NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kada kiyi shakka ko kokonto, ba yaudara’nki nake ba, dagaske nake har cikin zuciyata, don Allah ki bani dama Zahrah, burina da fatana kawai ki amince min!”

Kai Zahrah ta shiga girgizawa, cikin tsananin ɓacin rai da danasin sauraransa da tayi tasoma cewa ” Nayi Babban kuskure, haka kuma na tabka nadaman baka daman shigowa rayuwata da nayi, ashe dukanku haka halinku yake, macutane ku azzalumai,  ashe bazaku taɓa sanjawa ba, dama ɗaya kawai idan aka baku, sai ku nemi shigo da manufarku, kaicona da abun da Zaid yayi mini baikasance IZNAH ga rayuwata ba, kaicona dana sake aminta da kai, kaicon zuciyata,  kafita a rayuwata dan Allah, kaje banaso nasake ganinka ko kuma  jinka, katafi kayi nisa da ni, kabarni na rayu cikin salama dan Allah!!” gaba ɗaya hawayen ɓacin rai yagama wanke mata fuska,  ƙoƙarin fita daga motar ta somayi, cike da tashin hankali Doctor Sadeeq ya riƙo hanunta, ko kaɗan baiyi zato ko tsammani ba, saijin sauƙar mari yayi akan kumatunsa,  Zahrah ce ta ɗaukesa da lafiyayyen mari, babu abun da ke kwance akan fuskarta banda tsananin ɓacin rai, 

“Koda wasa kada kasake ƙoƙarin taɓani, mayaudari, dama haka kuke bakuma zaku canza ba!!” fuuuuu haka Zahrah tafice daga cikin motar tamkar kububuwa.  

Tamkar statue haka Dr Sadeeq ya tsaya, komai nasa daina aiki yayi, sai numfashinsa dake fita da sauri,  ganin komai yake tamkar al’amara,  wai yau shine Zahrah ta mara da hanunta, a hankali yasanya hanunsa ya shafi kan kumatunsa inda Zahrah ta wankesa da mari, ko kaɗan baiga laifin Zahrah ba, kuma baiji zafin marin da ta masa ba, babban damuwarsa da tashin hankalinsa, shine yanda yaga Zahrah tana kuka wiwi, sannan kuma ranta yayi matuƙar ɓaci,  tabbas da yasan abun zai ɓaci har haka, to da baiyi gigin furta mata kalmar cewa zai aure ta ba, ko da na minti ɗaya ne bayason ɓacin ran Zahrah, yanzu yasan haka zata kwana tana kuka, maiyasa? maiyasa na kasa jurewa? ni nake burin faranta rayuwa da zuciyarta, amma sai gashi da kaina nasake ruguza farinciki’nta  maiyasa? yatambayi kansa da ƙarfi, cike da haushin kansa ya sanya hanunsa duka biyu ya daki siterin motar tasa, wani irin haushin kansa yakeji,  yayi dana sanin sanar da’ita abun dake cikin zuciyarsa,  “mai yasa na yarda nazamo LOSER?” ya tambayi kansa cikin ƙunan zuciya, yakusan 10 minute yana zaune a cikin motar, da ƙyar ya’iya tada motar yabar cikin unguwar tasu…

Zahrah kuwa tana shiga gida, kaitsaye ɗakinta ta wuce,  zamewa tayi a ƙasa, tashiga rera sabon kuka,  lallai tayarda cewa Ƙaddaranta mai girma ce, daga wannan sai wannan,  bata taɓa zato ko tunani’n haka zai fito daga bakin Dr Sadeeq ba, ko da wasa bata taɓa ayyana wani abu a ranta ga me da shi ba,  maiyasa zai zo mata da wannan maganar a daidai wannan lokacin? maiyasa zai sake maida ita uƙubar da tayi nasaran samun bakin fita daga cikinsa?   tabbas yanzu kam tayarda cewa duhu yasamu mazauni a cikin rayuwarta

“Bawanda zai soni a haka, shima nasan ba sona yake ba, wata manufarsa kawai yakeson cimmawa, ashe ƙaddarorina suna da yawa?” ta tambayi kanta cike da ruɗu.
Sanin bata da amsar bawa kanta, yasanya ta cigaba da kukanta, ganin hakan bazai fishsheta ba yasanya ta ɗauro alwala tazo ta fara gabatar da salla, haɗe da miƙamawa mai kowa mai komai duka lamuranta…

