SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ba’asan jarumin Namiji da tsoro ba!” wata zuciyarsa ta furta masa hakan.
Ƙwarai ya yarda da cewa shi ɗin jarumi ne, amma kuma gurin da yake da muradin isar da saƙonnasa wajene mai rauni, dole zai fuskanci ƙalubale guda biyu, rashin nasara, ko kuma, yin nasara, wayarsa ya ɗauka ya sanya a cikin aljihunsa, kai tsaye ya fice daga cikin ɗakin nasa, yana shiga cikin motarsa ya bata wuta, kai tsaye unguwar su Zahrah ya nufa, sosai ya yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa, lallai yazama dole ya bayyana mata sirrin dake kwance cikin zuciyarsa, sai dai yasan balallai ta aminta da ƙuɗirinsa ba, amma zai jarraba ya gani.
A ƙofar gidansu yayi parking motarsa, haɗe da ciro wayarsa, ya danna wa Number’n Zahrah ƙira, sai dai harzuwa lokacin zuciyarsa fat fat haka take bugawa. tana ɗaga wayar yace “Ina ƙofar gidanku, dan Allah kizo ki sameni” banji mai tace masa ba, sai gani nayi ya mai da wayar tasa cikin aljihunsa, haɗe da sauke nannauyar ajiyar zuciya….
(Tofa readers, mai kuke ganin Doctor Sadeeq zai faɗawa Zahrah, da haryakejin tsoron faɗa mata, sbd baisan daya zata ɗauki maganar ba, to zadai muji kome nene a next page insha Allah! Ko ina Baba Zaidu kuma ????♀)
3/December/2019
*Voted,Comment, and Share please….. Follow me on Whatsapp and Wattpad @fatymasardauna

????????????????????????????????????????
SHU’UMIN NAMIJI !!
Written By
Phatymasardauna
Dedicated To My Brother Khabier
????Kainuwa Writers Association
{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
WATTPAD
@fatymasardauna
Editing is not allowed????
(????Yasin bansan haka Baba Zaidu yake da masoya ba sai kwana biyu da bana taɓo sa, ashe dai masoyan Zaid sunfi maƙiyansa yawa, kusha kurumin ku mutanen Zaidu yau zan taɓo muku chapter’n shi, su Munubia nasan anyi missing ????)
Chapter 46 to 47
Tana aje wayan ta ɗauko wani rover hijab ɗinta ta sanya a jikinta, koda tafito daga cikin ɗakin nata, zaune ta iske Baffa da Inna, a tsakar gida, domin dai dama dare yasoma rufawa, cike da ladabi tace ” Baffa Doctor Sadeeq yana ƙirana a waje”
Gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa ” to naji ƙaran tsayuwar mota ai, ashe dai likitane yazo, to adawo lafiya”
Muguwar harara Inna ta jefamawa Zahrah, cike da masifa tace “Wato ni banza bankai matsayin da zaki tambayeni ba ko? wato Baffanki kaɗai kika gani a wajen?”
Cikin sanyin murya Zahrah tace “Kiyi haƙuri Inna, naga shi ya kamata na sanarmawa hakanne, tunda ya na nan!”
“Wuce kije ƙiran da yake miki kinji Zahrah’u, barta Salame yau masifa take ji dashi” Baffa yaƙare maganar yana mai wurgamawa Inna harara.
Bata kuma sauraran abun da Inna zatace ba tasakai tayi ficewarta daga cikin gidan..
Duk da cewa babu wadataccen haske a wajen, amma tana iya hango kyawun da kayan jikinsa sukai masa, “gaskiya Dr kyakkyawane shima” tafaɗi hakan a cikin zuciyarta.
Da sallama ɗauke a bakinta ta ƙaraso inda yake tsaye, cike da fari’a Dr ya amsa mata sallaman da tayi haɗe da cewa “Wato sai anjamin aji kafun a fito ko?”
Ɗan guntun murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa “Bawani batun jan aji, ni a hakan ma inaganin na fito da wuri”
Shima murmushin yayi haɗe da cewa “Kinyi kyau!”
Still murmushi tayi, cikin son kawar da zancen da yayi na cewa tayi kyau, tace “Lafiya kuwa naganka a dai-dai wannan lokacin?”
Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da maida nutsuwarsa gareta “Maganar danazo miki da’ita Zahrah bata tsaye bace, yana da kyau mushiga mota, sai mu tattauna ko?”
