SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

Ko kwalli, yau bata shafa ba, balle kuma uwa uba fawder, zumbuleliyar doguwar riga ta sanya, haɗe da ɗaura ƙaton hijab akai, kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa tana cikin damuwa da ƙunci.
Koda tayi mawa su Baffa sallama, suma sun fahimci cewa yanayinta ya sauya, amma sai suka share babu wanda ya tambayeta.
Tana kai ƙofar gida zuciyarta tayi wani irin bugawa, sakamako’n ganin motar Dr Sadeeq, da tayi fake a ƙofar gidan nasu, tsayawa tayi cak ganin cewa driver’n sane yafito daga cikin motar, saɓanin shikansa Dr ɗin.
Cike da girmamawa Mudi driver ya ƙaraso inda Zahrah ke tsaye.
” Ranki shi daɗe barka da safiya! dama yallaɓoi ne yace nazo na kaiki makaranta, shi ba zai samu daman zuwa ba, wani aiki ne ya riƙesa, kawo jakar na karɓamiki” Mudi driver ya ƙare zance’n nasa yana mai ƙoƙarin karɓan jakar dake riƙe a hanunta. Saurin ja da baya tayi haɗe da fusge jakarta, cike da ɓacin rai tace.
“Kakoma kace masa bana buƙatar kulawarsa koda kaɗanne, ka kuma ce masa injini yafita a rayuwata, saboda bana buƙatarsa!” tanakai ƙarshen zancennata tasakai tayi tafiyarta.
Da kallo kawai Mudi driver yabita. “Uh ni naga bala’i, daga taimako kawai, to Allah ya kyauta” Mudi yafaɗa yana mai komawa cikin motar, key yayimawa motar haɗe da nausata kan hanya, tabbas zai koma ya shaidawa uban gidansa, duk abun da tace a faɗamai..
Cikin ikon Allah tana isowa bakin titi tasamu mai taxi, bawani ɓata lokaci tashiga yaja sukayi gaba, bayan ta sanar masa inda zai kaita.
Tun shigowarta cikin ajin, Husnah ta lura da mugun sauyawan da fuskar Zahrah’n tayi, domin kuwa kowa ya kalli idanunta, zai fahimci cewa tayi kuka har ta ƙoshi. kasancewar Zahrah’n na shigowa malami yashigo, yasanya Husnah bata samu damar tambayarta komai ga me da sauyawarta ta ba.
Koda aka fito daga lecture, kan dakalin da suka sama zama, yauma sukai mawa kansu masauƙi.
“Wai meke damunki ne Zahrah? gaba ɗaya kinsauya, bayan jiya ba haka muka rabu dake ba, sannan kuma na kula cewa, yau ba Dr bane ya kawoki, maike faruwa?” Husnah ta tambaya cike da kulawa, ga ƙawarta ta.
“Inacikin matsala Husnah! a she a yanzu babu wani, wanda zai taimakeka don Allah sai don biyar buƙatar kansa? na ɗauki yarda ta na basa, na ɗaukesa tamkar ɗan’uwa, na’aminta dashi, nayi saurin yadda haɗi da sakewa dashi, bantaɓa zaton haka zata faru ba, ashe shi abun dake cikin zuciya da ruhinsa daban ne, wani abune saɓanin tunani na!” Zahrah tafaɗa tana mai share ƙwallan daya gangaro daga cikin idanunta.
“Banganeba, kinsani a duhu, maikuma ya sake faruwa? ki faɗamin !” Husnah tafaɗi hakan cike da zaƙuwa, don ta ƙosa taji menene matsalar ƙawarta ta.
“Kinsan abun da yafaru dani Husnah, Zaid yaci mutumci na, ya ƙwaci budurcina da ƙarfin tsiya, ya halaka min rayuwa, shin kinaga akwai wani namiji dazai soni tsakani da Allah, bayan yasan abun da yafaru dani?” Zahrah ta tambayi Husnah.
“Haryanzu banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zaifi kyau ace kiwarwaremin komai!” Husnah tafaɗi hakan cikin rashin fahimta.
“Ba gaskiya bane Husnah, bai faɗawa kansa da zuciyarsa gaskiya ba, baizamanto gaskiya ba, soyayyar da yakemin ba gaskiya bace, Husnah bazan yaudari kaina ba, domin nasan babu tayanda za’ayi cikekken namiji mai aji da lafiya kamar Doctor Sadeeq, yace wai ni yake so ya aura! ina kokonto akan al’amarin !” gaba ɗaya hawaye sun gama wanke mata fuska, lokacin da takai ƙarshen zance’n nata.
Nannauyar ajiyar zuciya Husnah ta sauƙe, domin kuwa sai yanzu ta fahimci inda matsalar ƙawartata take, dakuma abun da ke damunta.
