror ɗin dake kafe a jikin bangon ɗakin nasa, yayi kyau sosai cikin riga da wandon shadda dake jikinsa, ba abun da jikinsa keyi banda tashin ƙamshi, hannayensa duka yazura a cikin aljihun wandon shaddan dake jikinsa, tabbas a kwai wani al’amari mai girma dake cikin zuciyarsa, haƙiƙa kuma akwai abun da yakeso ya furta,amma tayaya, baisan da wani manufa zata ɗauki zancen ba, baisan wani amsa zaiji daga bakinta ba, wannan shiya hanasa furta mata tsadaddan kalman dayake ta ɓoyewa tsawon lokuta, bayajin zai samu abun da yakeso daga gareta, bakuma yajin zai samu amincewarta, ya tabbatarwa kansa cewa, a yanzu lallashi take buƙata fiye da komai, sannan kuma bata buƙatar wata magana wanda zata zamo sanadiyar rugujewar ɗan farincikin da ta soma samu, sai zuciyar sa ta ƙarfafa masa guiwa, saikuma gangar jikinsa tayi sanyi laƙwas.