Ɗan jim Zahrah tayi, haɗe da cije lips ɗinta, “Shikenan amma inafatan bazamu jimaba, kafasan banson fitowa waje da dare”
“Insha Allah, bazamu ɗau tsawon lokaci muna magana ba!” Dr yafaɗi hakan lokacin da yayimawa kansa masauƙi a cikin motar tasa, bayan ya kunna ƙoyin wutar dake cikin motar take haske ya gauraye cikin motar.
Gyara zama Zahrah tayi, haɗe da tattaro duka nutsuwarta “Inajinka” tafaɗa a taƙaice.
Wani irin numfashi Dr yayi, haɗe da fitar da iska daga bakinsa, sai yanzu yakejin cewa, bazai iya furta abun da yakawosa ba, gaskiya yanajin nauyi, baisan tayaya Zahrah zata karɓi muradinsa ba, kada maganar da zaifaɗa ma ta yazamo sanadiyar rugujewar nishaɗin da yake gani akan fuskarta yanzu, “Ta’ina zanfara?” ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
“Lafiya kuwa, naga kayi shiru?”
Zahrah ta tambaya, cike da mamakin yanda yayi shiru, bayan yace akwai maganar da zasuyi.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗi da maida kallonsa gareta, saida ya tattaro nutsuwarsa kafun yace…
“Yazakiji idan wani yazo miki da batun soyayya a wannan lokacin Zahrah?” abun da ya iya fitowa daga bakinsa kenan, domin a gaskia shikam yarasa ta’ina zai fara.
“So kuma? wani irin so?” Zahrah ta tambaye shi cike da mamakin kalaman nasa.
“So na Aure Zahrah!” yafaɗi maganar cikin ɗar ɗar.
“Au..r..e.. Kuma Likita? Aure fa kace, dama akwai wani wanda, zaiji kwaɗayi da sha’awar aure na ne? hmmm a gaskia bana tunanin haka, domin kuwa babu wani wanda zai so ni da rayuwata, a yanda nake ɗinnan!” Zahrah tafaɗi hakan da’iya ka gaskiyar ta.
“Kada kice haka Zahrah, akwai mata masu rauni da yawa irin ki, amma an auresu, kuma anzauna dasu, ke me yasa zaki yanke ƙauna da….”
“Dan Allah kadaina min wannan zancen Doctor, banjin zan sake son wani ɗa namiji a duniyar nan”
Zahrah ta katse shi da ga maganar da yakeyi, ci gaba tayi da cewa
“taya kake tunanin zansake kai kaina tarkon da ya ruguzamin rayuwa, shi So ɗin dakake faɗa yanzu, shine ya ruguzamin rayuwa ta, ya rabani da duk wani farinciki na rayuwata, shin idan kace min na sakeyin So, kamin adalci kenan? ” Tuni hawaye sun gama wanke mata fuska.
“Kada kice haka Zahrah, kefa musulmace, kuma ke mace ce, nasan kina da sanin cewa, kyautatuwar rayuwar ƴa mace shine aure, haka kuma rayuwar ƴa mace bata cika hundred percent sai da aure, haka kikeso ki ƙare rayuwarki ba aure? ko kin manta cewa cikar mutumcin mace shine a ganta gidan mijinta? yin Aure shine burin kowacce mace ta ƙwarai, nasan kema wannan shine burinki, kada shaiɗan yayi amfani da abun da yafaru dake, ya ruguza miki rayuwa, ya hanaki aikata sunna!”
“Hakan shine burina amma ada, wa zai aureni a yanzu? waye zai ɗaukawa kansa duhu? waye zai ɗauki sauran da wani yaci ya rage, sauran da wani ya tarwatsa, ya zuba ƙazantarsa, acikin cikinta, waye zaiyi hakan? bazan yaudari kaina ba, nasan babu wani wanda zai aureni a yanda nake, bantaɓa aure ba, amma kuma niba budurwa bace a yanzun, ya cuceni yariga ya karɓe abun da nake burin bawa mijina na sunna, waye zai yarda da haka?”
“Nine nan Zahrah, Nasan komai a kan ki, kuma zanyarda da duk wata ƙaddaranki, nine wanda zan sharemiki hawayenki, kece damuwata bawai budurcin kiba, kiyarda dani dan Allah!!” Doctor Sadeeq yafaɗi hakan cikin jajircewa..
Kamar sauƙan aradu haka Zahrah taji sauƙan kalamansa a cikin kunnuwanta, cak ta tsaida kukan da takeyi haɗe da, da hangame baki tana kallonsa, gani take kamar ma baya cikin hayyacinsa, ƙaryane tayaya za’ace Namiji mai aji, kamar Doctor yace wai ya amince da ƙaddaranta zai aureta, wannan ba gaskia bane,