“Doctor da kansa yace zai aure ki Zahrah?” Husnah ta tambaya, bayan ta aza hannayenta duka akan kafaɗun Zahrah.
Kai kawai Zahrah ta’iya gyaɗawa, alamar “eh”
“Ba wasa bane Zahrah kamar yanda kika ɗauka, haka kuma ba yaudara bane kamar yanda kike tunani, har yanzu keɗin mai kyauce, kuma haryanzu keɗin haɗaɗɗiyar mace ce abar so ga kowani irin namiji, ba’akanki a ka faraba, baikuma dace ki ɗau hukunci mai tsanani gawanda baiji ba bai gani ba, kina tunanin Doctor Sadeeq yaudaranki zaiyi ?” Husnah ta tambaya.
“Ƙwarai kuwa Husnah, ke kanki kinsani, namiji kamar Dr ba sa’an aurena bane, ko lokacin danake ɗauke da mutumcina yafi ƙarfina, balle yanzu danake fanko, inaso kisani wannan karanbani’n shi na tafka a karon farko, yazo yazamemin babbar matsala, domin kuwa nayaudari kaina, na sawa zuciyata soyayyar wanda har gaban abada yafi ƙarfina, yakuma yi mini rata, na yaudari kaina danaƙi amfani da tunanin cewa Zaid yafi ƙarfina, bazan taɓa yarda nasake aikata haukan dana aikata a baya ba Husnah!” Zahrah tafaɗa cike da raunin murya dana zuciya.
“So baitaɓa zama haukaba Zahrah, kada kicemin kin wulaƙanta Doctor saboda abun da Zaid yayi miki, kada ki yarda da tunaninki nacewa gaba ɗaya maza mayaudara ne, kowa da irin halinsa, kuma masu irin halin Zaid basa ɓoyuwa a kamanni da halaye, soyayyarsa ce kawai tarufe miki ido, har ki ka kasa hango mummunar manufarsa a kanki, yana da kyau ki nutsu kiyi tunani, inada tabbacin cewa Dr Sadeeq, ba zai taɓa cutar da rayuwarki ba, kema kuma yakamata kisan hakan, kada tunaninki ya gushe ki kasa tantance fari da baƙi, wlh ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq ba mutumin banza bane, bakuma zan ɓoyemiki ba, tabbas idan kika tsaya wasa da damarki, to zata miki mummunan suɓucewa, haƙiƙa Dr Sadeeq haɗaɗɗen gaye ne, wanda ko wacce mace zatayi fatan samunsa a matsayin mijin aurenta, nasan idan nace miki kiyi soyayya yanzu na haɗaki da babban aiki, amma zai kyautu ace ki koyawa zuciyarki soyayyar Dr Sadeeq, shawara nake baki Zahrah, idan kuma har kikayi amfani dashi, bazaki taɓa danasani ba, dan Allah ƙawata kiyi tunani mai kyu!” Husnah tafaɗi hakan cikin son ƙarfafawa Zahrah guiwa.
Hawayen dake zuba daga cikin idanunta ta sanya hanu ta share.
“Bazan iya ba Husnah, bazan iya taɓa sake son wani ba a cikin rayuwata, kada ki ga laifina, nasan Dr Sadeeq yafi ƙarfina, yana da asali, yana da ƴan uwa, yanada gata, yana da kuɗi, yanakuma da ƴancin da zai zaɓi matar aure wacce ransa keso, nikuma fa? idan kikayi dubi da tushena, to ban cancanta da zama inuwa ɗaya da shi ba, nifa yanzu banda wani ƴancin da zan iya zaɓin mijin aure da kaina, sbd akwai nakasa acikin rayuwata, dole sai mai tawakalli ne zai iya aure na, to maiyasa zansanya kaina a cikin wahala? balallai farincikin da Dr Sadeeq ke ƙoƙarin bani yakasance dauwamemmeba, nafaɗamasa yafita a rayuwata Husnah, a yanzu bana buƙatar kowani namiji, zaifi kyautuwa a gareni nayi rayuwata ni kaɗai, nayarda da ƙaddarata, amma kuma yazama dole na kiyaye sake jefa kaina a haɗarin soyayya!”
Rungume Zahrah,
Husnah tayi ajikinta, sosai tausayin ƙawarta ta ya kamata, haƙiƙa Zaid yacutar da rayuwar Zahrah, ya rabata da duk wani sukuni nata, amma a kwai Allah.
“Haƙiƙa dole zakiji ciwo Zahrah, amma yana da kyau ki zurfafa tunani, ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq auren ki yakeso yayi bada wasa ba, amma abun da kikayi masa baki kyauta ba, ki basa haƙuri, koda kuwa bazaki auresa ba, yayi babban ƙoƙari acikin rayuwarki, kiyi nazari, amma kuka ba naki bane, kuma yana da kyau rama halacci da alkhairi !”