Koda Doctor ya isa gida, baije koda ɓangaren mahaifiyarsa bane, kai tsaye ɓangarensa ya nufa, gaba ɗaya jiyakeyi duniyar ta masa ƙunci,  saboda cimma muradinsa yasake sanya Zahrah a damuwa,  kwanciya yayi lamo akan gado, zuciyarsa cike da tarin tunanuka kala kala, gaba ɗaya kalamanta ne suke yawo a ƙwaƙwalwarsa, babu kalman da tafi tsaya masa a rai kamar inda takecewa ” Natabka  nadamar baka daman shigowa rayuwata da nayi, katafi ba naso na sake ganinka ko kuma jinka!!”  wannan kalamannata sunfi komai ɗaga masa hankali,  sam shikam ya ma manta da marin da tayi masa,  saboda bai ɗauki marin a matsayin komaiba, shidai shiga damuwarta ne bayaso, baisan wani irin so yake mawa Zahrah ba, bayason ganinta a cikin damuwa, ba kuma yason ɓacin ranta, amma tayaya Zahrah zata fuskancin hakan?  Yanaso ya aureta yakuma inganta rayuwarta, ba budurci’nta bane abun so a gareshi ita kanta ce abarsonsa, haƙiƙa kowani namiji yana burin auren mace yasameta a budurwa, shima kuma yana burin hakan, amma son da yakemawa Zahrah, yasanya zai iya karɓanta a yanda take.. Haka Doctor yayita saƙawa da kuncewa, da ƙyar bacci ɓarawo yayi nasaran ɗaukarsa.

Ɓangaren Zahrah ma dai hakanne takasance da ƙyar ta’iya runtsawa a wannan dare….

TURKEY

ZAID ne zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera,  sanye yake da riga long slive, white colour yayinda wandon jikinsa ya kasance baƙi,  suit ne baƙi ɗaure a saman kayan nasa,   sosai yayi kyu a cikin shigartasa,  hanunsa riƙe yake da wani dogon kofi na glass, bakomai ne acikin kofin ba face giya, a hankali yake sipping giyar tasa, yayinda ya ɗaura ƙafansa ɗaya kan ɗaya,   gefensa kuwa Abid ne zaune shima dai irin shigar Zaid ɗinne a jikinsa, sai dai shi nasa kalan sun kasance blue,   “Lokaci fa yana tafiya Zaid, yakamata ace yau munkoma New York, amma bansan dalilinka nacewa muzauna anan ba, ni fa duk yanda instanbul takai ga haɗuwa da daɗin zama, batakaimin new york ba, kasan can akwai mata ƴan harka, amma ni gaskia nan a takure nake!” Abid yakai ƙarshen zancennasa cike da ƙosawa.

Kyakkyawan murmushinsa yayi haɗe da maida kallonsa ga wani kyakkyawan ruwa dake gudana a gefensu,
“Inason zaman Instanbul sosai Abid, domin yanayin garin yanasawa inajin shauƙin abar sha’awata!!”

“Bangane shauƙin abar sha’awan kaba? wai meke damunka ne? kusan tsawon watanni kenan dana fuskanci sauyawa a tattare dakai”

“Sha’awa nakeji Abid, matsanancin sha’awarta nakeji!”
Zaid yafaɗa cike da tsananin shauƙi.

“Sha’awa? wacece ita?” Abid ya tambaya cike da zaƙuwa, domin shikam yarasa wace irin macece Zaid ya kejin sha’awa’rta haka, ko da yaushe cikin maganarta yake, kuma ita kaɗai yakejin sha’awa.

“ZAHRAH NA!” Zaid yafaɗa cikin wata murya mai ɗauke da ma’anoni.

Dariya sosai Abid yasanya, hadda riƙe ciki,  “Zahrah fa kace Zaid, wannan villager girl ɗin, koba sugar baby’nka ba?” Abid yatambaya yana ƙoƙarin gimtse dariyar da ta tasomai.

” Tana da matuƙar mahimmanci a wajena Abid,  bantaɓajin irin abunda nakeji akanta ba, inason kasancewa da’ita a koda yaushe, inaso tazama ita ce mace guda ɗaya dazanna yin sex da’ita dare da rana,  sha’awarta tamun mummunan kamu Abid, kasan yanda nakeji kuwa ?”  Zaid ya tambayi Abid cikin sigar rashin wasa.

“Kokaɗan bansan ya kakejiba, amma kuma Zaid wannan ba sha’awa bane SO ne” Abid yafaɗi hakan da iya gaskiyarsa, domin shi abun da ya fahimta kenan.

Dariya sosai Zaid yashiga yi, haɗe da sanya hanunsa ya daki kafaɗan Abid.
“Shirmen banza, wai SO? menene SO Abid? kasan me kake faɗa kuwa, taya sha’awa zata zama SO, so fa kananufin wai inasonta ne, hahaha Abid ƙwaƙwalwarka ƙaramace, taya za’ayi nayi soyayya da’ita,  sha’awace kawai kuma da zaran na sakeyin sex da’ita nasan komai zai wuce,  tun farkoma danasan ban ƙoshi da’itaba, ai da banbari ta tafiba!!” yaƙare maganar yana mai ɗaga kofin giyarsa yakai baki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button